← Book details Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 99

Sashe 88

Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nata yayi arranging, da kansa yaje kasa ya kunna burner yasa turaren wuta a ko ina cus yanason kamshi sannan yawuce yashiga bayi yayi wanka yafito daure da towel he s really missing that girl kaman tamai asiri, wlh he feels kaman yarufe idanu yabude yaganta anan, wani kalan shiga rai ne da Amrah he s finally seeing why Mami ke sonta, gabaki dayan gidan memory nata yake tadomai, yasauke ijiyan zuciya kawai, ringing wayansa yayi yadaga wayan Mami ne hakan yasa yakai wayan kunnensa baiyi magana ba, Mami tace Haidar kana ina ga Abban ku yazo kazo side dina anatse yace okay ya katse wayan yamike, cire wayan yayi ya ijiye saiya wuce yaciro wani yadi na riga da wando milk color yasaka yana kamshi yadauki turare ya feffesa sannan yawuce yafito yasauka yatafi flat nasu yabude kofa ahankali, Abba yagani zauna kan kujera yana sanye da manyan kaya, sai Imam da Samha da Amirah dukansu kallonsa suka sai Mami dake zaune kan one sitter tana sanye da hijabi har kasa, maida kofan yayi yarufe dasauri Samha da Amira sukace. Yaya ina yini gyadamusu kai ahankali yawuce yashigo yazauna kan kujeran dake next to Mami yana kallon Mami data bisa da kallo tanajin wani kaunar danta da tausayinsa cus ya wahala sosai aduniya ga karfin hali, kana ganinsa kasan yana kewan matarsa amman bazai taba nunawa ba, ahankali Imam yazamo daga kan kujeran dayake kai saiya taho gaban Aliyu yayi kneeling, Aliyu yayi kaman bai gansa ba wlh, kowa na dakin na kallonsu, ahankali Imam yahada hannunsa biyu yace Yaya Aliyu idan ka tanka Aliyu ya tanka, Mami batacemai kala ba hakama Abba cus anger Aliyu are very very valid, ahankali Imam yace I know my actions were inexcusable, nazauna namaka sheri kala kala, namaka kazafi, ban duba duka abinda kamin arayuwa ba, you ve been a brother to me you support all my dream kai ka dauke ni dana nuna inason ball and enroll me on a club katayani rokon Abba kan ya banni nai living my dream life, Yaya Haidar namaka laifi dan girman Allah kayakuri kayafemin banda wani yayan dayafi ka, wlh banason Amrah, banajin sonta araina ma, dan Allah kayafemin naci darajan Mami kayafemin kaji, you mean the world to me and I don t wanna lose a precious brother irinka yanda Aliyu bayako kallon Imam Mami ta kalla tasan yayi fushi and idan barasa bakiba Aliyu bazai yafemai ba, family is everything, bazata so kansu yarabu ba ata dalilin yarinyar dabata taba ma Imam kallon masoyi ba, ahankali tace Aliyu everybody makes mistake arayuwan nan, amman the best among us shine wayanda suka gane sunyi kuskure sannan suzo su nemi yafiya, don t just look at mistake da Imam yamaka, look at alkhairai dubu daya maka, this boy will leave everything yazo yazauna dani, yatayani hira, yasani dariya duk kana office a asibiti, the only abu da Imam baiminba shine girki shima sabida ko ruwan zafi bai iya tafasawa bane Mami tai murmushi kadan tace Imam is a good person, a kind soul, dan haka inaso kayafe masa, banson ka yanke zumunci da yan Uwanka duk inda akaje aka dawo baka da yan uwa daya wuce Imam, Samha da Amirah dan haka amance da komi, forget the past and move on Abba dake kallo Mami kaman zai hadiyeta tunda take magana yace ba Imam ba hatta ni namaka laifi, amman dagani har Imam din duk mun fadama sherin mace ne, tundaga kan sakin mahaifiyarka danayi da muguwan soyayan Amrah da Imam keji duk mahaifiyarsa tai asiri tasamana laya a pillow wanda naji tana fadi a waya shima Allah ne ya jiyar dani, I ve destroy everything, mun karbi addu a na tsari da kariya sannan nidai narabu da matan nan har abada, Aliyu kaine d ana na fari, you are the leader of the family, kowani family da crisis nasu, you have no choice you have to forgive and put family ka together kaji Aliyu that s what a family man does, kayafe mana cus hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, sannan ina maka addu a Allah yamaka albarka, Allah yabiya ka abinda kama mahaifiyarka tasami lafiya, dudda I was hypnotize lokacin dana rabu da mahaifiyan ka amman you stood your ground and took care of your Mom thank you Aliyu, I m very very proud of you, Maman ka is the best woman of this earth yayi maganan yana satan kallon Mami dataki kallonsa ma, hannunsa Imam yarike sosai ganin Aliyu still yaki kallonsa saiya kifa kansa kan kafan Aliyu hawaye na fita daga idanunsa ahankali yace m sorry Doc, please I really am sanyi Aliyu yaji aransa Mami tamai kallon ya yakuri hakan yasa kawai ya share abin aransa ahankali yadagako kansa kaman abinda Imam ke jera kenan hugging Aliyu yayi sosai Samha da kowa na dakin sukahau murmushi, hakama Mami kaman ance ta dago kanta hada ido tayi da Abba dake mata wani kallon maitan soyayya dasauri tadauke kanta kirjinta na bugawa. Lumshe idanu Aliyu yayi yana kallon fuskan Imam daya cika da hawaye yakai hannu ya share fuskan yace nayafe maka Imam but moving forward let s have better communication, kome kakeso say it out loud, stop believing people have the ability to understand emotions naka batare dakai speaking up ba, let s be better version of ourselves okay gyadamai kai Imam yayi dasauri Aliyu yakamosa yazauna kan kujera, Abba yace in sha Allah zanje gidansu Amrah ayi magana tadawo dakinta tunda an sami gaskiya, Allah yamuku albarka gabaki daya, Allah ya hada kanmu yadan kalli Mami yanadan rage murya yace Hajiya nabar yammatan nan wajen ki for now ? Mami batare data kallesa ba tai murmushi tace ai nan gidansu ne ko Samha? Gyadamata kai Samha da Amirah sukayi cus duk sunason Mami, Abba yakasa tashi yatafi sai uban kallon Mami dayake kaman yau yafara ganinta, Mami taji ajikinta tace muje na nuna miki dakinku Samha suka tattashi sukai sama Abba yabi Mami da kallo karaf a idanun Aliyu daya tsare Abba da kallo, shima Abba kaman yaji ajikinsa Aliyu na kallonsa saiya kalli yaron sai kunya yakamasa dasauri yamike yace bari naje naga mahaifin Amrah yayi wajen kofa dasauri Aliyu yashare and just pretend bai gane what is going own with his Abba ba. Bayan magrib Abba yakira wayan Daddy koyana gida yanason yazo Daddy yace masa eh, har gida Abba yaje Daddy ya tarbesa yakaisa asalin flat nasu Mommy tamusu sannu da zuwa aka kawo kayan sha da kwamulashe Abba yazauna yaci sosai Mommy tace bari nakira Amrah tazo ta gaidaka zata tashi Abba yace dakata tukunna my Inlaw yakalle dukansu yace nazo ne nabada hakuri bisa ga kuskuren abinda yafaru dakuma misunderstanding, bazan muku karyaba harda nawa iyalin are involves abin yanzu nazo nadauki iyalin Aliyu na maida masa da ita murmushi Mommy tayi tai shiru tabar Daddy yayi magana. EPISODE 9 Daddy yace kagan ni da ita nan yanzun nan muka gama maganan nan kan idan Allah yakaimu gobe zamu maidata gidanta sabida ita kanta yarinyar tadamu tanason takoma especially datamaji yanda aka sallamo Mami kasan kaunar dake tsakaninta da Mami murmushi Daddy yayi yace inlaw kafan dana saka naje na dauko diyar nan is only right nizam maidata, dama nasan maganan nan zakazo mini dana sanar dakai gobe zan kawota, namaka alkwarai gobe da safe misalin goma zamu maida Amrah dakinta bari akirata tazo ta gaidaka Mommy tawuce sama tabude dakin Ziora dake zaune bata wani farin ciki wlh, Mommy tace ga Baban Aliyu yazo dasauri ta tashi tace is he here to take me ? Mommy tace ba Daddyn ki yagaya miki gobe zamu maidaki da kanmu ba, tashi kije ki gaidasa ki duka har kasa ne not hug him ki natsu cover your hair gyadama Mommy kai tayi saitama dauki hijab dinta tasaka, she walks better now with all the gashi datake samu wajen Mom, tundaga staircase take kallon Abba tana murmushi tana zuwa gabansa ta duka looking at him tace Abba good evening Abba was so happy ganin she s calmer compared to rannan daya fara ganin ta ta natsu Alhamdulillah murmushi yayi yace tashi tashi how are you ahankali tace fine, Abba is Yaya Aliyu feeling better now? Abba yace yes he is dasauri tace Abba I love Yaya Aliyu a lot I can t leave without him adan kunyace Abba tace toh Allah kara dankon kauna tawuce tazauna kusada Mommy anyi hira sosai sai wajajen 11 yabar gidan. Da kyar Ziora ta iya bacci rannan da asuba ta tashi tayi wanka bayan ta zauna ruwan zafi tasaka normal half gown nata sky blue mai flowers farare, tasaka stud earring na gold tasa hijabin datazo dashi, tanaso Yaya Aliyu yaganta da hijab and be happy sannan tafito tun around 6 tazauna afalon sama tana kallon agogo takosa atafi dawowa daga masallaci Abba yayi yace lafiya princess dasauri tace Daddy let s go please bude kofa tayi tafito tace Madam remove that hijab kizo kitchen muyi breakfast Badan taso ba tabi Mommy kitchen sukai breakfast lafiyayyen akaci mommy tawuce sama wanka abinta ita da Daddy na jiran Mommy saida Mommy ta shirya tsaf tafito da gudu Ziora tamike tsaye sai kawai ta kwasa da gudu tafito tsakar gida Daddy yakalli Mommy suka kwashe da dariya suka fito hartakai wajen motan tabude baya tashiga abinta Daddy da Mommy suka taho wajen suka shiga shiga drivern Daddy yajasu Ziora tace Daddy I m very happy today I will see Mami and my husband Daddy yace wai ke you re not even talking about school ko dasauri tace Daddy I don t want school me Daddy yace baki isaba I will talk to Aliyu zaki koma turo baki tayi tace Daddy tell uncle driver to speed please ahaka sukakai gidan ana bude musu gate ta yunkura zata bude motan kafinma suyi parking. Mommy tabuge hannunta tace karatun dana koya miki kenan bazaki natsun ba ? Dasauri tace Mommy na mance I m just so happy ne that s why parking akayi Ziora tafara fitowa tana kallon flat nata dana Mami kaman tai shekara bata gidan kafafunta har rawa suke takalli motansu ganin Mommy na kokarin fitowa yasa kawai ta kwasa da gudu tai
Chapter 88 · 0% Book details