← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 95

Sashe 84

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ya kallesu yayi dan guntun tsaki, yace "Ba abun daria bane, duk yanda na so to get along with her, i just cant, shes Annoooooying" Daria Daddy yayi, Uncle Zaid yace "shiyasa nace zata zauna maka 'yar zaman daki" Rafeeq ya gwalo ido yace "Wa? Aikuwa da wata rana na mata dukkan tsiya" Maalesh ya bude baki yace "Nenen?" Rafeeq yace "Ita fah" Maalesh yace "aikuwa kamar a kunnenta" "in ka fasa tsoron ta nakeji ne dama?" Maalesh ya fashe da Daria yace "Aa fa guy, kar fa kamanta randa tayi shirin Buje da gatari a hannu ka tsorata fa" Rafeeq yace "Randa tayi shigar 'Yan daba dai, everyone in my shoes will do the same, daga ganinta ta ta6a Daba" Zaid ya murtuk'e fuska yace "Rafeeeq" da sauri Feeq yace "Sorry".
Haka suka iso Katsina Lafia, straight Guest House suka nufa inda aka ajiye Abii da mutanen shi, Suna sauka Rfaeeq ya Sanfe ya tari Achaba ya haye sai Gidansu inda aka gama Mothers day, da sauri Feeq ya hau sama, haka ya dinga k'etara Mata har ya shiga dakin Seebi, wayam be ga kowa ba, ya lek'a dakin Mami, Zaune Mami take da Friends dinta su Mom din Maalesh da wasu yana ganinsu yayi saurin juya wa, don bai san surutu, amma kash Mom din Maalesh ta ganshi tace "Come here boy" sum sum ya shiga dakin kamar wanda yayi k'arya, Mom tace Yadai? Murya k'asa k'asa yace "Mom Naseebah nake nema" ta harareshi tace "If i slap you ehn, baka ga Aunties dinka ba? Cant you greet?" dan guntun tsaki yahi ya kallesu tare da Turo baki yace "Ina wuninku" duk suka amsa cike da faraa" ya juyo ga Mom din Maalesh yace "Mom where is she?" Mom ta ja kunnenshi tace "Listen to me boy, you are not to see the Bride sai bayan an daure Aure kaji ai?" Rafeeq ya turo baki kamar zaiyi kuka ya kalli Mami da fuskar tausayi ta ta6e baki tace "Kai da ita ba ruwana" juyawa yayi yana tafiar yara idan an hanasu abu, Mom din Maalesh tayi daria ta kalli Friends dinsu tace "Kun ganshi ko? Shine fa Angon, wai Amaryar sa ya ke nema" su ka kalli Mami "wai dagaske Hajia Aishatu?" Mami tayi daria tace "gashi Mom dinshi ta fada". Duk mamaki ya lullubesu.
"Yauwa Anee, ina Baby?" Aneesa tace "Yaya Rafeeq ta tafi gida bayan an gama Mothers Day" ya dan bata fuska, wani Gida?" "Gidan Nene mana" "Oh shit!" ya fada tare da yin hanyar k'asa da gudu yana mita.
°°°
Gidan Nene cike da dangi, kowa da abunda yakeyi wasu daga ciki kuma ana yankar Alaiyahu da zaayi Miyar Yinin Biki, wasu na 6are Ledar tuwo, su Nene kuwa an shige Dangi ana ta labari a lokaci guda kuma tana bada Umurni. Be san gidan cike yake ba, Cikin muryan shi yayi Sallama tare da kusta kai lokaci guda, Nene kadai taji Sallamar sa, sai ganinshi kawai sukayi a kansu, yayi nadamar shigowa da ya ga idanuwa sun mai chaaa, ji yake kamar ya juya, haka ya tsaya musu k'ikam, shi be juya ba, shi be ce dasu komai ba, Goggon Seebi tace "Wanene wannan ya shigo mana gida ba Sallama" Daure fuska yayi tamau, Nene tace "Ya fayi, haka yake sallamar sa kamar Wusir, Dunkum kike gani, Dangin Tsaka, Miskili yafi mahaukaci ban haushi" inji inna tani "Toh fa Shikuma fa?" "Shine fa Angon Seebi" wata Yayar Ummi tace "Ahh Nene kice duk kirarin nan ba a banza ba, ashe kishi kikeyi, Ya dauki Seebi yace beyi dake" Nene ta ta6e baki tace "Ni me zanyi da Dunkum? Ai Sai Seebin da ta ga zata iya" da Ummi suka hada ido, ta mishi Inkiya da ya gaida su, guntun tsaki yayi, a hankali yace "Ina wunin ku" suka amsa da faraa, Kakkanin Seebi suka fara jan shi da wasa, Yak'e me kama da Kuka yakeyi, nan ya samu ya sanfe daga gidan.
Tsaki ya buga da k'arfi da ya kira Wayar Seebi karo na 6 ya ji shi kashe, shi gaskia ba zai iya kwana be ganta ba, Wayar shi ya zaro ya latso Wayar Uncle Zaid "Boy ya?" Cikin Marairaicewa yace "Ba gani nazo gidan Neh-neh ba, na ga Mata sunfi 60, wai a gidan Neh-neh zasu kwana, kuma Baby na cikin su, duk sun matse ta, sun takura mata" Uncle Zaid yace "Boy ban san rigima, ba daga yau shikenan ba?, Danginta ne" Kamar Zaiyi kuka yace "Please Uncle Zaid, do something" ajiyar zuciya yayi yace ya kake so ayi to? Cike da shagwaba yace "Ni ta koma gida" Zaid yace "Ohh saboda ka hanata sukuni ko?" da sauri yace Aa Wallahi, ni da zan kwana Gidansu Lesh " Good inji Zaid ya latse wayar ya kira Wayar Nene, "Halo Zaidu Bawan Allah, ango, kayi hakuri ban hallarci bikin ka ba, Yanuwa na daga k'auye sunzo ne"Murmushi yayi yace "bakomai Nenen mu, ya taro? Ya jamaa?" "Alhamdulilah ya naku?" "Lafiya lao Nene, nace dama Seebi da k'awayenta su je chan Gida su kwana, an gyara musu daki Biyu" Nene bata kawo komai ranta ba tace "kamar ka san a gwamutse muke, bari ko su shirya su koma chan" bata kashe wayar ba ta shiga kwadawa Seebi Kira ta shirya su koma Gidan Lema.
*********
"Baby" jin muryar shi kawai tayi a tsakar Gida, Friends dinta sukace "lahh ga Ango" Mur ya sha, saida Seebi ta harareshi kafin yace "Sannun ku fa" su ka amsa sunso Magaanr tasu yayi Nisa, amma ba hali, Nasibah tace "zamu shiga ciki" yace kije ki rakasu ina jiranki" zatayi magana ya tsareta da idanun sa, Alright tace tayi cikin gida da Friends dinta, shi ko dakinsa ya shiga ya ciro Key din motarsa ya bude ya shiga tare da kunna AC, ya ga fitowarta, yana ganin yanda take dube dube ta window da alamun shi take nema,horn ya mata da ya dan firgita ta, a hankali ta tako ta side dinshi, a taka'aice yace "Get In"
tace "Hamma Please"kallonta kawai yayi, ta san maanar kallon da ya mata da sauri ta zagaya ta bude motar ta shiga, Gyara zamanshi yayi ya maida hankalin shi kachokam kan ta, yana binta da kallon so da k'auna, sadda kanta tayi k'asa, ya sa hannu ya kamo hannayenta duka biyu da suka sha zanen Lalle, ta yi ta kwace hannunta ta kasa, ya fi minti 3 a haka shi be tanka ta ba, da k'yar bakinta ya lalubo " Ina jin Bacci" Murmushi yayi yace "Baby, kin kashe wayanki, kin hanani ganinki and now kina jin bacci? Oya zo ki kwanta" ya karashe tare da nuna chest din shi, Ido ta ware tace "Hamma"yayi Murmushi yace "Alright, kije ki kwanta, I love you so much baby, I got you, I got Us" Smile tayi tare da fadin "Goodnight" ta bude murfin k'ofa zat fita ya rik'o hannunta daya ya kai bakinshi yayi kissing, Lokaci daya Seebi ta daburce, ya sake hannun tare da cewa "Goodnight Baby" da sauri ta fita ta bar Motar tayi cikin Gida, shikuma ya ja Mitar ya fita daga Unguwar ya nufa Unguwar su Lesh.

SATURDAY 11:30AM
Chapter 84 · 0% Book details