← Book details Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 99

Sashe 16

Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M SHAKUR
EPISODE 1
Wanka yayi yafito daure da towel, shiryawa yayi cikin wani simple 3quater ash color da white vneck t-shirt sai uban kamshi yake, yafito sanye da slippers yakaraso falon daidai nurse na fitowa daga dakin takallesa tace
she refuse to take her drugs Dr
Imam dake zaune a dinning kallon nurse din yayi jin abinda tace, anatse Haidar yakalli agogon dakin yace
s almost time you can leave, I
m not going anywhere
dasauri Nurse din tace
thank you Dr
tawuce wajen kujera tadauki wani leda ta warware abayanta tasaka tasaba handbag tafice while shikuma yawuce kitchen, da kansa Imam yataso yabiyosa yace
mezaka dafa mana Dr Yaya Aliyu Haidar
? Wani kallo Haidar yamai baiyi magana ba, Imam yayi dariya yazo ya tsaya kusada shi, kadakai kawai Haidar yayi yabude freezer yana ciro chicken Imam ya karba yawuce wajen tap yana wankewa, yaciro frozen peppers yasa a food processor yayi chopping nasu, cikin 40min yahada chicken soup sannan yayi smoothie na apples da cucumber, yabude wani powder magani na magnesium da Calcium yazuba ciki yasa komi a tray yadauka yafice daga kitchen din, Imam kuma yazuba nasa soup din yafito yawuce yayi zamansa a dinning.
Gently yabude kofan dakin Mami da sallama abakinsa yar karama, Mami na kwance kan gado tana ganinsa tadauke kai, maida kofan yayi yarufe yataho dakin yazo wajen gadon ya ijiye abincin a kan carpet yadawo bakin gadon yazauna yayi shiru yana kallonta kafin ahankali yakama kafafunta yadaura kan cinyansa ya matsa calmly da wannan muryan mai bala
in dadi ta lallashin iyaye yace
Hajiya Mami
shiru Mami tamai, ahankali cikeda lallashi yace
I am sorry Hajiya Mami, dan Allah kidena fushi dani
yayi maganan yayi shiru yana kallonta, yakai kusan minti daya ahaka yana kallonta sai Mami tajuyo takallesa sai kawai ta taso ta zauna kusadashi tace
I felt dizzy na sume and so what? A gida ma yanamin haka naga ko, inaso nai kunshi
tanuna hannayenta da akamata kunshi dayayi kyau sosai da kafafu tace
bazan iya fita ba? Aliyu mutuwan nan ko munaso ko bamu so saitazo then why should I restrict my self from living? Ka barni lemme make the few days I have left memorable, sanda ciwon zata kankama ma ko ance naje nan da chan bazan iyaba eh
dan shiru tayi sabida yanda taga yana kallonta idanunsa sun kada sunyi jaaa, saikuma taji zuciyanta yamata rauni, ya mugun bata tausayi, danma namiji ne, is not easy kaga mahaifiyarka right in front of you kuma kasan bazata dade a duniya ba, yanda yaga jikinta yayi sanyi tama daina fadan sai yaji komi ya tsaya masa, ataushashe yace
me da me kikeso Hajiya Mami?
Yanda kirjinta yamata sanyi na rashin kuzari yasa tama kasa magana, matsa kafanta yayi yayi murmushi yace
tell me
kallonsa tayi tai murmushi tace
inaso nadan dinga fita koda bazanyi nisa ba, kaman zuwa su chefane, da sauransu inaso nadinga zuwa
gyadamata kai yayi yace
okay zan dinga kaiki
dasauri tace
aikin ka fa
? Ahankali yace
my work can wait anytime kike bukatan wani abu Hajiya Mami, yanzu sauko kici abinci
abincin ta kalla saita kallesa tace
nagaji da cin irin wayan nan abinci Haidar, kubani dambu, fate, burabusko, farfesu, da abubuwa masu zaki sunake so
shiru yayi duk yana kallonta saiya gyadamata kai yace
okay let
s finish eating this i will get pen ki lissafa ko me kikeso i will get them tommorow, you haven
t eaten anything, come Hajiya Mami
yayi maganan yana kamata batai musu ba ta sauko carpet din ta zauna daidai ana bude kofan Imam ne yaci gayu yace
bari naje gida
Mami tace
ka gaidamin da Maman Samha
murmushi yayi yace
okay makesure kin cinye tasss, idan kinason wani abu call me zan taho miki dashi anjima
gyadamai kai tayi tace
banda gudu a mota
karban smoothie tayi tanasha, ahankali Haidar yace
what happened today Mami?
Dan kallonsa tayi kafin tabasa labarin from beginning to the end tace
nadade banga yarinya mai shigarai kaman itaba, she
s very very caring Aliyu
baice komi yadinga bata abincin tanaci she ate small yabata magungunan ta tasha na dare dan magrib yayi sannan yakamata yakaita bayi tai alwala yafito yasata a dadduma yabata hijabi lokacin an tada salla a masallaci bayinta yakoma yayi alwala sannan yafito yaje sama yasa jallabiya yana zuba kamshi yafito yawuce mosque.
Saida akai isha
i yadawo yashigo gidan, dakin Mami yabude itama mikewanta dagakan sallaya kenan tamasa murmushi tace
bari na watsa ruwa
gyadamata kai yayi tabude bayi ahankali ta shiga shikuma yawuce wardrobe nata very comfortable abubuwa suke saya mata, rigan bacci yaciro mata doguwa har kasa pink mai bala
in taushi ya ijiye akan gado, skin dinta use to become so flecky so sheerbutter take shafawa ya ijiyemata dawani simple body spray dawasu safuna dawani man zafi saiya wuce yazauna kan wani kujera dake gaban study desk dake dakin yana facing bango, fitowa Mami tayi daure da towel idanunta akansa saita dauke tazo bakin gadon ta zauna tai amfani da karamin towel ta goge jikinta tadauki man ta shafa tadauki rigan tasaka ta zare towel ta ijiye gefenta sannan tazauna tadanyi gyaran murya, juyowa yayi yataso towel din yafara dauka ya maida bayi saiya dawo yaduka agabanta kafanta yadauka yasaka kan cinyarsa ya shafaman da kyau kafin yashafa man zafi yasa mata safa duk Mami na kallonsa, yasake daukan dayan kafan yamata haka saiya gutsuro kadan yazo ya shafa a lips dinta sai kallonsa take Haidar baida magana, baida hayaniya, amman yanada zurfin ciki sosai, banbancinsa da Imam kenan shi yanada magana da yanzu yacika dakin da hayaniya. Maida kayan shafa yayi yadawo ya gyara pillows din ya kwantar da ita yaja bargo ya rufamata yana rage remote na AC while Mami tahada hannu tana yan addu
a zama yayi abakin gadon yana kallonta, ahankali Mami takai hannunta takama nasa, kallonta yayi hakan yasa calmly Mami tace
taho
jawosa tayi sai kawai tadaura kansa saman cikinta zai tashi dasauri tace
m fine ba abinda kemin ciwo ka kwanta Aliyu
ijiyan zuciya ya sauke ya kwantar da kansa cikin nata, anatse Mami ta shafa kansa tai shiru kaman mai tunani kafin chan tace
ve dedicated your whole life to me, baka fita da frinds, baka zuwa shakatawa na samari irinka, baka zuwa buga su kwallo ko golf kaman su Imamu, you don
t do anything for yourself sai ni, amman natashi natasaka agaba da fitina, inata masifa kaman bana ganin abubuwan dakake tauye kanka akaina ko, I
m so inconsiderate
zaiyi magana tace
shiii I don
t want you to talk
shiru yayi saitadan jinkirto ta yanda zataga kansa da kyau akan cikinta shima yana ahaka ya kalleta all she sees is dan yaronta data haifa 35yrs ago, lumshe idanu tayi tabude cikin wani sanyin murya tace
I don
t think without you I would have survived all this years Aliyu, seeing how you
ve worked so hard everyday for me wants me to live more for you, banso natafi na barka, thank you Aliyu, Allah maka albarka
maida idanunsa yayi ya lumshe da sauri he hates when Mami tafara irin maganganun nan, har gwara ma tanamai masifa da fada ma da wannan emotional abubuwan, yayi shiru kawai ahaka, baitaba nunama Mami weakness nasaba bazatasa yakuma fara yauba, seeing him weak will be wat will kill her first kafinma ciwon, dago kansa kawai yayi yana bude idanuwansa yakama hannunta yakai bakinsa yayi kissing yace
enough of the talk, you had a busy day yau, now sleep
ijiyan zuciya ta sauke saitai murmushi ganin karfin halinsa da jarumtarsa cikin yar kankanuwan murya tace
gobe zakaga Amrah don
t be rude like your brother Maheer kaji
? Gyadamata kai kawai yayi saitai murmushi ta kwanta yasake gyaramata rufa ta lumshe idanu nan da nan bacci ya kwasheta yadade zaune awajen yana kallonta, juyawa tayi cikin bacci hulanta ya salube babu gashi akanta sai wasu yan kwarorin gashi farare Chemo ya cinye gashin tass, yadade yana kallonta ahaka kafin yatashi ya gyaramata hulan yasa mata da kyau, yaja drawer gefen gadon yaciro stethoscope yamakala a kunnenta yakai ya daura a kirjinta yayi shiru sannan ya cire ya ijiye yamata addu
a da kansa saiya mike yajuya yafita daga dakin yarufe kofan ahankali without making a sound ya kalli agogon bango is 9:30 tunda har yakai war haka bai dawo ba bazai kwana nan ba yau, kofa yawuce ya rufe dudda sunada ma
aikata he don
t trust aikinsu, immune system na mamansa is low, baison anything dazai sa tadauki wasu germs ko bacteria hakan yasa kawai yashiga kara gyara falon da dinning dan nanne wajen zamanta da gadonta na mara lafiya, yayi mopping ko ina ya goge ko
ina da duk inda hannunta zai iya tabawa da abubuwan dake kashe germs har tv kana ganin yanda yake aiki kasan yanada zafin jini, wuraren 10:30 yagama yatafi sama dakinsa yashiga direct yafada bayi sai wanka.
Yafito daure da towel yana tafiya abubbude zai wuce wajen wardrobe yaji wayansa na kara juyowa yayi yakalli wayan saiya bude wardrobe nasa yadauki kayan dazai saka yadawo yazo yazauna abakin gadon yakalli screen na wayan Dr B aka rubuta a screen din, saida wayan ya katse yayi dialing number yakai kunnensa ringing daya aka daga muryan mace ne daga bangaren cikin more like fada da masifa tace
how many miss calls kaga na maka Haidar?
Shiru yayi baice komiba sabida yanda tamai maganan da fada, kaman tagane meyake nufi tadan sassauta murya tace
how many miss calls kaga namaka fisabilillahi? I
ve called you more than 30times, you left the hospital without letting me know, inata kiranka tun kafin magrib har zuwa yanzu baka dagawa and ina tambayanka kamin banza wani irin miskilanci ne wannan
KAUNA DA SO
Chapter 16 · 0% Book details