← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 95

Sashe 18

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hafiz ya shigo da Sallama, ya zauna tare da gaida Yayan shi, Yaya Habib yace "Oga Hafiz, ya aikin yau?" yace "Alhamdulilah yaya, Tea zaka sha? Yace eh, as usual, ai nafi 20years ina shan tea duk dare" Hafiz yace "haka ne, nima barin dauko cup inzo mu sha" ya mik'e don zuwa kitchen, ya samu Opportunity ba zai yi watsi da hakan ba, a kitchen ya iske Aishatu, yace ahh Mami Abinci kikeyi?" tace Hafiz an shigo? Wallahi dan rigimar nan nake dafa ma indomie kafin ya shigo gidan" Hafiz yayi daria yace "dan Zaid dan rigima, ina baby na?" tace "tana daki, tana sanaar ta, kasan in ta dauki wayar ta" yace na ma kusa chanza mata waya, Iphone6s, tayi chatting din da kyau" tayi daria yace "ina mugs dinnan nima yau zan bi yaya in sha Shayi?" tace Shayin Ibada,tare da miko mai Kofin tangaran".

Ya faki idanun yayan shi da yake ta duba jarida ya juye maganin nan tas, ya tsiyaya ruwan zafi cikin kofin, yace yaya "bismillah" wai Hafiz kai ka zuba min tea din? Ai da ka bari Maminsu ta zo ta zuba min" yace "no yaya bakomai", shima ya tsiyaya ya zauna suna shan shayi suna Fira.

Asuban ci ta ma Garin Jigawa gun bokan na kan tudu, kasancewar yau Weekend: Bayan ta gama ma boka kirarin da ta saba mishi, tace " na kan tudu aure zanyi" ya kalleta yayi daria yace "naga hakan saude" tace "ai ni nasan akwai nasara, abunda nake so da kai na kan tudu, bana son a samu mishkila, kar ko ya tambayi dalilin ko ba'asin auren nan, kar kowa yace don me, inshort a rufe ma kowa baki kan Auren nan" daria ya tuntsure da, yace "an gama" yayi yan tsubbace tsubbacen shi yace komai daidai ne" ta ciro kudi masu yawa ta dire mishi tare da yin godia.

Hankalin Hafiz ya dan kwanta don yaga kwana biyu har sun wuce ba abunda ya samu Yaya Habib, tabbas kam Sauda ba wani mugun abun zata ma yaya ba.

Ji Yayi kawai ya na son zuwa Office din da matar shi ke aiki, Zuciyar shi na tunzura shi, yace da Driver "mu tafi Office din Madam" Direba Yayi mamakin Umarnin Alhaji, amma be tanka ba yayi Ofishin Madam for the first time da Alhaji.

Alhaji Habib ya fita ya nufi cikin Office din ba tare da yasan me zaiyi a ciki ba, yayi knocking bakin k'ofar Secretary, Sauda da ke ciki tace "yes come in" Alhaji Habib ya tura kofa tare da Sallama. Zurum Sauda ta mik'e tsaye, gabanta ya yanke ya fadi, Duk yanda take zaton Alhaji Habib lema, ya wuce tunannin ta, yayi ne ta ko wani fanni, Kwarjinin shi ya cika mata fuska, shima kallonta yake yi da murmushi a kan fuskar shi, lokaci guda ya ji ya kamu da son ta, Sai da ta daidaita natsuwan ta da yaudarariyan murya tace "Welcom sir, i'll tell the Director You are here" cikin sark'ewar Murya Alhaji Habib yace "no i'm here for you" murmushi tayi ta gefen kumatu don ta san tunda ya sha maganin nan dole zai zo neman ta. Tace sit please, ba tare da jin komai ba ya zauna suka dan fara magana, har ya mata maganan aure, ba da bata lokaci ba ta amince mai.

"Sauda ga wannan files din ki shigar da shi cikin documents din-- bata rufe baki ba idon ta ya kai kan mijinta dake zaune yana ta kyalkyale daria shida Secretary. Shima ya dago ya kalleta da murmushi "Shatou nah" tace "Habibi what a suprise, what are u doing here? Yace "gani nan dai, har nayi gamo" tayi daria tace gamo kuma? Da mene? Ba tare da yaji dar ba yace "da matar aure" dammm gaban Mami Aisha ya buga, firgici da tsoro suka baiyana a fuskar ta, ta zaro idanuwa tare da dafe kirji tace "a ina?" yace "a nan, Secretary dinki Sauda" take firgici da tsoron fuskan ta ya koma murmushi tace "ai sauda na da kirki, Allah ya tabbatar da Alheri" Wani shuumin murmushi Sauda ta saki.

Bayan Wata Daya
Abu kamar wasa, Yau ake daura Auren Alhaji Habib Lema da Amaryar sa Sauda Ahmad. Zaid da Matarsa sunzo tun shekaran jiya,Manyan mutane daga wurare daban daban sun hallara, har yau ba wanda ya daga kai ya ce don me Habib zaiyi aure? Ba abun da ya damu kowa da bikin nan, Rafeeq ko har Dinner ya hada ma Baban shi.

Muje zuwa

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg2⃣2⃣

Daria Sosai Hafiz yayi, yace "i know you are stupid, but bansan stupidity dinki ya shahara har haka ba, kina son Habib Lema ya aure ki? A mafarki ko? To bari kiji, ko a mafarkin, Habib Lema ya fi karfin ki, Habib Lema ya miki fintikau, Tsakanin ki da shi nesa nesa" tayi daria ta mik'e tace "Hafiz, Sai na Auri Habib Lema, i am asking u now nicely to help me, u know what i am capable of right? Bani da kyau, kuma dole ayi abu yanda nake so".

Zuciya taci Hafiz ya zo ya makure mata wuya ya buga ta da bango, k'akarin amai ta fara, tace "Feezo, ka sakeni DonAllah, you are hurting me" Yace Saudah " listen to me close, wannan shine warning dina na farko kuma na karshe, Stay away from my family, Habib be miki komai ba, idan akwai wanda ya miki wani abu, to nine, ni zaki hukunta, dont let my Family into this, they didnt do anything wrong, ina rok'on ki Saudah" ya karashe magana yana mai sausata murya, tare da sakinta.

Ta gyara tsayuwar rigarta, tace "nifa ba wani mugun abu nace zanyi ba, Allah ne ya jarabbeni da son shi, kamar yanda ya taba jarabbata da sonka, amma son da na maka, ko rabin wannan be kai ba, ina son Habib Lema, Ina ganin zan rasa raina idan be aure ni ba, so ka kwantar da hankalin ka, Aurena kawai nake so yayi, ba wai ina so na tarwatsa muku Family bane, zaka taimaka min, ko don Diyarka" ta na kai wa nan ta yi hanyar fita, Hafiz ya dinga kiranta amma bata tsaya ba.ta fice.
Har aka kusa tashi office Hafiz be samu sukuni ba, tunanin maganganun su da Sauda yayi tayi, Wai yanzu shi ke da diya? Shegiya? Wacce aka haifa ba ta hanyar aure ba? Ya akayi haka?.

Shekaru 16 da suka wuce (16 Years Back).

Food is Ready Restaurant Sabon Gari Kano.

A lokutta da dama idan Hafiz da Anas sunzo yawon banzan su a Kano, wannan Gidan suke zuwa don cika Cikin su, da rabon kudin da suka ciyo wurin Gambling(ChaCha). Wuri ne 'wanda yan iska da yan tasha ke cin Abinci, Shagon Maman Sauda ne, Sauda da kanwarta Maryam suke serving abinci, idon su bude yake don suna hulda da yan tasha, har Sauda na ba da Jikinta don Kudi, Tun randa Allah ya fara kawo Hafiz Shagon maman Sauda, Sauda ta kamu da son shi bilhakki, ta fada ma mamanta, maman ta tace "ke kinga Saude, wannan yaro akwai kudi jikin shi, ki tatso mana shi kawai, ki bar wani batun soyayyah kinji? Ta turo baki, tace ni gaskia mama son shi nake, har ina so na aure shi, Maman tace "aure? Babban magana" a haka Saudah ta kudurta a ranta ko ta halin k'ak'a sai ta auri Hafiz Lema, don gayen ya hadu ta kowane fanni.

Anas ya Kalli Hafiz yace "Kaga Saudah sai signal take maka ko? DonAllah ka bata chance, kullum muka zo Kano, bata da wani sukuni, sai neman attention dinka, kalleta fa She's not bad, da kyanta, da dirin ta, ta hadu ko ta ina" Hafiz ya buga tsaki yace "na sani mutumin, nifa da zata zo in huta da ita in biyata da na fi kowa jin dadi, amma ita sam wannan be gaban ta, wai aure take so muyi, kai har wani abu take so muyi wai shi Soyayyah" Anas ya tuntsire da daria yace "duk a zatona Sauda ta waye ashe da sauran ta, wake Soyayyah yanzu? Ai kawai mata yan hutu ne, a huta dasu a biyasu kowa ya ware, banda jakkan ci har ta na so ta aure ka" "bar banzar" inji Hafiz.

Karaf kan kunnen Saudah, tazo ta zauna kusa da kujerar Hafiz, tace "Anything for u" mikewa tayi ta ja hannun shi, shi ko sai binta yake, wani daki ta ja shi. Anas ko sai babbake wa yakeyi da daria.
Chapter 18 · 0% Book details