Sashe 69
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Darian takaici Maalesh yayi, yace "yes you are Rafeeq freaking Lema, i know, the guy that cares about nothing, na san kai ko waye, nafi kowa saninka, which is Why nagano exact feelings dinka towards Seebi, Saboda Kai na bar Seebi, saboda kai maganar So bata ta6a hada mu ba ba wai don bana sonta ba, aa sabida na lura kafini sonta, ka fini bukatar ta, Shuttup Maalesh, ka fara hauka ne wai? Me zanyi da wannan yarinyar? Ce maka tayi ina sonta? Ko kuma meye? She means nothing to me, na dauketa a 'yaruwa ta, shes like Rafee'ah to me, nothng more nothing less" Maalesh ya katseshi "Ofcourse, naga alama, ai naga lokacin da wuta ya kama gidansu ka fita daga hayyacinka kake ta sambatu ba wani abu bane wannan ko? Ko da yake ba sai na tsaya gaya maka ba, kai da kanka ka san what you want, like it or not, you are deeply in love With Seebi" Zuciya ta ci Rafeeq ya dunkule hannu ya kai ma Maalesh Naushi a baki, nan take ya fasa mai baki, Maalesh ya taba yaji jini, Murmushi yayi yace" yanzu ka gasgata min Zance na, kana Son Seebi, in ba haka ba mesa zaka damu kanka har haka?why are you affected With what i said? idan ba haka abun yake ba, me zai dameka? Har kana tada jijiyoyin wuya? Har ya kaika ga naushi na, It only means onething, you love Seebi this much" Fuskar Rafeeq yayi ja sosai, zuciya na tunzura shi, Rafeeq ya sake daga hannu zai kai ma Maalesh mari, Maalesh yayi saurin rik'e hannu tare da ture shi iyakar k'arfin shi, Rafeeq ya zube k'asa, ai kuwa ya tashi da zafin nama ya wawuro Maalesh da fada haka suka kama dambe iya karfinsu, suna nushin juna, abunda basu ta6ayi ba kenan Dambe, iyakacinsu gardama da chachan baki, abun be taba kaisu ga fada har haka ba.
***********
"Ai kuwa Asirin ki ya tonu, don k'ona wannan layar zanyi, duk asirin ya kone tare da layar" har mu zaa nuna ma hatsibibanci, mu ba boka ba mallam muke maganin mutum" mitar da Nene take tayi kenan bayan fitowar ta daga garden rik'e da layar zata shiga cikin gida, daidai wani daki taji alamun Hayaniya, kamar fadafada, ta shaida Muryan Rafeeq da na Maalesh, da sauri ta k'arasa dakin ta bude gami da doka uban salati "Lailahaillah, me zan gani haka? Dambe? Kuna cikin ganiyar Samartakan ku kuke dambe? Zaku rabu ko kuwa? Inaaa sam ba su san tana yi ba, dambe fa sosai sukeyi, kowa da tashi kalar Zuciyar, Ta ajiye karikitan hannunta a gefe ta shiga tsakaninsu tana raba su, Maalesh ya dan ja baya amma Rafeeq sai k'ara wawurar Maalesh yakeyi suka cigaba da damben, ba yanda batayi su rabu ba sun k'i, har dai ma Rafeeq ya yi kuskuren hanbarin Nene a gefen fuska, ta ko ji zafi sosai, tace "bala'in nan, daga rabo na samu kasona? Ku ba ku san ku bari ba ko?ta waiga ga Rafeeq tace "Ana baka hakuri kak'i bari ko? Kai me zuciya, har warewa kakeyi don ka saba dambe ko, to kar ku fasa, ku jirani inje in dawo, in kun fasa damben kun ci uwarku duka, ku jira ni nace" ta durkusa ta kwashi tarkacenta ta fita tana tsuma, wurim baba maigadi taje taga baya nan ya tafi masallaci, ta wuce baya inda ta shuka zogale ta hango gatarin da tayi amfani dashi. ta hau cire kayan jikinta tana fadin "har ni za a nuna wa dambe, Allah kasa kar su fasa" sai da Nene ta cire Zani da rigar da ke jikinta ya rage daga ita sai fan guntun Buje(Skirt), ta dauki Gatarim ta cire wurin tsinin(blade) gatarin ya koma kamar tabarya, nan tayi cikin gida tana huci kamar Zakanya.
"Yihuhu ina Dunkum din yake, ba ka fasa ba ko? To gani nan zuwa, yau sai nayi k'ullin k'ullin kubura da kai, yau ko ni ko kai".
A lokacin ba su bar damben ba, cikin ikonAllah Allah ya nuna wa Maalesh Nene ta gefen ido, kallo daya yayi mata ya dauke kai, gabanshi ya fadi, a ranshi ya ke tambayan kanshi anya Nene na da hankali kuwa? Ba da ban dan guntun siketi din dake jikinta ba da yace zindir take, cikin seconds din da be wuce Goma ba Maalesh ya gama tunanin nan, da sauri ya bangaje Rafeeq ya fice a guje, a zaton Rafeeq Maalesh ya ji tsoro ne shiyasa ya gudu, da azama ya bishi don kamo shi, ya ci karo da Nene wanda ta yo dakin gadangadan, ai da gudu ya rufe daki ya shige toilet tare da sa Key, tsakaninshi da Allah be gane ko wacece ba, duk zaton shi gamo yayi, bugu daya Nene ta ma k'ofar dakin Rafeeq ya bude, ta shiga dakin tana dube dube ta na fadin "ina dunkum din yake, ka fito mana, in ba ga tsoro ba, yau ko ni ko kai, yau sai na cire maka duk wani abun da ke kanka" jikin Rafeeq rawa yakeyi, ta hujin makullin toilet yake kallon Nene sosai ya firgita da yanayinta,tsoro ya hanashi gane ko wacece. Addua ya hauyi a zuciyar shi, na Allah ya kawo mai dauki, Allah ya cece shi daga wannan Zararriyar matar" Fitsari yaji na neman kubce mishi sakamakon Bugun da yaji Nene na ma K'ofar toilet din" baki na rawa yace "Lord have Mercy" karaf kunne Nene, ai ko ta tunzura, ta cigaba da bugun k'ofar nan da Gatari tana cewa "Ni kakeyi wa Turanci?" Jikin Rafeeq na kyarma, a hankali ya shiga kiran "Mamiiiii"
(Manage this zan cigaba daga nan😬)
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Cikin Masoyan Biebee Isa harda Tsofi💚 wannan abun ya min dadi.
Ina mik'a gaisuwa ta musamman gareki, Kakar mu Hajia Saje❤ at your age i never thought you'll have time to read This Story of mine, I was so happy and excited when i was told by your granddaughter (Benazir) that you are a Fan of My Story, which is why i'll make you Friends with Nene😉 Thank You Hajia Saje❤, Allah ya Albarkaci Zuri'ar ki, ya k'ara miki lafiya da tsawonci rai da kwana. KE ALHERI CE This Page is for you Grams Hajia Saje❤
Pg5⃣4⃣