Sashe 11
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hafiz ya yanke hukuncin ziyartar Save din da daddare, haka ko akayi, dare nayi wurin 8 ya san Yayan su na gida time din, ya wuce straight Gidan inda Save din yake, da yake an san Hafiz dan Gida ne, kuma ba wanda ya musu shamaki da shiga gidan ya sa mai Gadi ya wangale kofar Gate din, Hafiz ya shiga da motar shi, Staright office din ya wuce, ya bude lockcode (LEMA)din ya shiga hankalinsa kwance.
Wardrobe din ya bude ya ga Save's biyu sai kuma inda aka cire nashi safe din, Irin Save dinshi mai kama da nashi ya jawo, aka sa enter password, Hafiz ya hau chanki-chankan(guessing) passwords, ya sa;Lema, be bude ba, wani tunani yazo mai, ai password din safe dinshi Hafiz Lema ne, kuma Yaya Habib ne yayi setting dinshi, which means toh wannan Save din can either be Zaid Lema or Habib Lema, bari ya fara da Zaid, cikin ikon Allah ya na typing Zaid Lema safe ya bude, wani ihun jin dadi Hafiz ya sake, baiyi wata wata ba ya kaushi kudin son ranshi, ya kulle yayi locking ya maida komai yanda yake ya fita.
Bayan kwana 3 Hafiz ya dawo ya kara diban kudin nan, haka Hafiz ya maida Save din Zaid Bankin kudin shi, da yan bukattunshi ya tashi ko na abokan shi sai yaje Ma'ajiya(Save) din Zaid ya jida na jida, da abun yayi kamari sai dai Hafiz ya dauke Save din ya kai gida, cikin Save dinshi ya juye dukkan dukiyar da muhimmar takarddun daga Save din Zaid. Ya na tunanin ya zaiyi da Empty Save din Zaid? Ina zai wurgar inda ba zaa gani ba?
Rafeeq da Rafee'ah sunyi bulbul da su, kowa na sonsu, maman su na ta zuwa Aiki, da su take tafia tunda tana da mai aiki, Soyayyahr su sai gaba takeyi da Habibinta.
Hold up ne ya tsaida Zaid daidai titin Kofar kaura,kamar ance waiga gefe, Wani yake hangowa kamar Hafiz da wata babbar mata dake gaban mota, daga baya kuma Anas ne zaune, Zaid yayi mamaki, to ko dai Mamar Anas ce? Kai aa, in mamar Anas ce sai dai ta zauna bayan mota ko shi Anas din ya tuk'ata.Gani yayi matar ta sa hannu ta shafi kumatun Hafiz, cikin Zaid ya kada, Haka kurum zuciyar Zaid ya ki aminta da ganin da ya ma su Hafiz, ya bi Bayan su da aka basu hannu.
Be bari sun lura dashi ba, don a hankali yake bin bayan su har suka zo wani Gida da Hafiz ya siya don holewa da yan matanshi ya shiga yayi parking, ganin wani mota a bayan su ya sa Maigadi barin gate din bude don a zaton sa tare suke. Tun da Hafiz yayi parking motar nan suka fara watsewa da wannan matar cikin mota, Anas kuma na kwankwadan Syrup duk sunyi nisa gun aikata Sa6o.
Iya karfin shi ya shiga bubbuga gilashin mota, ji kake kwam kwam!! A firgice suka dago, Hafiz ya tsorata, da sauri ya fito, idanuwan Zaid suka kada sukayi jaa, da karfi yace "Haba Hafiz, me zan gani haka? Dama harkar mata kake yi? Ji wannan matar a haife ta haifeka wlh, amma kaji kunya". Hafiz dai ya kasa magana don kunya ya kama shi kamar kasa ya tsage ya shige ciki, Anas yayi ta maza yace "Ji mana Zaid" Zaid ya galla mai harara ya kalli matar da ke tsaye tana gyara tsayuwar rigar ta yace dallah wuce ki ba wa mutane guri, ko a jikin ta tace "Fizboy my balance" jiki na rawa ya ciro rafar dubu 1 ya bata ta sa a jiki ta mai blowing kiss, Zaid ya bita da harara" ya juya a fusace zai bar wurin, da saurin Hafiz ya rik'e hannunshi, yace "Zaid, i'm terribly sorry, Sharrin shaidan ne, yau na fara, kuma iyaka ta kenan wallahi, Zaid ka yarda dani" Zaid ya kalle shi shek'ek'e yace wannan kuma tsakanin ka da Ubangijin ka, shi zaka roka gafara bani ba" da sauro Hafiz yace" Wallahi na bari, da ma ba halina bane, kai ka sani, don Allah kar ka gayawa Yaya" Zaid ya kalli Hafiz, ya ga hawaye kwance cikin idanuwanshi, ya bashi tausayi matuk'a, yace Allah shi Kyauta ya shige motarshi ya tafi".
Anas yace "Fizboy, Zaid ya ga gurin kwanan ka, yana kaninka amma ji yanda yake gasa maka magana kamar ka kashe wani, mtsww dole ka dauki mataki a kanshi" Hafiz yace "barni da dan shegiyar, zanyi maganin shi nan ba da jimawa ba"..
SATIN DA BAI WUCE BIYU BA.
Hankalin Habib yayi mummunar tashi da ya bude Wardrobe ya ga ba Save daya, ya duba ya ga Save din Zaid ne babu.
Habib ya kwala wa Securities kira cikin rudewa, suka zo a gurgurje, yace "Akwai wani baren da ke shigo gidan nan ne?" Security yace "ai Oga Gidan nan ba me shigar shi daga kai sai kannenka biyu, a rude yace yaushe suka zo last? Yace " Oga Zaid yazo jiya, sai bayan Maghrib ya tafi, Oga Hafiz kuma ya kusa 3weeks rabon shi da nan arean"
Habib ya fita da sauri ya shige motar shi, yayi gidan shi.
Tsaye suke a parlo suna ball shi da Rafeeq, Aisha ta fito dauke da Warmers ta ajiye kan dinning ta kalle su cikin murmushi, tace Uncle Zaid da danshi, wallahi ku ka fasa min Showglass sai kun biya ni, in banda abunku wa ke kwallo cikin parlo? Zaid yace "haba Matas, don dai Showglass? In mun fasa ni da boy dina muna da kudin sayen miki wani ai--" be rufe baki ba Habib ya shigo kamar zai tashi sama. Aishatu ta tsorata, Zaid ya dauke Rafeeq da sauri don kiris ya rage Habib ya ta kashi.
Aishatu ta matso da sauri, Daddyn Rafeeq me ya faru? Lafiya? Yace "ina lafiya shatu? Banga Save din Zaid ba. Kai zaid ka dauki Save din ka ne?" cikin rashin fahimtar abunda Yayan sa ke fadi yace "Yaya meye kuma Save?".
Yaya har sai ka bata bakinka wurin tambayan inda Save din Zaid yake? Ai shi zai dauki abunshi? Idan ba shi ba wa zai dauka? Duk suka maida hankalin su ga Hafiz da yake shigowa parlorn, ya cigaba da cewa " bros, ashe baka gaya mai ka dauko ba?" Zaid baki ya sake galala yana kallon Hafiz, sai yanzu ya gane me suke nufi. Ran Habib in yayi dubu ya gama baci, da karfi yace "Zaidu, Ya za ka min haka? Idan kana da bukkatar Gadonka kamata yayi ka gaya min, ba wai kaje ka dauka kai tsaye ba, haka kurum ka sa hankali na ya tashi?" Zaid cikin rawar murya yace "Yaya, Wallahi ban dauka ba, hasalima ban san inda suke ba" Hafiz yace "Ka fara jokes dinka ko? Jiya jiyan nan kace man kana da bukatar Gadon ka na baka shawara ka sanar da Yaya" Zaid cikin bacin rai yace "Kaji tsoron Allah Hafiz, yaushe mukayi haka da kai? Wallahi ban san inda Save din yake ba Wallahi ban dauka ba" Habib yace "dallah rufe wa mutane baki, mutumin banza mutumin hofi, karya za a maka?, yace "Yaya wallahi-- tasss kakeji, Habib ya tsinke Zaid da Mari, ya shiga dukkan shi ba kaukauta wa, ni za ka tada ma hankali? After all i'm doing for u? Dukkan shi yake ko ta ina, Rafeeq na ta tsala Ihu, Aishatu ma kukan takeyi, da kyaur ta kwace Zaid hannun Habib ta turashi waje tace "Ruga daki Zaid". Habib ya zube kan kujera yana maida numfashi, yau yayi abun da be taba yi ba, bugun kanneshi,.
Ran Aishatu bace, ta daga kai don neman Hafiz, tunani takeyi ina Hafiz yaje da Habib ya ke dukkan Zaid. Tsaye ta ganshi daga gefe, da alamun yana gun a lokacin da Habib ya ke ta jibgar Zaid, In dai idanuwanta ba yaudarar ta suke ba, to murmushi ne kwance kan fuskar Hafiz.
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣5⃣
Tabbas Hafiz, murmushi yake yi don ko da suka hada ido da Aishatu gwalo yayi, a ranta tace me hakan yake nufi? Da kyar ta samu Habib ya sha ruwan sanyi ta tura shi toilet don yin wanka, ta shiga sintiri cikin daki tana tunanin abun da ya faru yau, tabbas akwai ayar tambaya akan lamarin.
Ashe fitar shi, gidan Baba Tijjani yayi, ya gaya mai Karya da gaskia, hikimar yin hakan, kar Zaid ya zo ya fara samun shi ya wargaza mai lissafi shisa yazo ya fara gaya mishi, Cikin mamaki Baba Tijjani yace "kuma shi Zaid din ya ki amsa laifin sa? Hafiz yace "sai rantsuwar karya yake tayi" Ran baba Tj ya baci, yace tashi muje gidan.
Tara su yayi duka a parlor, Zaid a kasa yana hawaye, Hafiz da Aisha kan kujera, Baba TJ yace "Habib Me ya faru?" yanda Habib ke magana zaka san ransa a bace yake, yace "Wai Baba, bayan munyi maganan Joint Ventures din nan, na tafi Warehouse don cire 2m daga Save din Zaid, na cire 5m daga Save dina kamr yanda ka shawarta kawai ina bude wardrobe naga saura Save daya babu daya, hankali na ya tashi a tunani na wasu yan ta'ada ne sukayi gaba da Dukiyar maraya, Ashe shi da kanshi ya dauke kayansa. Ran Baba Tj ya baci yace "kai Zaid meyasa ka dauke Ma'ajiyar ka ba tare da sanin wan ka ba? Zaid ya girgiza kai yace "Baba, banda masaniyyar abunda ya faru, ku yarda dani wallahi"
Habib ya jefe shi da mukullin motar sa. Yace "ni kana bata min rai idan kana rantsuwa a kan karya, tsaya kaji Zaid, ni ba ka ban haushi ba don ka bukaci hakkin ka ba, da ka gaya min kana da bukata da da kaina zanje na dauko na damka maka komai kamar yanda na ma danuwan ka, amma kai kaje ka dauko, ka tada min hankali, yanzu kuma kana ta rantse rantse ka ki amsa wa." Zuciyya ta dau Zaid, yace Yaya shi kenan, na dauki Save dina, ina da bukkatun na shiya sa na dauka, ka yi hakuri idan na tada maka hankali. Yana kaiwa nan ya tashi ya bar musu parlon.