Sashe 9
Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
bude kofan mazaunin driver wani matashi ne zaune cikin motan baki yana sanye dawani dogon wando na linen dark blue sai canvas a kafansa but sport canvas fari, jikinsa yana sanye dawata t-shirt fara kal wuyanta mai zip na channel kansa sanye da p-cap itama fara, idanunsa akwai black shade na channel akai dayama fuskansa da gemun daya tara wani irin bala in kyau, yanada dogon hanci dakuma lebensa that s dark daya kara defining face nasa, wayansa ne yahau ringing hakan yasa yakalli screen din Nabeel aka rubuta hakan yasa ya danna yakai wayan kunne ahankali yace m here! muryansa bala in dadi, yunkurowa yayi yasauko daga motan ya tsaya yana gyara zaman rigansa, yanada tsayi, boot na motan ya bude ya kwaso sandunan buga golf a wani irin jaka mai kyau yabi ya rataya yamaida boot din yarufe yafara tafiya kana ganin tafiyansa kaga footballer, daga shigowansa ko ina ya dauki kamshinsa, direct field yawuce inda wani hadadden guy fari ke wajen already yana playing shikuma yana sanye da farin wando da farin takalmi da hula but yasaka dark blue t-shirt da dark shade a idanunsa yajuyo yakallesa yace re always on time why were you late Imam? Sauke jakan yayi yasa hannu yadauki stick dinsa ya tsaya da kyau yana kallon target dazai buga ball din yana gyara stick din cikin husky voice yace I was with Mami dariya Nabeel yayi yace Dr fa ? buga ball din yayi professionally ko kaine sai abin ya burgeka, Nabeel yahau clapping, Imam yayi murmushi yace wanna challenge me? Nabeel yace yesssss! Daidai Mira na fitowa Bella biye da ita da stick nasu sunyi bala in kyau Ziora na binsu abaya kanta na mata light light sosai kaman paper ita ko stick dinma bata dauka ba, tunda Mira tafito take kallonsa har tana neman tai tripping tafadi tai maza tai controlling kanta suka wuce suka shiga field din, Ziora kawai binsu take jikinta gabaki daya ya saki, balls dinsu ma aikata suka kawo musu Ziora ta karbi ball daya ta rike tana juyawa tana kallo sosai kaman bata taba gani ba, Bella takai hannunta takamata tace muje ki zauna achan and watch us play Ziora make mata kafada tayi ta jefar da kwallon da hannu tana ihu tace m going to play yanda yar siririyan muryanta mai bala in zaki ya cika wajen saida Nabeel da sauran ma aikata suka juyo suka kallo wajensu, Ziora tai wani murmushi daya karamata bala in kyau tace look at my ball over there, I m going to get it kafin Bella ko Mira suyi magana tabi kwallon da gudu tana murmushi tanajin wani irin dadi da farin ciki da annashuwa kaman ba itaba, kunya duk yakama Mira sabida yanda Ziora tayi kaman wata classless girl zataja arainasu a irin wajen nan, tasan yaran waye a bangaren nan kuwa? Dasauri Bella tabita cus bataso anything yasaketa su shiga uku ta shiga kiranta. Ziora Ziora Daukan kwallon tayi saita juyo jin ana kiranta ganin Bella tabiyota da sauri abin yamata wani dadi hakan yasa ta kwashe da dariya kawai tashiga gudu tafada bangaren filin wajen su Nabeel tana gudu sosai tana dariya tana waigen baya, tunda aka fara hayaniya bai dago ya kalli yammatan dayaji suna ihu ba sai yanzu dayake shirin buga ball nasa, yana bugawa zai sami yarinyar dayaga tana tahowa da gudu tana yawo a field din tana kallon bayanta sabida wata na biyota dake sanye da mini skirt, ransa baci yayi yama ma aikatan wajen wani kallo dayasa duk sukace sorry Sir sukayo cikin field din dan tare Ziora that s having the best time for her life, ganin mutane sun taho daga front nata da gudu suma saitaji hakan ya kara faranta mata rai, kawai saita tsaya tahau tsalle tai wani ihu da muryanta mai bala in zaki tace catch me if you can sosai Nabeel kawai yasaki baki yana kallon ikon Allah, Ziora na juye juye da tsalle abinta, Mira da ranta yagama baci saitaga ma ai she can take advantage of the situation yayi noticing nata, kawai saita shigo field nasu tazo dab da Imam tace sorry dan Allah, i think she s on something lemme get her, Ziora tashiga tafiya tana juya ass ko kallo bata ishesu ba, Ziora saida taga duk kowa yazo ana shirin kamata kawai saita duke suprisenly tai wani rarrafe kaman yar yarinya tabi ta tsakiyansu tafito daga rundunan haba Nabeel yafashe da dariya yace wanan kuma wave genz mahaukaciya ce tana wutosu Ziora tamike tsaye tahau gudu tayo wajensu Nabeel duka jama an na biyota daidai security Mommy na shigowa wajen tana ganinsa ta tsaya chak tana kallon security Mommy tana lumshe idanu kafin tabude tajuyo batare datama kalli gabanta ba kawai tasa hannunta ta fizge stick na hannun Imam for the first time yadago fuskansa ya kalleta daidai itakuma ta maida fuskanta kallon security Mommy dake tahowa ta turo baki sosai, faduwa gaban Imam yayi hakanan, wani kallo security Mommy yamata saita kasa motsi yana tahowa fuskansa ba wasa kawai Ziora saita fashe da kuka sosai da duka karfinta tace I don t wanna go back home, tell Mommy I m not coming back, I want to travel to the sky see my flight is there tanuna wani bishiya tana kuka idanun Imam tsaf akanta, anatse security yazo wajen yakalli Imam da Nabeel da ma aikatan saikuma yakalli su Mira da Bella da jikinsu yayi sanyi yace I am so sorry if she spoils anything I will pay for the charges sannan yakalli Ziora dake kuka yace I dont wanna force you Ziora your Mom asked me to bring you back home, quietly follow me makemai kafada tayi tana lumlumshe idanu taki magana, dasauri Mira tace please we will bring her b wani kallo security Mommy yamata dayasa tai shiru, strictly yace what did you give her ? Wani kallo Mira tamai tace what do you mean? Kafin yayi magana kawai Ziora tazauna akasan grass na wajen tafashe da kuka, the whole drama was annoying him hakan yasa yajuya zai wuce kawai yaji an rike mai writs na hannu bala in faduwa gabansa yayi dasauri ya juyo yakalleta tana zaune a kasa tama lumshe idanu tace tell Mommy I m not coming backkkkkk! https://chat.whatsapp.com/KRf3oxehKU4Ez0JQ4kipd3 KAUNA DA SO