← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 95

Sashe 26

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da tayi wanka tayi Sallah ta fita parlorn k'asa, Saude ta sauko itama, tace "Rafee'ah, har kin fito? Tace "eh Aunty i'm just eager to talk to you", Saude tace "tohfa, what's it about?" Rafee'ah ta rik'o hannayen Saude guda biyu ta zaunar da ita, tace "Aunty, donAllah ina so ki gaya min gaskia, duk wanda na tambaya baya bani gamsashiyar Amsa, ki taimaka ki gaya min, ina Mami na take? Na kusa wata 3 daga dawowa na da kaduna, ba labarinta, kar kuna 6oye mun wani abu, please ki gaya min".
Cike da makirci Sauda ta fashe da kuka, nan da nan Rafee'ah ta rikice "Aunty me ya sameki? Ko dai Mami na mutuwa tayi?" Saude cikin kukan munafurci tace" ko daya Rafee'ah, zan gaya miki abunda na sani game da Mamin ku, amma kar ki ce ma kowa ni na gaya miki don ba sa so ki sani" Rafee'ah ta gyara zama tace "InshaAllah" Sauda ta kara sautin kukan ta, tace "Rafee'ah, ashe maminku yar iska ce? Ashe Magajiya ce uwar karuwai? Kwarto ta kawo cikin dakin auren ta, Kwartu--" bata k'arashe zancenta ba taji an sauke mata wasu kyakyawan mari biyu, a zabure ta dafe kuncinta, ta daga idanuwan ta taga Rafee'ah tsaye tana huci kamar Zakanya, Sauda ta dago a fusace, tace "Rafee'ah, ni zaki mara? Don na gaya miki gaskia? Don ma ban gaya miki gaskian lamarin ba? To kwance a ka ganta haihuwar uwarta da gardi" Wasu Mari ta sake ji an sake mata wasu na bin wasu, Mamaki ya rufe ta, tabbas ba Rafee'ah ce tayi marin nan ba, kafin ta ankara taji muryan mijinta Alhaji Habib cikin daga murya yana cewa "Rafeeq, dont, kar ka sake taba ta" Rafeeq beji ba illa ma dunk'ule hannun da yayi zai kai mata nushi, da murya karkausa Uncle Zaid ya kira sunan shi "Rafeeeeq".

_Bibilicious biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg2⃣9⃣

Fasa nushin ta Rafeeq yayi, ya sauar da hannu yana ajiyar zuciya, Zaid ranshi a bace, be ji dadin abun da Sauda tace game da Mami ba, k'ila da shi ke kusa da ita da ya karairayata, Alhaji ne yace cikin fada"ke ma dai me yasa kika gaya mata? Tun farko Zaid ya nema Alfarma gun mu yace kar a gaya mata, do u want to break her? Bakiga yanda abun yayi affecting Rafeeq ba? kinsan zai yi affecting dinta, maybe worse than Rafeeq, u shouldnt have told her" Sauda ran ta ya gama baci, amma ganin Mijinta da Zaid tsaye ya sa ta fara kukan munafurci, tace "Haba Alhaji kasan ba zan taba yin wani abun da zai cutar da su ba, ina son su kamar ni na haife su, Rafee'ah ce ta titsitsiyeni da tamabayoyi.

Rafee'ah ta sake ihu dakata " Daddy, Uncle Zaid, Hamma, wai me ke faruwa? Bana fahimtar komai, tell me this is not true, ku fahintar dani, ku ce mun Sharri aka mami na" kuka takeyi sosai, kamar ranta zai fita, Rafeeq ya rikota, yace "kiyi hakuri Rafeeah, shiyasa tun farko ban so a sansr dake, coz nasan cewa u'll be broken" ta dan zabura kadan, ta ma rafeeq wani kallon da be taba ganin ta mai ba, tace "Me kake so kace? Ka yarda da sharrin da aka ma mami? Ashe wayon banza ne dakai?" Da sauri ya kalleta don be tabajin irin maganar nan daga bakinta ba, sam be ji haushin ta ba, yace "Rafee'ah, i saw Mami with my eyes" da sauri tace "you must be stupid Rafeeq, da ka manta who ur Mother really is, ka manta the type of woman she is, ka bari anger yayi controlling dinka, look at you now, you are miserable" Alhaji yace "Rafee'ah, ki kula da yanda kike ma Yayanki magana, beyi k'arya ba, tabbas abunda sauda ta fada miki gaskia ne, Zaid ne ya nemi Alfarman a boye miki saboda kina iya shiga wani hali a matsayin ki na mace, amma tabbas Mamin ku Kwarto ta kawo dakin aurenta, Mamin ku ta dade tana cin amana ta" tsananin bacin rai Rafee'ah ta shiga, tace "whoever believe this is a stupid idiot, wallahi sharria aka mata, makiri ba ta inda be yin makircin shi, ta daga hannayen ta sama ta cigaba *amma Wallahi Tallahi Billahi*, _da yardan Allah da izinin Allah_, _Whoever did this to my mum is going to pay for it_, _ba zan taba hutawa ba har sai na bi mata hakkinta_ *Ya Allah ko yau na fadi na mutu Allah ka bani hanyar saka wa Uwata*, *Ya Allah ka amshi addua ta ka bani iko Ameen*
Wani irin dumm Sukaji a jikin su gaba ki daya, gaba ki dayan su suka ji a jikin su wanna addua ta Rafee'ah karb'abba ce, Sauda hankalin ta ya tashi matuk'a, Zaid da Alhaji Habib bakin su ya mutu murus, Rafee'ah ta juya da gudu ta haye sama tana kuka, Rafeeq kuwa hankalin shi ya gama tashi, abun da yake gudu ne ya faru. Zaid yayi saurin bin bayan Rafee'ah.

Sauda ta dafe kanta takaici goma da ashirin, Yaran Mijinta sun mammareta a gaban mijinta amma ya kasa cewa komai? Nan gaba k'ila belt zasu sa mata su mata mugun bugu, wai har Rafeeah ta daga hannu ta mareta, Rafeeq ma haka. Tabdijam aiko sun tsokalo wa kansu tsuliyar dodo, ita kadai tasan abun da zata musu, ba shegen bokan da zai ci kudinta wanna karon da kanta zatayi maganin su once and for all, ita kadai ke ta maganar ta.

A.Habib ya shigo dakin matar shi, tana ganin shi ta fara murmushi, Alhaji ka shigo, yace eh "Saude, hakuri nazo baki kan abunda yaran su ka miki, basu kyauta ba" sauda a ranta tace "jar uba, wato ba zai ban hakuri a gabansu ba don kar suce ya musu ba daidai ba shine ya biyota daki ko? A fili kuwa tace "haba Alhaji, ni ko daya ban rik'e su a rai na ba, ai da na kowa ne, na mata uzuri, tana cikin tsoro da rudani, amma wlh Alhaji bakomai" Alhaji har ranshi yaji dadi, yace "shiyasa nake son ki, nagode Saude."

Bayan Maghrib Uncle Zaid ya shiga dakin Rafee'ah da Sallama, ciki ciki ta amsa don tana ji haushin kowa a gidan, Kan side drawer ya zauna yayi yace "Rafee'ah" ta dan yi shiru kafin tace "kaima ka yarda da k'azafin da akayi ma Mamin mu?" Zaid yace "ban tab'a yarda ba Rafee'ah, Mami ba haka take ba" farinciki ya lullube ta, da sauri ta juyo inda Uncle Zaid yake zaune, ta riko hannuwan shi biyu tace "Uncle Zaid, ka taimake ni mu gano inda Mami take, Uncle Zaid so nake a wanke ta daga zargin da suke mata duka, har Daddy ya maidota dakin ta, Uncle Zaid so nake duk wanda yake bayan wannan manakisar ya wahala, ya wulakanta, Uncle Zaid ka taimake ni" Zaid ya sauke gwaron numfashi yace" Rafee'ah its not easy as u think, Wallahi ba inda ban neme Mamin ku ba, a wani zuciyata ta bani she's safe, only if i know where i can find her, zan fi kowa jin dadi" Rafee'ah tace "Uncle Zaid, dole mu nemo Mami, Zaid yace "toh Rafee'ah ta yaya?" tace muje mu ga Baba Alhaji (Baba Tj) na fi zaton yasan inda take" Zaid yace "wallahi nafi sawu nawa yace shima nemanta yake" Rafee'ah ta mik'e ta zura Hijab dinta tace "Uncle Zaid, i dont believe baba Alhaji, i have a feeling he's hiding something". Zaid yace "lets go findout" a tare suka bar Dakin don zuwa gidan Kakan su Rafeeq.

Rafee'ah ta durkusa gaban Kakanta, tana kuka kamar ranta zai fita, tace "Baba Alhaji, mesa ba zaka gaya mana inda Mamin mu take ba? Haka kake so mu cigaba da rayuwar mu ba Uwa? Kua da ranta? Baka ga yanda Rayuwar Rafeeq ya koma ba? Hankalin Baba Tj ya tashi, cikin in ina yace " wai waya gaya muku na san inda take?" Rafee'ah tace kaji tausayin mu ka gaya mana, watanni 4 kenan rabon mu da mahaifiya, please ka fada mana" Baba Alhaji yayi shiru, yace "nifa ba zan maida ma Habib Aisha ba, har sai gaskia ta baiyana da kanshi, sai Habib ya bambance. Sai a sannan Zaid yayi magana yace " Baba ba mu na nemanta bane don ta koma gidan Yaya ba, ina so na tafi da ita gida na ne, na san duk inda take kadaici ya ishe ta, amma idan ta zauna gidana time to time zata dinga ganin su Rafee'ah" Baba Tj yace Aa Zaid, zan dai gaya muku inda take amma bazai yiwu ka kaita gidan ka ta zauna ba, ai akwai matsi da takura ga ka da iyali" Zaid yayi saurin cewa "Haba Baba,kar fa ka manta ko bata auri Yaya Habib na ni me kula da ita ne, ma tsare mutuncin ta, donAllah baba kar ka hanani" Mama tace "gaskia ne Alhaji, ni na amince ma Zaid, ka fada musu" Baba Tj yace "Hakane, Aisha na gidan Goggon ta dake Malumfashi tsawon watannin nan, kuma har ta gama Iddanta" Rafee'ah tayi saurin rugume kakan ta don murna yace "tafi chan kar ki karya ni".

*KUYI HAKURI, ABUNDA YA SAMU KENAN YAU, BA KUMA NAN NA SO TSAYAWA BA,WANNAN YA FARU NE SABDA WASU DALILAI. INSHAALLAH GOBE DA SAFE ZAKU GA CIGABAN 29 ATTACHED TO THIS PAGE, DA NA SO BARI SAI DA SAFE, AMMA DA YAKE NAYI ALKAWARI SHISA, PLEASE BEAR WITH ME THANKS*
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg3⃣0⃣
Chapter 26 · 0% Book details