← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 95

Sashe 47

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanan shi biyar be ganta ba, so da dama zai zo bakin k'ofar gidan yaga ko zai ga fitowar ta amma shiru, ya mata text kala 2 ba reply, wayarta in ya kira har ta gama ringing baya dauka, a rana sai ya jera tsaki fiye da dari, haka kawai yake jin kanshi wani wani iri, gashi Maalesh ba ya nan, haka kurum yaji he wants to see her, zumbur ya tashi daga kan gado, ya zura takalman shi, fita yayi daga gidan be dauki Mota ba, ya taka har k'ofar gidan Nene, mintin shi sha biyar tsaye gaban gidan, ya rasa yanda zaiyi, to wai ma ya ganta yace mata me? Tsaki yayi ya juya, zuciyar shi tace to ko lafia dai? Ko ciwon Nene ya tashi ne shisa ya daina ganin gilmawarta, ko a Unguwa sometimes ya kan ga wucewarta zuwa shago, dawowa yayi, ya tura k'ofar gidan, ya shiga Chan k'asan Mak'ogaro yayi Sallama, Nene na zaune tsakar gida tana gyaran wake ta amsa Sallamar tare da cewa Bismillah, kamar ya juya da ya ji muryar Nene, amma be san me ke tunzura shi ya shiga ba, cikin tafiar shi ya ida shiga gidan, Idon Nene a kan shi, a ranta tace "Yau su Dunkum ne a gidanmu" ba yabo ba fallasa tace k'araso ga wuri ka zauna, kan kujera ya zauna, chan taji yace "Sannu fa" kallon shi tayi tace "Ahh! Ai kai ke da Sannu me ciwon baki" be tanka ta ba, suka zauna jugum ita kuwa ta cigaba da tsintar waken ta, shi ko waige yake ta inda zai ga ta bullo, amma shiru, ko duniya zata nad'e ba zai iya tambayar Nene inda take ba" sun kusa minti 30 ba wanda yace ko 'kala, Nene ta yi Kamar bata san da kowa gun ba, sai 'yan wakokin ta takeyi masu kama da habaici (kuji min Nene kamar wata yarinya)haka ya k'araci zaman shi ya mike sai da yayi dan guntun tsaki kana yace "sai anjima" kamar jira take tace "mu jima da yawa" ya juya ya fita, ta bi bayanshi da gyatsine tace "Dunkum dangin Tsaka".

"Assalam Alaikum" ta fada cikin Siririyar muryar ta, Mami na zaune ta yi firgigit ta tashi don Nasiba ta gani tsaye gabanta da kwano a hannu wasu lokuttan tana rikidewa ta koma Rafee'ah, da Sauri ta amsa Kwanon Hannunta, ta rungumo tana shafa fuskar ta tana hawaye, Sandadar Nasiba tayi, ta kasa tabuka komai, chan Mami ta dawo hayyacin ta, da sauri ta ja baya tare da fadin "I'm so sorry, kina min kama da diyata, kiyi hakuri" Nasiba ta girgiza kai tace "lahh bakomai" ta jawo hannun ta ta zaunar da ita, suka gaisa, tace "Ummi ce tace ako miki" ta bude Coolern tana fadin me muka samu? Ahh Alkubus? Aikam Nagode sosai" ta dan ballo tasa a baki" gashi kuwa yayi dadi" Murmushi kawai Nasiba keyi, Ayman ta shigo parlon dauke da Doll babyn ta a hannu tana tafia dagwas dagwas, da alama tafiar batayi kwari ba, Nasiba ta tsura wa 'yar diyar ido, har Ayman ta tako kusa da Mami, Mami ta dagata sama, "Ayman baby na kin tashi? wa ya sauko dake daga kan gado? Yarinyar dai lafe wa tayi jikin Mami, Nasiba tace "Ayman sunan ta? tace "eh" Nasiba ta mik'a hannu tace "Zo nan Ayman" ga Mamakin Mami Ayman ta nufa gun Nasiba, Mami tace lahh kin ciri tuta, k'uiywa ne da ita, amma tazo gunki, ba ta yarda da kowa, ko gidanku mukaje bata yarda ta sauka k'asa zata mak'ale a jiki, daga ni sai Baban ta je daukan ta" Nasiba tayi murmushi tace "haka yara suke ai" Mami tace "to ya karatu? Wane Course kike?" tace "MicroBiology" "Allah sarki ajinki nawa?" tace "Aji na Daya" idon Mami ya kawo ruwa, Nasiba ta lura tace "Mamin Ayman lafiya?" Mami tace "you see, Diyata bata samu ta gama Makaranta ba, da ajinta biyu zata uku" Nasiba tace "Allah Sarki, Aure tayi ne?" Mami tayi murmushi ne ciwo, tace ta koma ga Mahalici, shekarar ta daya da rabi da Rasuwa" Nasiba ta rausayar da kai cike da tausayawa, tace "Allah Sarki Ubangiji Allah ya mata gafara, ya sa ta huta Amin" "Amin Nagode, shekarar ki nawa?" tace "19" tace "ita kuwa tana da Shekaru 20 ta riga mu gidan Gaskia, Shes just like you, ba wai kuna kama bane, aa, kawai ina ganinta a cikin ki, i see alot of her in you, shiyasa lokacin dana ganki i was so emotional, ki dinga sata a adduar ki kinji? Murmushi Nasiba tayi tace " InshaAllah, Ya Sunanta?" Murmushi Mami tayk tace "Sunanta Rafee'ah" zabura tayi ta zaro ido tace "Rafee'ah Habib Lema?" da sauri Mami ta gyada kai hadi da cewa "Eh itace, kinsan ta ne?".

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

*Wannan Page din nakune Masoya _Nene Mamman(Nenen Seebi)_ Nene loves you all❤*

Pg4⃣3⃣

Nasiba ta fara sheshek'ar kuka ta nuna Mami da yatsa tace "kece Mamin Rafeeq?" da Sauri Mami tace "eh nice Nasiba, kin san Rafeeq ne?" Allahi Akbar da sauri Nasiba ta rungume Mami tana kukan farin ciki, Mami tarasa gane me Nasiba ke nufi da kukan da takeyi ne, daga bisani ta tsagaita kukan da takeyi, ta share hawayen ta, Mami ta tsura mata ido, tace "Nasiba me yasa ki kuka? Shin dama kinsan Rafeeq da Rafee'ah? Ki min magana ծiyata. Wani guntun tunani tayi ta girgiza kanta da sauri tace "aa ban sansu ba" ta mik'e da sauri tace "barin je gida Umminmu na Jirana" ba ta jira cewar Mami ba ta juya zata bar gun, da azama Mami ta rik'o hannun ta tace "Nasiba kar ki min haka, na san kina b'oye min wani abu, daga yanayin da kike a yanzu nasan kin san su, dukkansu, sanin da kika musu Sosai ne, ki fada min, Ya Rafeeq yake? Ba ta bari sun hada ido ba, murya na rawa tace " ni bansan su ba" haka kurum taji bata yarda da ita ba, akwai abin da ta ke 'boyo, ya zaayi da farko ta nuna ta sansu har ta na fada mata sunayensu yanzu kuma tace bata san su ba, ba zaiyiwu ba, yanda Nasiba takeyi ya nuna cewa tasan wani abu game da Rafeeq.

Ta kamo hannunta tace "Nasiba ke da Anan kadai ne gun Mahaifanku ko? Toh haka Rafeeq da Rafee'ah, na rasa Rafee'ah, K'addara ta rabani da Rafeeq, Ina sonsa sosai, ina so in san Halin da yake ciki, tun bayan tafian Uncle dinshi, bana samun Details yanda ya kamata, Misali Ummin ku ke cikin situation dina, zaki so ki ganta cikin matsanancin hali?" ta nuna zuciyar ta da hannu ta cigaba da cewa "You see dis heart of mine? Its Empty, you have no idea what i've been through, i mean what i am going through, i've Swallowed alot, ki taimakeni, Help a Helpless Mother please".

Nasiba ta isa gareta ta rungume ta, kuka takeyi sosai, ta dago ta share hawayen Mami, tace " Mami ki bar kuka, i will tell you everything i know about Rafeeq, da yanda na sanshi, Komai" jan Mami tayi har kan kujera, ta dauki Ayman ta sata a baya, da hijabin jikin ta ta goya ta, ta fara rirriga ta har ta koma bacci, ta kalli Mami tace "ina zaa kaita? Da hannu Mami ta nuna mata cikin daki, Nasiba ta kai Ayman daki, ta dawo ta zauna kusa da Mami.

"A Makaranta na fara ganinshi, shi da abokin shi Maalesh, ina tare da k'awayena muna neman abun hawan da zai maida mu Cikin Gari.............................................." tsaf ta kwashe komai da ya wakana tsakanin ta da Uncle Zaid da Rafeeq ta gaya mata daga ranar da ta fara ganin su har zuwa rana irin ta yau. Abu daya ta boye mata, Mafarkan da takeyi da Rafee'ah, bata gaya mata tana mafarki da Rafee'ah ba.

Mami tayi Murmushi tace "Its a Small World afterall, So kakar kice Nenen da Zaid ke ban labari? Wacce ta bashi kuka da daddawa?" kai Seebi ta daga, ta riko hannunta tana murzawa tace "Labarin da Maigadin Lema ya baki, dukda ba ki gaya min me yace miki ba, kin yarda zan iya aikata abun da ake zargina dashi?" Murmushi Nasiba tayi tace " Bansani ba, and i wont Judge you, but i know a responsible Mother wont do that at her Matrimonial Home" Murmushi Mami tayi tana jin son Nasiba har ranta, irin son da take ma Rafee'ah tace "kinsan lokacin da na fara ganinki, naji ina sonki, like i told you I see Rafee'ah in you, Nasiba shin zaki zama diyata? We'll you make me feel like a Mother again? Kuka Nasiba ta fashe dashi, ta rungume Mami ta na daga mata kai, tace "Mami nah, you are my Second Mom" kukan farin ciki Mami ta fara yi "Seebi na, ina sonki kinji?" nima ina sonki Mamina". Daria sukayi duka.

Nasiba tace "Ayman fa? Kin sake aure ne? Mami tayi murmushi tace "anya zan sake Aure kuwa? Bana tunanin zan so wani ծa namiji baya ga Daddyn su Rafee'ah" da sauri tace "Aa Mamina kar kice haka, ba me cire rai daga rahamar Allah, kar kiyi Mamaki zaki koma dakin ki, abu ne fa na Allah, bana so kina cewa haka kinji Mami na" Murmushi Mami tayi ta k'ara jin son Nasiba a ranta, tace "Rafee'ah-Aymana taci sunan Marigayiya Rafee'ah, Ayman diyar Zaid ce, be taba gaya miki yana da ծiya ba? tace "aa be fada min ba" Mami tace "Matar shi ta rasu Shekarar da ta wuce, bayan suna ta Rasu" cike da tausayawa tace "Allah Sarki, Allah ya gafarta mata, ya sa taci Albarkar Haihuwa, ita kuma Allah ya rayata" "Ameen Ameen" Mami tace "to kodai Yak'i gaya miki yana da d'iya ne don kar kice ya miki tsufa, ba kya son tsoho? Cike da kunya da jin nauyi tace "Lahhh Mami" tayi saurin boye fuskarta jikin Mami don taji maganar wani iri, ita kuwa Mami sai dariya take mata.
Chapter 47 · 0% Book details