Sashe 19
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayana Wata 3
Kai ya banga gilmawar mutuniyar taka ba, Hafiz yace ga Maryam chan bari in kirata, "Maryam" tazo tace "sannu, baka ga Aunty Sauda ba ko?tana Gida Mummy ta rufeta, wai tayi Ciki kuma kaine ka mata cikin" wani irin Ashar Hafiz ya lailayo, yace "na ma uwar ta ciki? A gidan uban wa? Da ke da saudan da Uwarku food is ready kun kwashi kan--- Anas yayi saurin taran numfashin shi, yace "Haba my man, kaga ka fara janyo hankalin mutanen nan, yanzu za suyi mana caaaa, nan ne Maman Sauda tazo, ta sassauta murya don bata son mutane su ji su, tace "Hafiz, zo mu shiga daga ciki, akwai magana" da kyar Anas ya ja Hafiz cikin dakin. Maman Sauda ta fara magana, tace "Hafiz, dama jira nake kazo kano, don na san zakazo, Sauda na dauke da ciki wata 3, tace cikin kuma naka ne, Hafiz ya zaburo yace "bangane ciki na bane? Ni kadai nayi hulda da ita, ni so daya na taba hurda da ita, so taje ta nemo uban cikin ta ba ni ba" Maman sauda tace "aa Hafiz, kar kace haka, Allah ya jarabci sauda da son ka, tunda ta fara ganin ka ta kilace kanta don kai, kuma ta tabbatar min da cewa cikin ka ne" Hafiz yace ba fa zam yarda ba, yarinya taje tayi ciki zaa ce ni na mata?" Mamar Sauda tace "to ko zaa bari ta haihun ne, sai aje a gwada jini?" Anas yace Sam hakan ba zai faru ba, ai abun be kai ga haka ba, kudi kawai zaa baku ku cire, kai feezo ciro kudi kawai, ka bata ta murje shege, idan aka bari ta haife cikin Yawah go dey, kasala go burst" Hafiz ya danyi wani tunani yace nawa zai isa a cire ciki? Mamar Sauda taji maganar kudi, tace 250,000. Hafiz ba ji komai ba ya rubuta mata Cheque din dubu dari uku. Suka bar gurin, tunda daga ranar be sake waiwayan Food is Ready Restaraunt ba.
Abunda ya faru bayan nan; Maman Sauda tayi tayi sauda suje a zubda cikin nan, sauda ta yi k'ememe tace wallahi ba zaa zubar ba, tana son babyn ta, a cewar ta, da an zubar da cikin nan duk wani burin ta na auren Hafiz zai ruguje, Abun da zata haifa kadai ne zai sa Hafiz ya aure ta.
Bayan kankanin Lokaci Maman Sauda ta rasu sakamakon ciwon cikin da tayi rana daya, ko kwana bakwai baayi ba Sauda ta saida gidan Abinci suka hada kayan su ita da kanwar ta suka bar garin, suka nufa Wudil wurin dangin baban su, da suka ganta da ciki sai tace ai tayi aure mijin ya rasu, dangin sunyi mamakin auren Sauda ba da sanin su ba, amma ba suyi mamaki sosai ba don sun san cewa uwar su Saudan ba kirki ne da ita ba.
Lokacin haihuwar Sauda nayi ta haifi diyar ta mace, Ba su ko kara ganin Hafiz ba ko abokin sa Anas, diya dai taci suna Aneesa, haka Aneesa ta tashi gata nan dai, Sauda ko ba binciken da batayi akan Hafiz ba amma ta kasa gane komai game dashi, ta sa ba dan Kano bane zuwa yake, amma ta kasa gane takamaiman garin da yake, haka ta hakura da binciken shi, har ta manta dashi.
Bayan 15 years
Aneesa na da shekara16 ta gama Secondary Sch din GGS wudil, don ma mamarta na mata jumping, don Aneesa na da Girman Jiki sosai, idan kaganta zaka zata irin yan matan Jamian nan ne. Aneesa shagwababiyar yarinya ce, ta samu daurin gindin Mamarta da Auntyn ta maryam, acce take kira da Aunty Meemah, sai ahunda takeso akeyi, ta taka duk wanda ya so kawo mata cikas.
Sauda na kitchen taji ana kiran "Habib Ibrahim Lema" a TV da sauri ta fito ta k'ura ma Tv ido tana kallon wanda aka kira da COO (Chief Operating Officer) of Lema's Machinery Company. Tsaf ta karance shi, tabbas wannan jinin Hafiz ne Baban Aneesa, Habib na kama da Hafiz Sosai, amma yafi Hafiz komai, ta fada a ranta, ta aiyana ma ranta, ta kudurta a ranta, ta ma kanta alkawarin Auren Habib Ibrahim Lema, ko ta halin k'ak'a don yanzu tafi karfin Hafiz Lema.
Asuban Fari ta ma Gidan bokan ta na kan tudu Sammako, ta zaiyane mai bukatun ta, boka yayi daria yace Saude kin debo mai Zafi. Tayi daria tace "ina sane, shiya sa na zo don ka gaya min koma don Abun ya zo min da sauki"yace gaskia ne, nan boka ya zaiyane mata komai game da Habib Lema, da Iyalan sa, Har Hafiz dake lagos kulle sai da aka shaida mata, komai bokan kan tudu ya gaya mata game da Family din Habib Iro Lema. Tayi daria tace lokaci yayi da zan tarwatsa Happy Family din nan, tana dawowa Gida ta shirya yanda zata yi komai tun daga farkon zuwan ta Katsina, ita da diyarta don Meema na makaranta a nan Wudil, Tana zuwa Katsina ta nufi wurin Aikin Aisha Lema, ta samu karbuwa gunta kuwa, toh gashi abu zaizo mata da sauki tunda Hafiz ya dawo, ita da bata sashi cikin list dinta ba, amma tinda har ya dawo, komai zai zo mata a sauk'ak'e zatayi amfani dashi ta cimma burinta.
Wannan shine Labarin Hafiz da Saudah, da kuma Musababbin zuwan Sauda Katsina, to ko Allah na bata ikon auren Habib Lema baban Rafeeq? Nidai nace wane ita tayi kishi da Mameen mu Aisha? Ku biyoni don jin yadda za'a kaya.
_Bibilicious Biebee_
Jiya ina kwance da misalin karfe 2:30pm,ina bacci sai na farka.
Ina farkawa sai naji hayaniyar mutane a waje sai na fito amma banga kowa bah
Sai na koma daki na kwanta amma ban daina jin hayaniyar ba sai mah karuwa takeyi
Na sake fitowa a karo na biyu dut banga kowa bah.....Kamar ance in kalli sama,ina duba sama kuwa sai naga mutane
Wai ashe jirgin sama ne ya lalace shine suke turawa
Saura kuma kuce karya neh :,,,, a karya kumallo,,, Lol😂😂😂
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣4⃣
Zaman Lafiya akeyi a gidan Alhaji Habib Lema, Har yau Amarya Sauda na nan a matsayin Secretary na Mami Aisha, da Mami tayi maganan a chanza mata wurin aiki tace "aa, ita dai a barta nan don ta saba, haka mijin su ya barsu don yana jin dadin yanda matan shi suka hade kansu.
Hafiz ma girma yake basu duka, ba za ka ta bacewa sun san juna shi da Sauda ba, don da ga gaisuwa ba abunda ke hada su, Aneesa kuwa in kaga tayi wani abu sai ka rantse da Allah ita ce diyar Habib Lema ba Rafee'ah ba. Rafeeq kuwa be da matsala, idan ya shigo gidan be da aikin yi sai tsokanan Rafee'ah da Aneesa fada..
Bayan Wata 2 (Bakin Rana)
Gidan Shiru kamar ba kowa a ciki, Rafee'ah na Kaduna Gidan Uncle Zaid, taje taya Aunty Safiyya zama don ta na da juna biyu, kasancewar hutu, Aneesa na BUK wurin Aunty Maryam, Rafeeq na chan suna flexing da su Maalesh, Hafiz da Alhaji Habib sunje wani Bussiness trip . Sauda ta kirashi a waya tace " Alhaji ya Lagos? Yace "Ohh, banso kika kira ba, coz suprise nake so na muku, sai dai kawai ku ganmu, yanzu ma in less than 2hrs zamu shigo katsina" daria tayi cikin salon yaudara tace "kace yau da mun sha Suprise" yace "ina Shatou na?" ranta ya sosu, ta tsani taji yace "Shatou din shi" gashi shi be jin komai gaban kowa haka yake ce mata, zai sani, itama zata sani, don kawai ta barsu suyi enjoying time dinsu ne for the main time kafin ta fara operation dinta, ta daure dai tace "ni dai duk yau ban ganta ba, k'ila ta fita ko kuma tana daki" yace "to ki dai sanar mata da zuwan mu" ta murguda baki kamar yana ganinta tace toh sai kun kar'iso."
Dakin Mami Aisha ta shiga da Sallama, tana zaune kan gado tana latse laptop dinta, ta amsa mata cikin sakin fuska, tace "Sauda kin tashi lafiya?" "lafiya lao Yaya Aisha" suka yi shiru, har saudah zata gaya mata dawowan Alhaji sai wata zuciyar tace kar ki gaya mata, sak'esak'en da ta jima ta nayi ya fado ranta, ta tambayi zuciyar ta "to ko damar ce ta samu yanzu? Bari inyi amfani da damar nan" ta mik'e da sauri tace "bari in dan hada mana Sobo" Mami Aisha tace kamar kin san ina marudin shan Zobon ki. tace "karki damu i wont take long".
Ta shiga dakinta da sauri, tana sak'esak'en abun yi, ta yanke hukuncin kiran Mak'ale, ringing daya biyu ya daga, cikin muryan yan iska yace " Hello Matar lema ya akayi ne?" tace "mak'ale kana ina ne?" yace gani wurin Goruba road" tace "donAllah yi sauri kazo akwai aiki" yace "to gani nan karisowa" "yauwa idan kazo ka kirani"
Ta gama hada tsobonta tsaf, ta ciro wani k'ulli daga habar zaninta, ta ware, magani ne na gari ta zube shi a cikin cup din ta karkada, sai kuma ta ciro wasu k'wayoyin magani ta zuba a ciki, ta karkada sosai ta dauka ta nufi dakin Mami Aisha. "Lahh har kinyi me?" tayi daria tace "har na hada, ai ba wuya" ta dire mata jug da cup din, Mami tace "nagode sosai" tace "haba ai bakomi bari inje in daura sanwan rana" ba jira ta tsiyaya sobon a kofi ta sha, ta kara tsiyaya wa ta shanye, ya cigaba da aikin ta a kan computer. Saude da ke Labe bakin k'ofa ta daka tsalle ta na murnan ta sha, da sauri ta koma dakin ta ta kira Mak'ale tace "wai ya? Kana ina? Yace wallahi gani nan bakin gate dinku yanzu nake shirin kiran ki" tace "toh bari in fito in shigo da kai" ta yafa mayafi ta fita da kudi a hannu.