← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 95

Sashe 14

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare suka dawo daga Sallahr Asuba, tun a hanya ba wanda ya kula wani, Zaid fushi yake da yayan shi kan abun da ya faru da daddare, Habib kuwa ya san dole ran shi ya baci, don ba a kyauta mai ba da be dauki wani hukunci kan Hafiz ba, Zaid ba zai gane ba, be san halin mutane ba, ana iya cewa don Uwar su ba daya da Hafiz bane ya tura shi prison, Amma zai mishi bayani idan ya sakko. Suna shiga Gidan mai gadi ya ciro takarda ya mik'a ma Ogan shi Habib yace "inji Hafiz, jiya karfe 2 ya bar gidan nan" hannu na rawa Habib ya warware takardar, Zaid har yayi gaba ya dawo don yana son jin me Hafiz ya rubuta a wannan wasikar. A bayyane Habib ya fara karantawa, ga abun da ya rubuta nan ;
"*I know i'm a disgrace to this family, which is why i left you, na barku, zan shiga duniya, kar ku neme ni, ku mance kuna da wani danuwa me suna Hafiz, ba zan bari ku kara gani na ba, ku Shafe Hafiz Lema daga babin rayyuwan ku, saboda Hafiz Lema doesnt exist, Enjoy your lives without me brothers"

Ba Habib ba harta Zaid sai da hankalin shi ya tashi, tsakanin danuwa da danuwa sai Allah, Jini ba wasa bane, nan da nan Zaid ya fara hawaye, da gudu ya shige daki Habib ya bishi a baya, Zaid ya dauko wayar shi ya shiga neman layin Hafiz sai da ya mishi missed calls nawa kafin ya dauka, A dake yace Ya akayi ne Zaid? Zaid na kuka yace DonAllah Hafiz ka dawo, kar ka barmu, Wallahi na yafe maka, ka dawo, nd i promise we'll be like Nothing wrong has ever happened, donAllah, i need You. Hafiz ya fashe da dariya, yace "You dont need me oo, idan na tsaya zan cigaba da yi muku barna ne, gwara nayi nesa daku, kar ku sha wahalan nema na, don ba za ku taba binciko ni ba" Zaid ya fashe da kuka, Habib yayi saurin karban wayan, ya kara a kunnen shi, yace "Hafiz ka saurareni" Hafiz ya katse shi, yace "Yaya kar ka bata bakin ka, i've decided, be Happy brother kafin yace wani abi Hafiz ya latse wayar. Habib ya shiga neman layin yaji swtiched off ashe Hafiz fito da Sim card din yayi ya tauna a bakin shi ya zubar.

_Bayan Shekara Sha Biyar_ *(15 Years Later)*

Gidan Alhaji Habib Lema cike makil da mutane , da Alamu Biki akeyi, Hajia Aishatu na hango zaune kan Gado cikin wata tanfatsetsiyar Leshi, kamar yarinya yar shekara 20, sam girma be nuna a jikinta ba, shigowa akeyi ana mata Barkan an daura aure lafiya, wasu mata suka shigo suna fadin "ina Uwar Ango take, taje ta fito mana da Amarya?" ta tashi tana daria, tana fadin "Ni da kaina?" suka ce " ke fa da kanki Maman Zaid tunda da bakin ki kikace Zaid ba kani bane, d'a ne" tayi daria ta nufi inda aka tanada domin Amarya da kawayen ta Amare, ta shiga da Sallama suka amsa tace ince dai kun gama kimtsa min Amarya ta? Duk sukayi daria, Amarya Safiyya ta sunkuyar da kanta, Aunty Aisha ta nufeta ta dago kanta, tace "MashaAllah, Safiyyah kinyi kyau, ku muje Filin Launcheon din, an tattaru Amarya kawai ake jira"

Ango Engr Zaid Lema Suka shigo filin launcheon da Abokan shi, İnda aka tana da domin su suka zauna, Amarya ma aka rakota har gurin Angon ta, Bayan Aunty Aisha ta bude taro da Addua ta ma manyan Baki sannu da zuwa ta koma ta zauna kusa da Mijinta Alhaji Habib Lema.

Dj ya kunna kida gida ya kaure da sauti, gudu yake yana bangaje mutane, babban burin shi ya ganshi a filin rawa, Maalesh na kwala mai kira kan ya bar gudu ya ki, har hularshi ta fadi, Maalesh yace "ka ga hular ka ta fadi, ka tsaya ka saka" ina samm bai ji ba. Sanye yake da kaya komai iri daya Da Ango Zaid wato farin Shadda Kaftan mai Malummalum, yana zuwa Filin rawan ya wani ci burki, ya fara kallon kowa one by one, ya juya ya kalli Mamin su ta girgiza mai kai alamun kar yayi, ya kashe mata ido daya(wink), Abban su kuwa murmushi ya mai, Ya kalli Uncle Zaid Ango, ya daga mishi gira alamun go ahead haba kamar wanda aka sa ma battery, ya fara takunshi daidai da sautin kidan, abun be mishi ba har sai da ya cire Malummalum dinshi ya wulla ma Maalesh ya cigaba da rawan shi yayi gaba yayi baya. Ango Zaid yace ma amaryar shi "kinga mutumin ki na cizgar rawa ko?" da yake ba kallo take yi ba kanta a kasa yake tace wanene? Zaid yace "waye in banda RAFEEQ?"

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣7⃣

Iyakar tsorata Hafiz ya tsorata, ga case rike a hannun shi ba wurin boyo, amma da yake Hafiz namijin duniya ne sai yace "Aunty, ashe baki kwanta ba" kallon kai dakata ta mishi, tace "meye a hannunka?" yayi dan murmushi yace "Oh wai wannan? Sarka ne da yan kunne da na ba Yaya Ajiya kwanaki na dauki kayana" baki bude take kallon shi, tace "kai Hafiz kaji tsoron Allah, ajiya ka bashi ko kyauta? Ina cewa kayi ya sa a Lefen sa, shine gudumuwar ka?, kasan daukan abun wani ba tare da Izini ba Sata ne? Ya kalleta shek'ek'e, yace "Sata? Ta ina ya zama sata? I bought it da kudina, don na dauki abu na shine sata? Its mine anyways. Tace " its fine kai ka siya, i knw that, don ya gaya min, Hafiz Ka riga ka bashi, shi kuma ya bani, ko shi baida iko akan shi, its no longer yours". Yace "Madam, its mine, noone can get it from me, not even your husband, saboda haka sai da safen ki, idan kin isa ki gaya mishi ya zo ya amsar miki". Ya wuce ya barta tsaye.

Aishatu da dafe kai, wai Hafiz ke gasa mata magana haka? Duk Habib ya ja mata, da be amsa ba tun farko, da wannan ranar ba tazo ba. Tabbas ta san duk cikin Sark'ok'in ta ba wanda ya kai na Hafiz? to ya za tayi tunda ya bukaci abin shi? A fili tace "Allah shi kyauta" Zuciyar ta ta ke waswasin gaya wa Habib? Toh tace mishi me?Ta haddasa fitina tsakanin su? Balle shi Habib dake matukar son Hafiz, ko Zaid be so haka.
Kuma bata son wani abu ya kara shiga tsakanin ta Hafiz, don tsakaninta da Allah tsoron Hafiz takeji, yanayin sa na bata tsoro, a ranta ta kudiri cewa ba zata gaya ma kowa ba, idan yayi wari sa ji, ta dauki Blanket dinta ta datso kofar ta, tayi dakin mai gidan ta.

Da Sassafe Hafiz ya je kasuwa don saida Sarkar nan, kasancewar ta tsaddadiyar sarka tun shekara biyar da suka wuce, da aka auna Kadan ne babu cikin Miliyan, Naira dubu dari tara da goma(910).
Hafiz ya cire 650 ya ba yan Malaysia ya rike sauran da niyyar zai je Lagos Gambling kila ya ninka kudinshi so biyar (Allah ya shirya ka Hafiz.)

Matashi dan kimannin shekaru 22 yayi sallama a kofar parlon Habib da ke zaune shi da iyalan sa, Habib ya dago kai tare da amsa Sallaman, kallon shi kawai yake yi yana son tuno fuskar, Aishatu ce ta mike tace "Zaid?" Rafeeq ya sake Ihu da karfi, da gudu ya nufe shi ya je ya rungume shi, shi ko Zaid ya daga shi sama yana "Oyoyo my boy" i've missed you so much, look at you" Rafeeq dan shekara 5 yace "welcome home Uncle Zaid" yace "Thanks son, ina baby Rafee'ah? Cikin hausan shi da be fita Rafeeq yace gata chan tana fushi wai ka daukeni" Zaid ya sauke shi yace "Ohh my baby come here" da gudu ita ma tazo ya dauketa, suka ida shiga parlorn, Sai da ya durkusa har K'asa ya gaida Aishatu da ke ta faman jera mishi sannu da zuwa, kafin ya kalli Yayan shi yace "Barka da Rana Yaya" Habib baki sake kamar soko yake kallon Zaid, kwata kwata ya chanza kama, kamar wanda aka ma wankan Engine yayi Jazir yayi kyau. Suka gaisa, kafin kace kwabo Aishatu ta cika shi da abinci.
Kamar daga sama Hafiz ya fado Parlorn, da Zaid ya ci karo, kamar wanda yayi Gamo da Aljan yayi saurin juya wa, ashe Habib na kallon shi, yace "Hafiz ina zaka, baka lura da danuwan ka bane? Ba yanda zaiyi dole ya dawo.

Wani murmushi ne kan fuskar Hafiz mai wuyar fassaruwa, yace " Hello brother, its good to see you again, welcome home"
Zaid ya hadiye miyau, ya shiga tunanin baya, komai ya dawo mai sabo, ya sake hade wani bakin miyau, be san murmushin da Hafiz keyi na meye ba, a ranshi yace Allah ka min tsari daga Sharrin me sharri" a fili kuwa yace "Thanks, its good to see you too".

A year Later(Bayan Shekara 1)

Zaid ya gama bautar kasar shi a shekarar shi ta 23, Hafiz kuma a Shekara 24, Zaid Ya zama wani Azabbaben Guy, tun yanzu mata ke kawo mishi hari, Aishatu ta mishi maganan Masters yace, sai yayi settling. Rafeeq da Rafee'ah na ta zuwa school, da aji daya Rafeeq ya fi Rafee'ah, Dukkan su Allah yayi musu Baiwa na Kokari...
Chapter 14 · 0% Book details