← Book details Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 99

Sashe 14

Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

M SHAKUR
EPISODE 9
Hair stylist dakema Ziora tsifa tace
every month ko 2months depends tana zuwa yin kunshi anan but she always looks sick daman, yanzu yazamuyi
duk yan wajen sukai shiru dasauri Ziora tace
give me your phone lemme call Ya Moh
ba musu ta bata dasauri Ziora ta karba har lokacin matan na jikinta ta kankameta tasa personal number Ya Moh tai dialing yana ringing yadaga cus family members kadai keda this his number arude tace
Ya Moh is me, are you in the hospital? Somebody is sick a saloon
zare wayan tayi daga kunnenta tace
yana hospital yace nakawota let
s put her in the car
key motan ta karba tabude, matan suka tayata suka bude baya akasa matan Ziora tasa mata seat belt sannan aka rufe motan kawai tazagaya ta shiga mazaunin driver taja motan da gudu, Matan dakema Ziora tsifa ta kalli sauran mutanen tace
I know the girl, their house da duka yan gidansu ma nasani, yayanta is a Dr so everything is fine this woman will get better
ajiyan zuciya kowa ya sauke aka wuce aka koma ciki.
Bini bini tana tuki tana juyowa tana kallon matan that was unconscious har takai private asibitin da Ya Chidi ke aiki, tana shiga tagansa yana waje tsaye da labcoat yana jiranta kafin tai parking ta sauke glass kasa ta kwalamai kira.
Ya Chidi
dasauri yataho zuwa inda tai parking tareda nurses aka bude baya aka dauki matan, Ziora tafito tabisu da gudu, Ya Chidi dake tafiya tareda nurses da sauri sauri yace
did you know her?
Girgiza kai kawai tayi tace
a saloon na ganta
calmly ganin dukta r
ude yace
okay check her car or her phone or bag, call any family member nata, haka akeyi meanwhile lemme go and save her life
gyadamai kai tayi idanunta na ciccikowa da hawaye, suka shiga room da ita hakan yasa ahankali tajuya tafito takoma mota tabude ta shiga, tashiga neme neme babu wani abu mai mahimmaci a motan taduba ko ina, saita dauki handbag nata tabude drugs tagani cikin wani roba haka na drug holder anyi arranging kaman magungunna dazata sha da rana ne ko dare dan gasunan daban daban, saiga wayanta iphone 16 taciro call log nata taduba, Son1 and Son2 sune the only contact datake waya dasu like almost all the time especially Son1, ajiyan zuciya Ziora ta sauke sannan ahankali tafara dialing number Son 1 amman kwata kwata bai shiga ba kusan sau uku, bayama ringing ne, sannan network basa cewa komi is as if number yashiga flight mode, sai kawai tai dialing Son 2 bai shigaba shima, tana dialing tana duba magungunan a roba suke so babu ma suna, jakan takara dubawa idanunta ne ya sauka kan wani kati haka plastic card, ansa I
m a Cancer Patient! Gaban Ziora yafadi dummm! Dawani irin gudu tasauko daga motan tabar wayan ciki tai cikin asibitin tana zuwa tafada dakin emergency room din inda Ya Chidi da nurses ke kanta dasauri tace
Ya Chidi look, I think she
s a cancer patient I saw this card and this drugs in her purse
dakatawa Dr Chidi yayi yazo ya karbi drugs din yabude anatse yana kallo kafin ya kalli Matan da har lokacin bata dawo hayyacinta ba, anatse tace
that explain everything thank you Smart Ziora you just save her life, excuse us now
ficewa tayi daga dakin tana kara satan kallon matan saita zauna anan wajen dakin tai shiru tai tagumi gabanta kawai sai faduwa yake tawani kalan damu na ban mamaki, cancer data gani ya tsayamata arai, bude kofan akayi dasauri ta dago kai Ya Chidi ne yace
have you spoken to her family?
Girgizamai kai tayi, Moh ya tsareta da idanu yace
call them again
yajuya zai wuce dasauri tace
Ya is she aw
..awa
Tai maganan muryanta na breaking tana shirin fashewa da kuka, Chidi yawani tsareta da idanu he
s not trying to blame her infact she did the right thing na saving life din mutum, but Ziora is so soft she easily get attach, ga tausayi da saurin kuka yace
when you know bakida zuciyan why didn
t you let saloon people to take her to the hospital? Ba saloon dinsu taje ba
? Bayan hannu takai tayi share fuskanta tass tahana kanta kukan karya mata bala
i sannan tace
I know you
re the best Dr saisa nakawota wajen yayana
hararanta yayi yace
kikamin kuka anan saina tattakaki my friend go and call her family
gyadamai kai tayi tajuya yace
ina zaki?
Ahankali tace
wayanta na motanta
tana maganan tawuce tana goge hawayen, tawuce waje wajen parking space tabude motan ahankali tadauki wayan tana danna screen saitaga 3 missed call from Son1 dasauri tai dialing number back ringing daya aka daga wani nutsassiyar tattausan murya dake cike da izza dakuma dan tsauri kadan yace
Mami nah!
Hakanan gabanta yafadi sai kawai taji maganan datake shirin yi ya karare a wuyanta, and voice din kaman ta tabaji somewhere but she is not certain, sauke ijiyan zuciya tayi mai kara.
uhmmmmm
shiru daga dayan bangaren akayi ba
ace komiba kuma ba
a kashe wayan ba, daurewa Ziora tayi anatse cikin turenci tace
my name is Ziora, I am with your Mom in hospital, I actually brought her her
Which hospital!
? Mutumin ya tambaya babu babu wasa kan muryansa, hakanan kawai saitaji kaman she
s in trouble kirjinta wani kalan dum! Dum! Dum! Yake mata, ahankali tace
kawai taji shiru dasauri tacire wayan daga kunnenta taga wayan yamutu ba chaji, Innalillahi yanzu mezata cema Ya Chidi? Ijiiyan zuciya ta sauke kawai ta ijiye wayan ta fito tadawo cikin hospital din direct dakin tawuce danta gayama ya Moh wayan matan ya mutu daidai lokacin matan tashiga bude idanunta Chidi na juyowa yakalli Ziora datazo da sauri wajen gadon sai kawai takama hannun matan tarike sosai cikeda damuwa tace
Mami
cus taji haka danta yakirata, bude idanunta gabaki daya Mami tayi tadaura idanunta dake nuna rashin lafiya sosai akan Ziora da idanunta suka cicciko da hawaye ga gyalenta ya zame kasa, kannan rabi daya a tsefe bari daya ba
a tsefe ba, ahankali Ziora tace
do you remember me Mami in the saloon? I
m Ziora, you fainted u were having nosebleed shine I drive you to hospital na Yayana, this is my brother Dr Moh Chidi, he
s my elder brother, I tried calling your children ta wayanki but wayanki yamutu ba charge, can you give Ya Moh number su yakirasu?
Lumshe idanu Mami tayi tabude kafin ahankali ta yunkuro zata tashi tana salati ahankali.
ilaha illallah Muhammadu Rasulullah
riketa Ziora tayi ta tashi zaune anatse, Ziora duk tai wani iri idanunta na cikowa da hawaye sabida yanda jikinta yayi zafi, anatse Mami ta kalleta tace
mesa baki tsaya an gyaramiki kai ba
? Kallon Mami Ziora tayi the woman looks so strong dudda she
s sick amman she
s talking about kanta da ba
a gama tsefewa ba, hawaye sake ciccikowa a idanun Ziora yayi Mami tai murmushi ganin bata amsaba yasa takalli Chidi tace
thank you for saving my life Dr Muhammad, I see inda Amrah ta dauko kirki da kuma taimako
murmushi kadan Ya Moh yamata, cikeda girmamawa yace
how are you feeling Ma?
Ahankali tace
Alhamdulillah! I have Cervical Cancer
tadanyi murmushi kadan tace
ina last stage already, banson needles, kowani damuwa danasan za
a kawoni asibiti ma na hana, I don
t want hospitals again, Doctors said I have 6months to live so I
m just waiting for time
yanda Ya Chidi ke kallonta haka Ziora ke kallonta idanunta sunyi ja and matan looks so strong, ga addini, ga karfin imani, how can you be this strong and comfortable kasan duka duka wata shidda or less yarage maka a duniya? Zuciyan Ziora, ahankali Chidi yace
how can we contact your family Ma
? Murmushi tayi tace
no need yarana duk suna wajen aiki yanzu, discharge me, Amrah kawo jakana akwai card dina kizo kibiya
dasauri Moh yace
you don
t have to pay Ma, lemme just write the discharge papers and sign, but how will you get home? I won
t let you drive in this condition
dasauri Ziora da muryanta harya dan dishashe sabida tausayi tace
I will drive her home Yaya
dan kallon Ziora yayi itama Mami ta kalli Ziora da idanunta sukai ja, duk babu wanda yayi magana yashiga rubuta papers din Ziora ta mike tace
na dauko wheelchair Yaya?
Gyadamata kai yayi da sauri tawuce tafita Mami tabita da kallo, ahankali Chidi yaja kujera yazauna gaban Mami hakan yasa ta kalleshi, ahankali yace
why will you give up so early? I know wani good trial I can enroll you maybe the outcome will be good Hajiya
sosai Mami ke kallonsa saikuma ahankali tace
no wonder kakeda kanwa that
s very very caring da tausayi just like you, look at how worried she is sabida ni da bata sani ba
tasake murmushi tace
I am just so tired! Kasan tun yaushe nake battling da cancer? Tun yarona yana 18yrs old today he
s 35yrs, he
s also a doctor like you, Oncologist and a Surgeon, but I guess haka Allah yaso ya ganni, and I
m very grateful to Allah dayama bani tsawon rai cus I thought bazankai this stage ba
daidai Ziora na bude kofa tana shigowa da keke, tazo har wajen gadon tamika mata hannu tace
Mami zo
ahankali Mami tace
toh yar Mami
dasauri Ziora ta kalleta saitaji kunya kawai tasa hannu takama Mami, Mami ta kalleta sosai saita taso shima Chidi sai kallonsu yake, zaunar da ita tayi a keken sai Chidi yace
let me
gungurata yayi har wajen motansu tare sukasa Mami a baya, yakalli Ziora da zata shiga gaba anatse yace
be careful kikai dropping nata take a taxi back home I still have patient here
yazaro kudi a pocket 5k yabata na hawa taxi ta karba tace
thank you Ya Doctor
tashiga gaba ta tada motan Chidi ya tsaya saida yaga fitansu yajuya yakoma ciki.
Suna shiga hanya tace
Mami where is your house
? Ahankali Mami tace
GRA 1st Avenue house number 10
she knows GRA thanks to Mommy datake rakawa unguwa haka tasa wuta bini bini tana tuki tana kallon Mami ta madubi dake lurada ita, har sukakai hadadden layin suka shiga, unguwan shiru kaman ba mutane, gidan dataga number 10 tawuce tace
Mami nan?
Ahankali Mami data lumshe idanu tabudesu tace
eh nan ne, yi horn
horn Ziora tayi ko sakan uku ba
a karaba aka shiga bude gate din wani maigadi ne dake sanye da uniform na security, gidan babban gidane sosai kusan girman gidansu ga lafiyayyun motoci anyi parking, ga Imam tsaye a tsakar gidan dake sanye da 3quater da t-shirt yayi folding hannu a kirji yana kallon motan saikuma yashiga zuwa while Ziora tawuce wajen parking tai parking daidai Imam na karasowa wajen, Ziora tasa hannu tabude kofan tafito batama lurada Imam ba, tundaga kafa yake kallonta zuwa jean da riga dake jikinta da mayafin dake kanta da yake a zame ga gashinta awaje, kallo daya yamata yaganeta dan yanada gane mutane, yahada fuska sosai yana mata wani kallo da hakanan saida Ziora taji kaman ana kallonta tajuyo dasauri suka hada idanu, faduwa gabanta yayi tana kara kallonsa trying to understand waye kuma wannan wani kallo yake mata haka, sai kawai taji dauke kai ta taho baya zata budema Mami kofa kawai Imam yasha mata gaba.
KAUNA DA SO
Chapter 14 · 0% Book details