← Book details Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 99

Sashe 55

Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami gaba yayi Mami tabiyosa abaya da Nurse dinta itada Nurse suka shiga baya while Aliyu yashiga gaba yajasu sabida Mami na baya ahankali Aliyu ke tafiya da motan Mami is extremely happy today sai tunanin Ziora take dasauri ta kallo nurse tace laaaa kiga na mance da wayana agida kuma nasan abu mai wuya ne Amrah na bazata kirani ba Nurse tace ai zamata kira Aliyu sarai yana jinsu yayi kaman baijiba har sukakai asibitin su Chidi yayi parking suka sauko suka shiga har sama office din Dr Chidi Aliyu yayi knocking Chidi da kansa yafito yazo yace Mom welcome Ma yayi maganan yana bama Aliyu hannu suka gaisa duk suka shiga ciki suka zazzauna Chidi yabude fridge yabasu ruwa Mami tace ahh lallai har ruwa ake badawa kowa yayi dariya kafin ma afara magana Mami tace Muhammad nasan koda Aliyu zaimin rufa rufa kai bazakamin ba saisa nataho da nurse dina sabida takaramin bayani da kyau da kyau cus inada tambayoyi danakeso ka amsamin cutan nan nice mai ita ajiki ba wata ba murmushi Chidi yayi yace what are your question Mom ? Ahankali Mami tace ka gayamin gaskiya wannan maganin ko treatment nema zance dazaku daurani akai zai daukeni kwanaki naw? Sati nawa ko wata nawa kafin agama nasami lafiya kona gangara cus Allah ne mai kowa da komi? Kallonta Aliyu yayi Mami taki kallonsa, Chidi zai kalli Aliyu Mami tace ni zaka kalla Muhammad ba Aliyu ba trust me I am stronger than him murmushi Muhammad yayi yace gaskiya Mami I can t for sure say ga kwanakin da treatment din zai dauka, depend on yanda jikinki ya karbi abin depend on immune system naki, zai iya daukan weeks, months, days or even year komi na hannun Allah Mami ta jinjina kai tace okay tambaya ta tabiyu nafara karban treatment din ya zan dingaji ajikina, nayi trails da dama tun a UK wasu azaban da wahalan danake sha yamafi na ciwo na tell me wat should I expect? Ijiyan zuciya Chidi yasauke yace akwai zazzabi that s fever, rashin karfi da kuzari, amai ko gudawa, rashin apatite, jiri da sauransu, it can go as far as kizo ki kasa komi ba da kanki saidai adinga miki Mami tai shiru kaman mai lissafi saita kalli Aliyu tace Aliyu inaso kaje ka sami mahaifin Amrah ayi walimab da za ayi na tarbi diyata and welcome her to my home kafin na fara this treatment na rasa karfin welcoming Amrah ja idanun Aliyu yayi yabude baki zaiyi magana Mami tadagamai hannu alamun yamata shiru takalli Chidi dake kallonta tace I want to stand on my feet and welcome my daughter home da lafiyata ina cikin hayyacina na tabbatar yes d ana na tare da matarsa kafin na fara treatment din, hakan will guarantee me koda na rasu in the process na treatment din banda regret sabida nasan Aliyu ne nada mata that will look after him, idan kuma na rayu naji sauki zanga jikokina na rainesu dan haka Dr kabani 1week I will come back for my treatment Mami tamike tace muje nurse Nurse tamike tatie hannun Mami suka fita Aliyu na zaune kawai this is biggest butinsa he took leave for this but Mami is just about aure aure aure saikace yagayamata auren soyayya ne ko son yarinyar yake, Chidi yayi small smile yace Mothers will always be mothers Aliyu Ijiyan zuciya Aliyu yasauke yayi wani gajeren smile daya tsaya a lips nasa yace I will love to meet Daddy today dasauri Chidi yace sure kazo anjima da daddare zan gayamai Gyadamai kai Aliyu yayi yace thank you yawuce yafita daga dakin zuciyansa tafarfasa kawai yakeyi kaman zai fito. EPISODE 5 Wajen mota Aliyu yasame su tsaye suna hira yabude gaba yashiga abinsa Mami tasan ransa abace yake amman tamai banza tashiga baya Nurse ma tashiga yaja motan sundanyi nisa Mami tace Aliyu zaka bani kati zanje hado akwaiti dasauri ya kalleta ta madubi baice komiba sabida basu kadai bane awayan Mami tace wai ina Maheer dina ne ina yashiga yazo dan nasan muka biyema wannan kunya xamusha bari muje gida nakirasa da waya shima Aliyu ambato Imam yasa yahau tunaninsa rabonsa dashi tun shekaran jiya dayaje wajen Abba agidansu shima zai kirasa yaji ina yashiga ahaka har sukakai gida yayi parking sabida ana kiran salla yawuce yafita Nurse da Mami sukai ciki Mami tafara zama akan kujera tadauki wayanta dake wajen taga wayan ma ashe yamutu kunna wayan tayi tashiga kiran Imam amman harya katse bai dagaba takirasa yakai sau uku bai dagaba tace hala yana ball nasa ne ta ijiye wayan tawuce dakinta dan zuwa dalla saikuma ta dakata tajuyo ta kalli nurse tace kinga karki aka kayan nurses dinnan gobe dake da Chef zaku rakani Mall nahadama yarinyana akwati akwai wani cleaning company danaga ana talla a tv k me yan media kitayani kiransu suzo zan b fe flat din Aliyu gobe afara gyara sAbida mufara planning nurse na murmushi sosai tace Mami kome kikeso we are all here for you Mami tace Allah miki albarka ahankali tace Ameen saida safe Mami tadauki jakanta ta tafi. Salla yayi yana fitowa daga masallaci anan waje ya tsaya yaciro wayansa yayi dialing number Imam harya katse bai dauka ba sai kawai yamaida wayan aljihu and yaso shine zai rakasa gidansu Ziora baiso yaje shi kadai wlh gashi baida wani Aboki wayansa ne yahau ringing dasauri yadaga cus yadauka Imam ne yaga Beeba ce katse wayan yayi yamaida wayan aljihu yawuce yakoma gida sai after ishai zai tafi gidan. Bayan Ziora takoma side nasu wanka tafada cus kayan datasaka jitayi kaman sunsa fatanta yamata nauyi tafito tadauki waya tana kiran Mami amman wayanta baya shiga murna kawai take ahaka bacci yayi awon gaba da ita. Wuraren 3 ma Mommy tashigo gidan sama tayi kafin tawuce dakinta dakin Ziora tabude ganinta tayi kwance kan gado tana bacci da dan pant kawai ajikinta da singlet Mommy ta kadakai tajawo kofa tarufe takoma nata dakin ta watsa ruwa abinta ta chanza zuwa simple kaya tafito ta taho dinning tadauki plate tana deban abinci da chef nasu tadafa shigowa Daddy yayi takuyo kallo daya tamai tadauke kai dan har yanzu basu dawo daidaiba zuwa wajen yayi ahankali yayi hugging nata ta baya tareda manna mata kiss a kumatu ahankali yace welcome back dan sanyi jikinta yayi saita dakata da aninta takeyi hannunsa yasa ya karbi plate din yace lemme help sakinmai tayi ya karba ya ijiye saiya jawo kujera yace zama Mommy tayi ahankali yashiga samata white rice din da stew da nama yasa spoon ya matso dashi gabanta yace can you eat yourself or I should feed u? Kallonsa Mommy tayi sai tace biko tell me why are you being nice to me all of a sudden cus I know as of this morning ni da kai fada mukeyi murmushi Daddy yamata yace I just realized you re everything to me Nwunye, you gave me the most beautiful children what is the pint of fighting wanda da bamuyi ba sai yanzu Mommy tace owoooh nima shina gani, Nwunye we ve been married for years imagine Micheal our first born is about 38yrs now, Nwunke you converted ka koma musulmi ban kyamaceka ba I stood by you, I supported you I loved you regardless I still make my body available for you after kazama musulmi ne ma kamin cikin Ziora amman ni kace Ziora bazata auri Moses ba Mommy tai magana tana kallonsa sai kuma takai hannu takamashi tace Nwunke do you think zan iya bama Ziora abinda zai cutar da itane? Ahankali Daddy yace I know you can t, I know how important Ziora is to you and I know why you are doing this, banki taki ba, kawai addinin m ne musulunci forbid our women to marry Christian Mommy tace lallai aiko nida kai munada aiki agaba, Nwunke kaga im very very hungry I don t want this conversation dan haka munarta kawai lemme eat be fire I loose my apatite Daddy bai kara cemata komiba he will tell her about the marraige in due time when she s calmer dan yanzu emotions are high tashi yayi daga dinning din yace where my Baby ? Mommy tace I met her sleeping tana dakinta Daddy bai kara magana ba ya maida kofan yarufe abinsa yafita. Wuraren 8 Aliyu yadawo gidan bakowa afalo dan bude dakin Mami yayi yaganta kan dadduma hakan yasa yamaida kofan yarufe yawuce sama bayi yafada yayi wanka yafito yashiga shiryawa a tsanake wani soft yadi na maza that looks like lace, milk color ta bala in zama ajikinsa, brush yadauka yayi combing suman kansa dayadan cika yana coiling up, yadauki turarukan sa ya feffesa sannan yazaro Hermes na maza which is favorite brand nasa na takalmi yasaka yasa agogo na polo yadauki wayansa yafito da wata card na motansa na Tesla fara kal yana fitowa ko ina yadauki kamshin sa har falo Mami dake zaune a falo ga bowl na fruits a hannunta tana tanaci ga waya a hannunta tana tabawa tadago kai takallesa sai kawai ta tsaresa da idanu Allah yama Aliyu kyau sosai wlh kap yaran mahaifinsa babu wanda yakaisa kyau har matan karasowa falon yayi Mami tace sai ina? Zama yayi anatse yayi shiru chan yace gidansu yarinyar chan Mami ta tabe baki tace kaji dashi Amrah ce yarinyar chan Dan ijiyan zuciya ya fuzar cikeda takaici yace I want to see yanda everything can be done within this week cus inaso kifara treatment dudda maganan yama Mami dadi amman ta tabe baki tace gwara dai inba hakaba naki yin trail din sabida ka yardama ka auri Amrah nima na yarda zanyi kawai kallon Mami yake, tace gobe za a fara gyaran flat naka nasa akiramin kuma gobe zan fara fita sayan kayan akwati kaman yayi ihu yace Mami all this aren t necessary this girl idan tazo she can stay a any room datakeso upstairs ko dakin ki ma anan duk wannan shirin aka gama treatment dinki za a yisu ko ? Mami tace lemme just pretend banji makace ba, kudin karasa ko ubanka yarasa kudin da yarinya Amarya zata zauna a flat nata, ni wlh sabida ma jikina ne da maitan ka
Chapter 55 · 0% Book details