← Book details Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 99

Sashe 8

Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

inba dariya ba anga fine yar budurwa tafadi, hannunta takai tana kwashe ice cream na fuskanta ga sanyi tanama kokarin bude idanun takasa yan samarin wajen na cewa iyayen yanga da kafidiri Allah kara, faduwa gaban Ziora yayi sabida step din dataji dake takowa a natse approaching her saita fara yunkurin tashi zaune ma tana share ice cream na fuskanta da hannunta tana goge na hancin, wani kamshi taji ya ratsa hancinta mai wani irin dadi da bata tabajin kalansa a rayuwanta ba da batasan sanda tafara bubbude hanci tana waige waige da fuskanta ba tana neman kamshin ba, wani appealing calm voice na namiji ne ya sauka kan kunnuwanta. Stay still! Hakan yasa ta tsayar da shafe shafen fuskan datakeyi kirjinta na dukan uku uku, wani warm and soft piece of clothe taji a hannunta dasauri takama tarike. Wipe your face with this taji muryan yasake mata magana dasauri Ziora takai abin daya bata fuskanta dataji kamshi sosai shima kaman na jikinsa that means handkerchief ne ta goge fuskan tass tazare tai kokarin bude idanun amman yaji ga danko da sauri tace Daddyyyyyyyy my eyess wlh tama rude ta yarfe hannu sosai cikeda tashin hankali, bottle water taji kan hannunta dasauri tarike taji muryan yace wash your face with this muryanta na rawa sosai kaman wacce ke dab da sakin kuka tace is the bottle open Sir? Dan shiru taji anyi harsaida tace uhmm? Cikin wani husky voice mutumin yace yess dasauri ta karkata goran tadebi ruwa a hannunta duk yama diddiga jikinta ta wanke fuskan daidai security mall din na zuwa wajen. Sorry young lady karasa wanke fuskan tayi tasss sannan tabude idanunta tasss suka budu tabi wajen da kallo security guda biyu ne kawai agabanta saita mike da sauri tana kallon piece of clothes na hannunta taga handkerchief ne nawani soft yard fari mai bala in kyau saidaga tip na handky din bangare daya an rubuta Dr AH dasauri takalli security tace where is the Man that help me? The one that gave me this ? Daya daga cikin security yayi pointing exit door na fita dake nesa dasu yace gashi chan yana fita dasauri ta kalli wajen daidai wani dogon mutum dake sanye dawani sky blue yadi anmai dinki jumper yana fita kansa sanye da hula hannunsa rikeda leda, kafansa na cikin takalmin Hermes na maza, wayanta ta duka ta dauka da bottle water daya bata ta kwasa da gudu tai exit door din, tana ficewa ta tsaya tana kalle kalle ta hangosa parking space gaban wata Mercedes baka, da gudu tai wajen tace Sir, Sir, Sir baima jiyota kokuma yajiyota but baisan dashi akeba takara karfin gudun yana kokarin bude kofan motan tana isowa wajen cikin muryan haki tace juyowa yayi at once tareda dago kansa ya kalleta, wani irin black skin guy ne dakeda tsayi sosai yanada jiki but murdadden full jiki, yanada muscles na bala i ga chest dan rigan kaman ma ta matsesa a kirji tsabagen huge chest nasa, yanada wani irin saje mai bala in kyau da gemu da baida tsawo but a kwance gawasu irin pink lips that looks kaman lips din na ciwo ma tsabagen how pinkish they are, yanada siririn dogon hanci, ko kadan bataga idanunsa ba sabida wani shade ne a idanunsa na rayban baki saidai taga tilin gashin giransa, yanda mutumin yama Ziora kyau wlh wlh mance abinda tazo tafadi tayi daidai ana bude dayan bangaren motan na gaba wata doguwar mace tafito datafi Ziora tsayi da kiba da maturity sosai tana sanye da abaya tayi rolling gyalen itama fara ce kyau yawa ga makeup a fuskanta ga janbaki ta hadarai takalli Ziora dake kallon mutumin tace lafiya kika biyomini miji ? Yatsine fuska Ziora tayi dan bata gane hausan ba tace what? Can you speak English please wani banzan kallo matan tamata tace why are you following my husband wani banzan kallo itama Ziora tamata tace your husband helped me saita kalli mutumin dake tsaye har lokaci da zuciya daya da wannan free spirit nata kawoa ta matso kusa dashi wajen kofan motan tamikamai handky da bottle water da ruwa yarage tace thank you Sir, I m okay now dan yatsine fuska kadan yayi kaman wanda aka roka yayi magana yayi da kyar sounding so mean da english yace trash it! Wlh batama ji meya fada ba sabida yanda yake rowan muryan tsabagen wulakanci but movement na lips nasa yasa tagane meyace kafin tace wani abu ya shige mota abinsa ya kunna itakuma matar mai abayan tai wani dariyan keta tace munsan irinku karuwan mall azuciye Ziora tace say it in english zata sake magana aka danna horn hakan yasa dasauri tashiga motan kafinma ta idasa rufe kofan yawani ja motan da mahaukacin gudu yabar wajen hakanan Ziora taji zuciyanta yamata zafi sosai, ranta yabaci sosai sabida uban gudun datayi ashe baida mutunci dan wulakanci ne sabida yaga yanada kyau, kyan dan maciji, dagashi har matansa marasa mutunci, batasan sanda ta jefar da handky da water bottle din kaman mara hankali anan kasan wajen ba tashiga tattakesu da kafanta kaman dasu take fada saida farin handky yayi baki kirin sannan tawuce fuuuu tai cikin mall din. KAUNA DA SO M SHAKUR EPISODE 6 Komawa shagon tayi har lokacin shopping suke ta zauna kawai duk ranta yabaci batama gayamusu meya faru da ita ba. Sai wajajen 3 suka gama aka musu packing komi da manya manyan jakunkunan su about 7m tabiya da card dinta suka fito sukakai komi mota, Mira tace m hungry lets go for lunch cikin rashin kuzari dan kaman ma ta tafi gida takeji kawai batason suga tamusu wulakanci ne Ziora tace ina zaku cin abinci? Bella tace tulip motan kawai ta kunna taja batako magana sukaje wajen suka shiga sai order abinci suke ita batama da apatite nacin abincin haka aka kawo Bella dake kallonta tace nidai zanga randa zaki dinga cin abinci Ziora juyawa Mira tayi karap taga idanun wani matashin saurayi kan Ziora dake danna wayanta hannunta rike da glass na juice da bata wani shaba, Mira takai hannu ta tabata tace hey Ziora someone is looking at you over there did you know him ? Dago idanunta Ziora tayi karap tayi idanu dawani matashi fari sol dazaiyi mate da Chidi, gawata diamond necklace mai kyau a wuyansa irin wanda all this musician ke sawa dinnan irinsu Davido, he looks like Igbo sef, dauke kai tayi abinta daga kallonsa tacigaba da sipping juice abinta haka suka gama, su Mira sukai take away Bella takira akawo bill, mai kawo bill zai taho farin matashin ya tsaresa, kusan 2min saiga waiter yazo yace that Man wanchan yabiya muku mikewa kawai Ziora tayi tawuce ko kala batace ba dan she s so moody yau dinnan, while su Mira sukai godiya sannan sukabi bayanta, har downstairs ta shiga mota Bella da Mira na shirin shiga motan matashin yadan tsaresu, calmly yace Hi Girls atare sukace Hi, adan hankali ya kalli motan yace please can I get her number murmushi Mira tayi hakama Bella atare sukace sure suka basa number ta suka wuce mota, Mira na duba time tace oh my God muyi sauri he s there already jan motan Ziora tayi har zuwa wani private Golf club, from cars dake parking space din zaka gane dan wane da wane ne awajen nan not wajen yaku bayi, fitowa sukayi suka dauki kayayyakinsu dasukai shopping suka shiga anan reception sukai registration Ziora tace VIP sukeso dan Mira tace crush nata a VIP yake, 5M ta biya su uku sannan aka kaisu changing room nasu su kadai dan chanza kaya, Mira da Bella sun chanza kayansu duka, Ziora riganta kadai ta cire tasa farin shirt data saya ya zauna ajikinta da kyau, tasa p cap fari ta gyara gashinta ya fito ta hujin hulan, tasa farin sneakers din tayi wani irin kyau bana wasa ba, tazauna tana jiransu, batasan mesaba kanta ciwo ciwo yahauyi just like that, ko uban gudun datayi dazu ne oho, dan kishingida tayi a kujera Bella data kasa daurewa tace wai what is it Ziora? Tundazu you ve been so moody Lumshe idanu Ziora tayi, ba shagwaba takeba but yanayin maganan yayi kaman shagwaba tace headache, I m having headache Bella dasauri Mira tajuyo takalleta tace i have something to boost your mood and cure your headache, it s called crack nabaki? Dasauri Bella tace how did you enter wajen nan da crack baki tsoro kike yawo da abubuwan nan? How come those scanning machines basuyi detecting ba Mira? Murmushi tayi tace ke nine fa ta ijiye makeup brush din tadauki yar handbag nata taciro wallet taja wani lungu tacire wani yar paper saiga kwayar magani guda daya rak tamikama Ziora dake kallonsu tace take dasauri Bella tace dalla Mira are you serious about giving her this, you want her to od ne? Bata taba shan something like this ba fa Ziora najin haka ta zabura ta tashi cikeda curiosity tace ya akeji akasha? Bella tace you will feel on top of the world kaman kinfi kowa farin ciki aduniya babu abinda ke damunki ko miki ciwo zaro idanu Ziora tayi tace ohh wow zansha wlh takai hannu ta fizge maganin daga hannun Mira tana kallo, Mira tace idan bata faraba when will she start abeg she s an adult, she s a big girl dasauri Bella tace ni dai baruwana, kinga Mom nata doesn t like us, if anything happens to her baruwana, my father is not rich like them Ziora tace why are you talking like this, forget Mommy she s always grumpy saisa Daddy yamata kishiya aiko suka kwashe da dariya ta sunkuci bottle water tabude zatasha Bella tace please don t take it Ziora Mira tace t mind this one tafi kowa shaye shaye tana hanaki black belly wurga wa bakinta Ziora tayi abinta tasha ruwa, da normal magani ne da sai anyi drama kafin tasha amman dayake kwaya ne tasha ba musu, ijiye bottle water tayi takallesu with so much excitement tace nasha banji komi ba ya akeji? Dariya sukahauyi ta mugun basu dariya, Bella tace zakiji ne yarinya nan bada jimawa ba Around 4:30 wata jeep cherokee ta SUV ta shigo golf club din tai parking wajen,
Chapter 8 · 0% Book details