Sashe 27
Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana tuna rashin mutuncin data mata rannan a mall suna tare da Ya Aliyu, Mami tace wlh babu aikin komi agidan nan, bakinga Chef ba yanzu haka nasan ta daura ma abincin rana, yi kari abinki, idanma kinason wani abu kisa amiki Mami tayi maganan tana kallon Ziora datai lamo ajikinta kaman yar yarinya tace Amreery anyi breakfast kuwa ? Abincin plate na Beeba ta nuna tace Mami I want to eat that thing, my step mom use to make it for my Dady, I use to eat it with my Dady at home murmushi Mami tayi tace muje nasamiki dakaina dasauri tamike tacire takalminta takama hannun Mami tabita suka shiga kitchen Beeba tabita da kallo kanta ya gama kullewa, nurse din Mami itama tana kitchen tunda akai baki ta shiga wajen dan sun soma xama kawaye ma da Chef din Mami. Bugawa kirjin Beeba yasoma yi, tashiga bin ko ina da kallo a dakin taga drip na Mami dake cikin cart na drugs nata dakenan falo meaning duk randa taji zazzabi su drips dinne za a dauko amakala mata, all she needs is ta matsa wajen and just inject alluran in drip din before anybody gets out, the moment akama Mami fixing the drip sunanta gawa acikin likafani yanda zuciyanta ke bugawa zaka dauka fada ake awajen, ta kalli kitchen sannan tabi falon duka da kallo tana kallon sama babu CCTV camera, mikewa tayi rike da handbag dinta da syringe nata ke ciki tayi wajen cart na magungunan Mami, tai maza ta duka tana zaro syringe na alluran daga jakanta, tadauki drip guda tana waige waige tana juyo hayaniyansu a kitchen sama sama, jikinta rawa kawai yake tahau kiciniyan soka alluran ta saman bakin drip din EPISODE 2 Dawani irin sauri Beeba ta juye daidai ana bude kofan kitchen din, Ziora tafara fitowa rike da plate mai kyau a hannunta dake dauke da waina biyu da miya da nama dayawa, Mami biyeda ita abaya, awani irin rude Beeba tajaye syringe din ta wurga jakanta tana kakkallon drip tana juyawa, Mami ta tsareta da idanu hakama Ziora dudda bawai ta santa bane though ai kaman matan wannan mutumin ne ko, but hakan baisa tai mamakin ganinta wajen magungunan Mami ba, dan murmushi Beeba tayi tajuyo tana kallon Mami kafin ta duka ta maida drip din ta ijiye da kyau ta yanda bazai zuba ba tace Mami inadan dube duben medication dinki ne Tadawo ta zauna tana ijiye jakanta a gefenta while Mami tasa hannu tajama Ziora kujera dake rikeda plate tace maza sit here kici abinci Amrah zama tayi tana ijiye plate din agabanta har lokacin babu mayafi akanta, tadauki spoon zataci dashi Mami tace ba mun wanke hannu a kitchen ba ci da hannu gutsuran masan tayi dan karami takai baki tanaci takalli Mami dasauri tace Mami is yummy Mami tace eh amman banji kinyi Bismilalah kafin kifara cin abincin ba dasauri tace bismillah abu Beeba taji azuciyanta Mami is just after this arniyan, ga sirikanta tazo amman hankalinta nakan wannan, daukan tray tayi tafara cin nata ahankali, daya Ziora taci taji she s okay zata tashi Mami tace ina zaki? Murya chan kasa tace Mami I m okayyyy dan hararanta Mami tayi tace bani plate dinnan zauna kiga Mami ta karbi plate din tasa wankanken hannunta ta gutsuro masan tasa miyan tace haaa budemin bakin, yarinya batacin abinci saisa kaman ahureki kifadi, open your mouth bakinta Ziora tabude ahankali Mami tasamata abincin aciki wani dadi taji batasan sanda tai smiling ba saitaji abincin yafi dadi a hannun Mami, Mami takara gutsuro na biyu tace oya open your mouth bude bakinta tayi daidai ana bude kofan dakin Aliyu ya shigo da sallama ciki ciki Mami na sama Ziora abinci abaki, kallo daya yama wajen yadauke kai dasauri Mami dake ba Ziora abinci abinta tace kadawo Dr Aliyu? Gyadamata kai yayi yace Beeba tai murmushi sosai tana kallonsa yashigo falon yasami waje yazauna yadaura kafa daya kan daya yana taba wayansa Beeba sai kallonsa take hakanan she s feeling kaman yakosa ta tafi kuma ita bazata bar gidan nan yanzu ba. Mami tace good girl saura nama girgizama Mami kai tayi tace Mami I m okay ai anci nama see my stomach is too full now Mami tace naji muje, ki wanke hannu you will explain to me why you don t like school kullum gudowa kike ashagwabe ta gyadama Mami kai sukaje kitchen, hannu ta wanke Mami ma ta wanke suka fito Mami ta kalli Beeba dakecin nata masan ga Aliyu zaune a gefe daya yahade fuska tace bari na shiga ciki nadan kwanta dasauri Beeba tace toh Mami na, ina nan ai ba yanzu zan tafi ba ta wutsiyan idanu Mami taga Aliyu ya kalleta almaun baison zaman tai murmushi tace toh ba matsala you can join us kema kika gama gyadama Mami kai tayi Mamita juya ta kalli Ziora tace s go kama hannun Mami Ziora tayi suka shiga dakinta. Zama Mami tayi akan gado Ziora ma dasauri tazauna kan gadon tace Mami kanta Mami tashafa cikeda so tace as a Muslim bakisan babu kyau mace na yawo tsiraicinta na nunawa ba? Annabi Muhammad SAW yace ita mace ko ina a jikinta al aura ne illa wajhaha wa kaffaiha fuska da tafukan hannu sune ba al aura ba, I understand you, I know these are your kind of clothes, but riga haka kaman rigan yar tsana is meant for staying indoors bakifita dashi ba, sannan ba mayafi, ga gashinki ana gani, idan na kaiki na siyamiki kaya za a miki fada a gida ko? Gyadama Mami kai tayi ahankali alamun eh tace yes Mommy will collect them, these are the type of clothes I have, sai Daddy use to buy me abaya but is not the type I see on Hausa girls body a school namu, my own abaya is different, My step Mom use to buy me normal Hausa abayas, atampa and lace but Mommy collect all of them she understands the girl sosai hakan yasa Mami tace okay what about school? Mesa baki zama a school eh? Kinaso nai fada dake ? Girgixama Mami kai tayi ahankali tace I don t like the school, I want Daddy to take me to US, I want to school there cikeda hikima Mami tace to bakisan saikin nunamai zaki natsu kiyi karatu yaga kinada good result anan sannan zai kaiki US dinba, kidinga zuwa school kinji gyadama Mami kai tayi tace but Mami I m afraid of su Mira, I don t want her to beat me, she almost beat me that day is Yaya Imam that saved me Mami tai shiru tana kallonta nan da nan tashiga ba Mami labarin rannan, from yanayin Ziora kasan batajin magana but irin yaran nanne da rashin jinma bawai iyasa sukayi ba koya sukayi a wajen wasu kuma bata iya fada ba, and yarinyar na tsoron yaran especially Mira, anatse Mami tace kije makaranta abinki amman ba ruwanki dasu karma ki shiga harkansu duk randa she mistakenly touch you saina aika Imam yacimata mutunci and you will tell your Dad sabida ayi reportikg nata to school authority but karki karajin tsofonta she can t do you anything okay KAUNA DA SO M SHAKUR EPISODE 2 Gyadama Mami kai tayi, Mami tace s read Qur an then saimuyi magana kan yanda akeyin salla da kyau, anatse kuma cus gaida Allah yana bukatan ka natsu akuma tsanake sake gyadama Mami kai tayi, Mami tadauki Qur ani tabata tace budemin suran da kike da Malamin ki dasauri Ziora takarba tabude Juma a taba Mami tace this Surah Mami calmly Mami tace Masha Allah Suratul Juma a, karanta naji karban Al Qur anin Ziora tayi back to her hand, ta tashi zaune ta gyara zama da sauri, da zuciya daya tafara karatu kuma with all her voice, bawai she s shouting bane or screaming but tasaki duka muryanta and she s so audible exactly yanda take karanta ma Ustaz nata idan yazo gida. Tunda suka shiga daki Aliyu na zaune inda yake a falon baice kalaba, while Beeba nacin masa abinta kadan kadan just to pin down awajen, tadauki ruwa a glass cup tanasha kaman daga sama duk sukaji muryan Ziora daga dakin Mami, batada wani special kira a at all but her voice is more of English sef, sannan kanajin karatun kasan yar koyoce. Auzubilllahi mina shedani rajimmmm tawanija mmmm din yafi akirga, Mami sai kallonta take yanda take karatun her face da kanta duka suna moving like kaman all this yan yaran aji dayan islamiyya dinnan, but she s so damn precious and cute, tace Bismillahi Rahmani Raheeeeemmmmmm saitakara bude murya and she s so confident tace Yusabbihu lilaahi maaaaaaaaa tawani ja maaaa din ba iyaka Mami na kallonta, tace maaaaa fis samaawaati wa maa fil ardil Malikil Quddoosil Azeezil Hakeemmmmmmmmmmm Beeba dake falo tana shan ruwa dariya ne yakamata da batasan sanda ta kware sosai ba, Aliyu ya kalleta fuskansa a hade. Ziora tacigaba. Huwal lazeeeeeeeeeeeeee takara ja kaman ba gobe tana bude hanci cus da gaskiya and with all her will take karatun baiwar Allah, tace asa fimmmmm instead of asa fil tace ummiynaaaa instead of ummiyyeena Rasoolam min hum yatloooooooooo takaraja saitawani sauke ijiyan zuciya danta gaji, Beeba ta daura hannu akan bakinta dariya ba kakkautawa tana tare bakinta sabida kar Mami taji, Ziora tace yatlooooooo alaihim aayaatihee wa yuzakkeehim wa yu .yullll .yul takasa fadi sai fama take tanasa yatsanta akan Qur anin tanabi, ahankali Mami tace allimuhumul Kitaaba wal Hikmata wa in kaanoo min qablu lafee dalaalim mubeen dasauri Ziora tace mubeeeeeen tanabin Mami tana murmushi sosai. For the first time Aliyu tunda tazo gidan yamata magana ganin kalan dariyan datake tana taushe baki yace and what s the laugh for? Tana dariya tana pointing dakin Mami tace wace kalan dakikiyace yarinyar nan Dr? Hakanan Aliyu baisan mesa ba but har ransa yaji kalman dakikiyan yamai badadi ko kadan, ya tsareta da idanu kawai baya kyaftawa, Beeba tace I mean common little Idris na gidanmu 4yrs old can read Qur ani much more than this girl, yarinya sai kace a jahiliya perio stand up and leave! Aliyu yafadi da kakkausan murya dayasa takallesa da gudu danta kara gasgatar