← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 95

Sashe 65

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yana tuk'i yana kallon bayanshi hawaye na zuba, sambatu yakeyi, "DonAllah kar ki tafi ki barni, Rafee'ah ta yafi, kema kar ki tafi, bansan me zanyi ba in kika mutu, Ya Allah kar ka dauki ranta, Allah ka dauki nawa instead" ireiren maganganun da Rafeeq keyi kenan, Sanyi ACn Motar ya sa Nasiba farfadowa, tari ta hauyi ai da sauri ya juya ya kalleta, wani murmushin da be san lokacin da ta subulo ba ya sake tare da taka birki ya tsaida motar, fita yayi ya koma baya, hannunta ya rik'o Yace "Naseebah, Naseeba are you Ok?" tari ta shiga yi ba sassautawa ta zame hannunta daga nashi tace "I'm fine, ina Nene?" yace "Tana chan gurinsu Uncle Zaid" Nasiba ta shiga tuno abunda ya faru tiryan tiryan, tace "Hamma mu koma donAllah, Nene na chan ban san halim da take ciki ba" yace"karki damu nasan Asibiti zasu kawota, right now i need to take you to a hospital" tace "please mu koma, i'm fine now, i just need Water" da sauri ya dauko mata ruwa a gaban Seat, ya bude ya bata ta kwankwada" cikin sigar lallashi yace "Listen to me, zan kaiki Asibiti a duba ki, Neh-neh kuma is in safe hands, barin kira su in gaya musu kin farfado mu hade a Asibitin" Maalesh ya kira, "Maalesh kuna Ina?" cikin damuwa yace gata nan zamuzo "Alheri Clinic don ya fi kusa" "bata farfado ba?" Wallahi kuwa feeq, gatanan ko numfashi batayi" Rafeeq ya cije hak'oranshi, yace mu hade Asibitin ni na kusa ma" sukayi Sallama, Seebi tace ya jikin Nenen? Rafeeq ya fita ya koma matukin direba tare da cewa "gata nan zasu kawo ta wanchan Asibitin".
*****
Daidai isowar Ambulance, aka fito da Nene aka shiga da ita ciki already Daddy ya kira Dr aka yi da Nene Emergency, da kyar aka samu suka tsaya daga waje,Seebi kuwa ta k'i yarda a bata gado acewarta ba inda ke mata ciwo, Dr's suka buga nan suka ta6a nan ba alamun Nene Zata motsa suka dukufa da aikinsu a matsayinsu na Kwararrun likitoci.
Bayan 'yan mintoci Likitoci suka fito fuskar su ba Annuri.
Dr Sami yace "i'm so sorry, we couldnt save her" luuuuu Nasiba ta zame k'asa ta zauna dabas, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun inji Daddy, Zaid Ya dora hanayensa duka biyu akai, Maalesh ya fara matsar kwallah, Wtf? Inji Rafeeq, ya chakume shi, what do You mean by you couldnt, save her huh? Dr Umar yace "kuyi hakuri, kamar tana da Athma, kuma ta shaki hayak'in Sosai, kuyi hakuri Addua kadai take buk'ata" Bangaje shi yayi ya shiga dakin duk suka biyo bayanshi banda Nasiban da Hawaye ke ambaliya a fuskarta, Nene ta rasu? Nenenta? Inalillahi, Nan da nan ta chanza kammanni sabida kuka, tausayi Mahaifinta da Goggonta da ke Jigawa ya kamata, suna mugun son Nene (kamar yanda Iyalan Zailani keson Tsoho, lols) kuka takeyi sosai me hade da Sheshek'a, ta kasa yarda da Nene ta Rasu. Rayuwar da sukayi ya fara dawo mata, ta mik'e Zumbur ta shiga dakin.
Kwance ta ga Nene an rufeta da zanin Gado, Uncle Zaid ta fara kallo, har yanzu be sauke hannunshi daga kansa ba, yana kuka mara sauti, Alhaji habib be daina Salallami ba, Maalesh na kuka, Rafeeq na kwance kan jikin Gawar Nene yana kuka, Neh-Neh DonAllah ki tashi, DonAllah, Neh-neh kin zama wani Jigo a cikin Rayuwata, na k'i yarda kin mutu, in kika mutu bansan ta yanda Zan cigaba da Rayuwa ba ke a cikinta, Neh-Neh Ina sonki, ki tashi na yarda ki cigaba da cemin Dunkum, zan amsa sunan, ba zan k'ara miki tsaki ba, zan dinga shan Maganin nan, zanyi duk abunda kikeso, DonAllah ki tashi, Allah kar ka kashe min Neh-neh nah, Allah ka tada min ita I love you Neh-Neh. wani kukan me tsuma rai Nasiba ta fashe dashi, duk sun tausaya ma Rafeeq, Wai dagaske Nene ta Rasu? Shikenan ba Nene? Numfashinta taji ya kusa daukewa itama.
"kai ni Dallah daga ni,ka wani danne min kahon Zucciya, ko sai ka k'ara sani?" da mamaki ya dago ya kalleta yace"Neh-Neh??" tana yunkurin tashi Maalesh yayi saurin taimaka mata ya zaunar da ita, murna gun Rafeeq baa magana ya subuce da dariar murna "ku Bata mutu ba Wallahi bata mutu ba" Sujjudushukur Nasiba da Uncle zaid sukayi don godewa Allah, Alhaji Habib ya fita don kiran likita yana hamdala, daya bayan daya ta bi su da ido tace "wai ya? Ko cema ku akayi na mutu ne da kuke ta wannan abun? Dr Sami da Dr Umar suka shigo da mamaki, sun tabbatar da zuciyarta bata bugu kafin suka sanar da Yanuwanta, to ya akayi haka? Ikon Allah ne, Dr Sami ya soma dube dube a jikin Nene, Yace "Blood of Jesus has healed her, she is a strong fighter" Nene ta katse shi tace "wai gwajegwajen nan na meye? Kalau fa nike, zaka zo ka tasani gaba kana man turanci, Daga gani kai kace musu na mutu, haka kurun ka tada wa 'yan jikokina hankali" duk sai da sukayi Daria banda Rafeeq da ya daure fuska wai ba abun daria bane(ikon Allah ku ji min Rafeeq da ya gama fita hayyacinshi don ance ta Mutu) Dr Sami ya kalli abokin aikinshi yace "Dr Umar what is she saying?" Dr Umar yace "Shes thanking God that Shes still Alive, go to the Office i'll take it from here" Dr Sami ya fita daga Ofishin.
Ya kalleta da Murmushi yace "Sannu Mama, kiyi hakuri dogon Suma ne kikayi, Wallahi mun dade a kanki, Duk wata kafa ta sadarwa ta tsaya a jikin ki, saida muka samu tabbacin hakan kafin muka sanar dasu" tace "da kuka tabbatar kaine a zaune yanzu? Nace kaine a zaune? Toh ban mutu ba, bawai tsoron mutuwar nike ba, ku dai san aikin ku, ku san me zaku dinga fada ma mutane, yanzu da bakin labarinku ya sa Zuciyar Jikata bugawa ta shek'a lahira fa? Ni na mik'e ita ta mutu to me akayi kenan? Anyi ba ayi ba, ana muku kirari da likita bokon turai, to bokon kashi dai tunda ba ku san aikinku ba" nan ya shiga bata hak'uri tace su zaka ba hakuri, sai in yafe maka" yayi murmushi yace da su "Daddy suyi hakuri" murmushi sukayi sukace bakomai. Bayan nan aka fara diramar sama Nene Drip tace kwatakwata ita bata san Zancen ba sai dai a sallameta, Seebi tace "Wai Nene ki tsaya mana a sa miki drip din" tace "naki, ke ki zo a saka miki" Rafeeq ya daure fuska, "Uncle Zaid please talk to this Stubborn Old Woman" yayi daria yazo yace "Nenenmu kiyi hak'uri ki bari a saka miki drip din, kinga ko an sallameku yanzu ba inda zaku zauna a gidan don kusan komi ya k'one, da lallashi da lalama Nene ta yarda aka sa mata drip din.
"***
A dan tsorace Rafeeq yace "Ku tsaya ku tsaya? Ku tsaya! Ina Ayman? Nene tace sai yanzu ka tuna da ita? To kar ka damu tana gun Kakar ka, dazun Baban ta ya kaita kwana, ashe Soyayyar k'arya ake mata tunda sai da aka Neh-neh ta watsake aka tuna da ita, Rafeeq ya murtuk'e fuska, Zaid yace "kaii Nene, kinsan in ka rude abun da ke gabanka kawai kake gani, amma ba me tantaman Soyayyar Rafeeq ga Ayman, Nene tace sai ni don ya fi so na, yau naga tashin hankalin su O'eh, Maalesh yace "a fadi suna mana", tace "da Dunkum nike ai yasan dashi nike, tashin hankali yau Su dunkum har da su i lobi me Neh-neh, to nima i lobi you Dunkumeh, ai na rok'i Allah kar ya kasheni sai ya nuna mana auren mu" Alhaji Habib na daria yace "Aurenku ke dawa? Tace "yo ni da Dunkum mana, ai sai na Auri Dunkum" Duk suka fashe da Daria banda Rafeeq da ya hada gabas da Yamma kamar be ta6a daria ba.
Chapter 65 · 0% Book details