← Book details Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 99

Sashe 48

Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tun rannan dana fara ganinta agidan nan, ni karan kaina bansan dalilin dayasa ban natsu da ita ba, kawai ban hangota as mace tagari dazaka samu natsuwa, kwanciyan hankali and support dagata wajenta ba, nasan aure hadi ne na Allah, na kalli Beeba duka duka kanku kusan daya da shekara nawa ka girmeta Aliyu zaka iya tankwarata, zaka iya bi da ita? Zaka iya cemata yi ta yi bari na bari? Mami tadan sauke ijiyan zuciya tace All of those things aside Aliyu I m a sick woman da batada kowa, I m an orphan I want you to marry a wife da will see me as her mother nima zan ganta as my daughter, koda yaushe muna tare sabida hankalinka kaima ya kwanta kayi aiki da kyau knowing ka barni tareda wata, ba wannan dakake zuwa aiki goman safiya kadawo 4 na yamma ba no Aliyu, naga Beeba na zauna da ita na rannan I don t hate her but bana sonta a matsayin matarka kwata kwata Aliyu yayi shiru yana kallon Mami, ahankali Mami tace I want someone else to become your wife gabansa kawai faduwa yake bana wasaba, ahankali Mami tace Aliyu ina kaunar Amrah! Dasauri Aliyu yakalli Mami gabansa na bugawa, what is Mami saying all of a sudden? Cikin wata sassanyar murya mai rauni cus maganganun daga zuciyanta suke Mami tace Inason Amrah Aliyu! Yarinyar na matukar kaunata itama! Rabon dana sami soyayyan yaro a rayuwana tun wacce na samu daga gareka kana yaro sai yanzu da Amrah nahadu da ita tazo take sona, I ve never ever seen a girl of her age that s so precious, kind, innocent and sweet ba, banda haka inaso dani dakai mu taka rawan gani a rayuwan yarinyar, she lacks so many things in terms of musulunci, duba daga kalan gidan gidan data fito, plus abinda tafada mani rannan kan mahaifiyarta na son ta auri dandan Pastor Aliyu Mami tai shiru ta lumshe idanu tabude su cikin husky voice tace Aliyu bugawa kirjin Aliyu yashigayi, ahankali yace am Mami anutse tace nasan kariga kasan request din danake shirin yi but I will still say it tadan dakata kafin ahankali tace inaso ka auri Amrah Aliyu! Dawani irin sauri Aliyu yatashi daga zaunen dayake yana kallon Mami yadan hade fuska, Mami tadago kanta ga kallesa tace kayi jahadi akanta let s make her a better muslima, she s a good obidient girl da bata dauki duniya as anything ba, tanada free zuciya, zaka iya tankwarata duk yanda kazo, ka tafiyar da ita duk yanda kaso, seeing the two of you together will make me very very happy, I choose Amrah for you ita nakeso amman banace dole saikayi bane kona tursasa maka ba wlh wlh duk wacce kace zaka aura zan karbe ta da zuciya daya, kaizaka zauna da matarka not me Aliyu, I know one day zakaso Amrah sama da yanda kake tunani, kuma shi a aure babu yaro, so karka mata kallon she s too small for you, koka mata kallon ita kabilace ko wani abu don t think of anything just make up your mind zaka aureta and watch God pave way for u, da musulmi da christa, da bayarabe da bahaushe da inyamuri, bafulatani duk Allah ya halitto mu, being bahaushe doesn t mean kai Allah yafiso, being bahaushe baya nufin kaine musulmin kwarai inyamuri musulum musulum ne, dukanmu dayane awajen Allah sai wanda yafimu tsoron Allah, Amrah nada christan uwa that s not her fault or something daya kamata mu kyamaceta akai, kasan ko watarana d same way mahaifijta ya musulunta itama mahaifiyar ta mutdulanta? Allah Al Gafuraru Raheem so I want Amarh for you and I choose her for you idan har you re ready ka sanar da mahaifinka ka nemi aurenta, but ni ban yarda ka aure Habiba ba at all tunda Mami ke maganan kansa ke kasa gabansa bugawa kawai yake baimasan takamaiman meyakeji ba, but yasan babu abinda bazaima Mami ba, he loves yanda samin yarinyar keeps making her happy and he loves yanda yarinyar makes her happy, babu abinda bazai iyama Maminsa ba, but this request! Daman a tsaye yake kawai yajuya cus bazai iya kallon idanun Mami yacemata no ba yayi wajen kofa dasauri yakai hannu zai daura kan kofan cikin irin muryan nan da iyaye ke using su kama yaransu tace Aliyu I have less than 2months fa idan kana calculation! Chak Aliyu ya tsaya yakasa bude kofan yafita, Mami tayi murmushi tace I am just a dying mother making one last final request dazaiyi making dina nai farin ciki Tasake murmushi saitakai hannu ta yaye hijabin jikinta tacire ta ijiye a gefenta takai hannayenta tazare hulan dake kanta ta ijiye shima a gefe takalli Aliyu dake facing kofa ahankali, gabaki daya kanta ba gashi sai wasu yan kwararru dazaka iya kirgawa suma farare dasu, muryanta yayi sanyi karara tace juyo ka kalleni Aliyu juyowa Aliyu yayi ahankali yakalli Mami hannu tadaura akan yan suman tazare suna fitowa kaman ana cire tsakuwa ba wahala tayi murmushi sosai tace you see nothing is left again Aliyu I am dying nan da wata daya da yan kai kaman maganan yatabata sai kawai tafashe dawani irin kuka dagudu Aliyu yazo sai kawai yaduka agabanta yasa guiwowinsa akasa yace Mami dan girman Allah stop crying cikin wani irin kuka tace Aliyu na azabtu da ciwon nan tun kana dan shekara sha takwas, nine barin jini, zafin al ada, ciwo zazzabi, mahaifinka yarabu dani, banda kowa banda kai aduniya, Aliyu kanada kannai Samha da Farha basa sona, finally Allah yahadani da yarinya danakeso, yarinya dake mugun son mahaifiyarka, bata kyamaceni ba, batamin kallon mara lafiya ba, with all this tanuna saikon kanta tace Amrah will still hug and kiss me, all I want is to see you marry this girl dake kaunar mahaifiyarka na ganku tare amatsayin mata da miji kona rana dayane kafin na mutu Aliyu bazaka iyamin ba? Banason Beeba, bana kaunarta ni Amrah nakeso dakai, amman bakason wacce nakeso kai Aliyu yaga tashin hankali ganin yanda Mami ke kuka ba kakkautawa, cikin tashin hankali yace Mami na yarda stop crying please, I will marry her dasauri Mami dake kuka ta kallesa, hannunsa yakai ya share mata fuska asanyaye yace idan zan miki abinda kikeso zaki yarda kimin abinda nakeso nima Mami? Ahankali Mami na jan majina tace me kakeso Aliyu na ? Anatse yace my biggest fear is loosing you, akwai wani trail danakeso kiyi daga wajen Yayan Amrah Chidi abun yazo, I know kince bakison wani trail again, kin riga kin fawwalama Allah komi, but inhar kin yarda and try this trail I will marry Amrah Mami Wallahil Azim! Mami tadade tana kallonsa sai kawai yaga tamai murmushi tace thank you Aliyu naji zanyi trail din Allah yasa inada rabo, tunda nahadu da Amrah nakeson Allah ya aramin tsawon rai koda jikana guda ne nagani, Allah yasa musami sa a this time ahankali yace Ameen Mami hannu Mami tabudemai tace I am very happy come here akunyace ya sunnar dakai tace da Amrah ce da tuni ta rungumeni murya ciki ciki yace that girl batasan menene kunya ba yabude kofa yafice Mami ta tabe baki tace irinta nakeso kasamu a mata dan jakar butan uba, ja iri kawai EPISODE 4 Wucewa Aliyu yayi yahaura sama, dakinsa yashiga yazauna gaban gadonsa yayi shiru yana tunani, yanzu yazaiyi da Beeba? He literally raped this girl unknowingly and unintentionally wallahi, the least she deserves from him is ya aureta tunda shi ya batamata rayuwa, shiya keta mata haddi, mahaifiyarsa yanzu tace bata sonta batason aurensa da ita, and in this his life Mahaifiyarsa na gaba da kowa da komi wlh, Mami ta isa tasakasa yayi komi yayi, ta isa tahanasa karyayi komi kuma bazaiba, how is he even gonna apologize and talk to Beeba, tayaya zai gaya mata gashi gashi, this news will be so devastating cus if there s one thing daya sani is yanda Beeba ke sonsa, tayaya zai lallasheta yabata hakuri? Yace mata ne to name anything she wants yamata as compensation ko yaya zaiyi? He can never hurt Mami tunda ta hanasa yahanu ne kawai, yanason yarabu da mahaifiyarsa lafiya cikin soyayya da aminci. Yadan sauke ijiyan zuciya Amrah na zuwamai arai murya chan kasa yace this crazy girl da Mami tahadani da ita yayi shiru yana tunani how is he even going to start rayuwan aure da yar yarinyar nan wacce inda yayi aure since he s sure daya haifeta, this girl har yanzu bata gama sanin inda ke mata ciwo ba, ga bakin surutu, ga rawan kai, ga shirme, why is Ammi taking him from frying pan to fire cus left to him daya auri yarinyar nan Amrah gwara ya auri babban mace dan baison wahala, baison kayan takaici, dan gajeren wahalallen tsaki yayi sai kawai yatashi yadauki wayansa albashi yaturama Chef da Nurse yace su dakata da aiki for now till further notice zai kirasu. Daga yanzu zai dingama Mami komi for now kafin ya nemo new workers and he won t let this thing slide zai nemo kowaye behind it, yadade ahaka yatashi yatafi dakin Mami hartai bacci yayi shimfida ya kwanta yayi shiru yana tunani, Amrah yafara gani a idanunsa hakan yasa ya kori tunanin yana juya but yakasa daina ganinta, da kyar bacci yayi nasaran daukansa. Wuraren 5:30AM na safiya Ziora ke bude idanunta tun baccin datayi na jiya da yamma sai yanzu take farkawa, babu kowa a dakin sai Mommy datagani kan gadon tai hugging nata, lamo tayi ajikin Mommy Aliyu na zuwa mata zuciya, ita kanta abinda takeji is so new for her da batasan yazatayi da kanta ba, kawai she want him close to her, close sosai kaman irin na rannan nan da daddare data kwana gidan Mami, she just wanna hear yamata magana so calmly da yar karaman murya irin yanda yamata rannan da aka dauke wuta kaman yana magana da little Baby, bata tabajin dadin wani yamata magana kaman yanda taji dadi sanda Aliyu ke mata magana rannan ba. Ahankali tazame daga jikin Mommy tasauka daga gadon ahankali jikinta gabaki daya feels kaman ba nata ba batada karfi, ko ina ajikinta ciwo yake mata, tafiya tashiga
Chapter 48 · 0% Book details