← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 95

Sashe 82

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daria sosai sukeyi, Rafee'ah tace "Kakar ki na da abun daria, Allah dai ya ja kwana" Seebi tace "Ai zama da Nene sai hak'uri, wanda zai zauna da ita sai ya kai zuciya nesa, don haka zata dinga dasa miki kayan haushi, idan Nene ta k'unsa miki wani abun to sai kinyi kuka" Aiko Rafee'ah ta tuntsire da daria, sai da tayi me isarta kafin ta tsagaita, ta kamo hannun Seebi, ta murza a hankali ta na me Kallonta cike da So da k'auna, chan kuna ta rungume ta sosai ta na shafa mata baya tace "KE ALHERI CE Nasiba Muhammad, kin cika min buri na, Everything is now in place, now i can rest in peace, kin gama min komai, Allah kadai ne zai biyaki da daukacin Zuriar ki, kun kasance Haske a cikin Zuriar Lema, kun kasance abun kwatance a Alumma, kinyi Jihadi, kin sadaukar da Rayuwarki akan mutanen da baki san ko su waye ba, dalilin ki abubuwa da dama Sun faru, Ina Alfahari dake, Ina kuma miki Fatan ALHERI, Allah ya hadaki dauwamamiyar farin ciki, Allah ya tsare ki da Yayana" Seebi tace "Allah sarki Sis Rafee'ah, zaki sani kuka, Amin ya Allah, ke kika bani hope a Lokacin da nake zaton hakan ba me yiwuwa bane, Wannan shine kallan tawa Jarabawar, ba dabara ta ba wayau na" ba zan gaji da gaya miki *KE ALHERI CE* ba" Seebi na daria ta rungumeta tace "Kema Alheri ce Sister Rafee'ah, without you, none of these would have Happened" itama Rungumeta tayi ta na shafa bayanta a hankali, chan tace "Nasiba, This the last time you'll see me, Its been a priviledge to know you though i didnt get to spend more time with you, i wish we met while i was still Alive, but Nevertheless I Thank Allah for making these all possible, Cikin ikon shi, Izzar shi da Zatin shi ya sa kike mafarki dani, Ba abunda zance sai Alhamdulilah" Nasiba kuka takeyi sosai, tace DonAllah ki tafi, you've become part of me, dont leave me please" "Ohh Nasiba, dont cry Habibty, ina ma laifi we met for the 4th time? You'll miss me but abun zai zo miki da Sauk'i, tunda gaki ga Hamman mu, in kina tare dashi, zaki dinga ji kamar kina tare dani ne, you'll see him in me" Seebi ta wurga idonta ta sama tana cewa "That your Arrogant pompous Brother, he makes me sick" Daria Rafee'ah tayi sosai tace "Alright enough, i have to go now, but ina da Sak'o ga kowa" ki gaya ma Daddy nace " Ya gina Massalatai da Islamiyoyi da Rijiyoyi, ya kuma dinga Sadaka da bada Zakkah, ya kuma dinga Ciyar da Marayu " Nasiba tayi Murmushi ta maimaita abunda Rafee'ah tace, kamar a kunne Daddy zan gaya mai" tace yauwa Mami kuma kice nace ta cigaba da Hak'urin da na santa dashi, ta kula da Mijinta, ta zama Mace ta gari, kar rudun duniya ya sa ta shagala, kar Kawayen Banza su sata bin bokaye don Mallakar miji ko wani abun daban, ta Tsare Ibadunta, ta rik'e Adduoin InshaAllah zata ci ribar Rayuwa" kamar dazun Nasiba ta sake Maimaita abun da Rafee'ah tace, Fee'ah ta cigaba da cewa "Uncle Zaid the Noble Gentleman,wanda zai kuntata ma kanshi don ya faranta ma wani, kice mishi Allah kadai ya san yanda zai biya shi, Allah ya Saka mishi da Alherin sa, Ya raya mishi Takwara ta, ya bashi mata ta gari wacce zata kula dashi kamar yanda ya dade yana kula da mutanen da ke kewaye dashi, Allah ya biyashi da gidan Aljannah" haka Nasiba ta sake maimaita abunda Fee'ah tace, Rafee'ah tayi daria tace My Next message is for Nene, kice mata nace "Ba kamarta, Allah ya hada mu a gidan Aljannah Firdausi" Seebi tayi daria ta maimaita, Lastly Hamma na, kice mai nace "Stop getting angry Easily, Dont get Mad at anything, dont be Sad anymore, Live your Life, and Be happy, I love you so much Hammana" haka Nasiba ta maimaita sak'on Rafeeq, "And you, i dont know if i'm supposed to ask you this, because you've done alot for me and My Family, but i really want you to do this, I want you to take very good care of Hamma Rafeeq, i want you to love him for the rest of your life, Please" Sister Rafee'ah me kike cewa ne haka? Wannan hakkin matar da zai aura ne, how am i supposed to take care of him for the rest of my life? I'm getting married In 2weeks time, i cannot promise you this, i'm sorry i cannot do this, i shall take care of my Husband" Murmushi me kayartar da Fuska Rafee'ah tayi, ta lumshe ido a Hankali tace "Goodbye Nasiba, Be Happy" "Wait Sister Rafee'ah, kar ki tafi donAllah"
************
Cikin Barcinta taji ana shafar k'afarta, bata son tashi daga mafarkin don tana sa ran sake ganin Rafee'ah, amma sai dai kash tasan Rafee'ah ta tafi kenan don baccin ya fita daga idonta, a hankali ta bude idonta ta sauke su kan mutanen da ke tsaye kanta, cikin hanzari ta mik'e tsaye tana mitsitsika ido,ta bisu da ido, ta kai dubanta ga Nenenta tace "Lafiya Nene?" Nene tace "Sambatu kikeyi cikin bacci Seebi, kamar kina magana da wata cikin mafarkin ki, ina Sallahr Dare naji kawai kin fara maganganu, na zo daka miki duka amma ko shurawa bakiyi ba, haka na tsaya kanki jin kina ta turanci na dinga miki addua, dana ga abun ba me karewa bane ya sa na je na kwankwasa ma su Aishatu nace baki da lafia, tun kafin su karaso ta kira Dunkum da Zaidu bawan Allah tace su zo a kaiki Asibiti, shine ma fa mukazo dob cicinbar ki, sai Mukaji kina wani magana Sai Zaidu yace a tsaya yaji kamar ana son Isar da Sak'o a garesu, tsaf muke jin Amsar da kike badawa amma ba ma jin abunda ake ce miki" Seebi ta tashi tsaye tana salati, Mami ta matse hawayen ta tace "Nasiba da Rafee'ah kikayi mafarki ko?" kanta a kasa ta daga kai alamun Eh" Mami tace "For howlong kike mafarki da ita, saboda yanda naji kike magana kamar you two are so close to eachother" "Nayi mafarki da ita So 4 ko 5" Allahu Akbar, inji su, Rafeeq ya matso kusa da ita, ya tsura mata ido, yace "Naseebah tell us everything you know, kar ki boye mana komai" Nasiba ta kwashe komai tun farkon Mafarkinta da yanda ta nemi Alfarma taje ta biya mata bashi a makaranta, da yanda tasa bincikar Rayuwar R-lema, da yanda ta sa ta shiga rayuwar shi, da yanda ta taimaka mata gun tona Asirin Saude har zuwa rana ta yau da duk sukaji komai" Allahu Akbar kakeji da kirari ga Ubangiji Allah, abun Mamaki kamar Almara, ba su taba jin irin haka ba ko a Mafarki. Rafeeq ya rasa tunanin me zaiyi ya rasa sukuni, Wacce iri ce Naseebah? She did alot for him, how he wish he could show her love and Appreciation, he loves her so much, and after this wani girmanta ya karu a idonshi, wani sonta ya sake ratsa shi, wani kaunarta ya shige shi, hawaye ya zo mai da sauri ya juya ya bar dakin, Zaid ya bishi da ido ya na tunanin wannan abun Mamakin" Daddy yace "Nasiba My Child, Allah ya miki Albarka, naji Sakkon diyata Rafee'ah kuma InshaAllah gobe zan fara aiwatar da yanda tace Allah Kuma ya gaffarta mata ya sa Aljanna ce makomarta" duk suka amsa da Amin, Daddy yace "Oya muje mu kwanta is getting late" Mami tace "No, i'll sleep close to my daughter today" Daddy yace "Babanta kuma fa?" Mami tayi daria tace "yaje hutu" duk suka sa daria, Daddy ya fita, Mami ta kwanta gefen Seebi tana shafa kanta, Nene ta shimfida Bargo a k'asa tace "ki maidata ciki karshen shigewa jikinta".

Akwati Set1 (Guda 6) Mami ta hada, komai ya ji, Mami tace " idan zaka wuce Kaduna sai ka tafin ma su Ummin Anan dashi, duk da tace ba sai an kai ta gani ba, amma yakamata a bata hakkinta na uwa" Nene tace "Ni da kun bi ta tawa tunda Ran Jumaa zasu zo ba sai an sha wahalar kai kaya Kaduna ba" Mami tace dai a kai musu su gani.
Su Miemee da Usheey sunzo ganin lefe, suna ta murna don Seebi tayi Goshi, kaya sai sambarka, nan suka ritse Uncle Zaid a Parlor suna zolayar shi, dariya kawai yakeyi, Miemee tace "Uncle Zee ya maganar Dinner? Kasan dai biggest hall of them all zaa kama mana, Soli Center nake ma bayani, yayi daria yace "Kar ku damu, ga Son nan kuyi magana dashi, zai yi komai" Meemee ta waiga taga Rafeeq na shigowa Fuskar nan murtuk'e, a ranta tace "kai dai ka sani".
Chapter 82 · 0% Book details