← Book details Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 99

Sashe 11

Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

sallama while Chidi na lallashinta. Daddy yau yana kwanan Barrister amman ko takan zuwa dakinta baiyiba yana nan zaune yana gadin yar gaban goshinsa, bini bini yaduba yaga ko tana numfashi sabida yanda take wani irin bacci kaman matatta har gari yawaye bacci take. Wuraren 9 tashiga bude idanu kadan kadan kanta yamata bala in nauyi na hang over ga kanta na ciwo as well dakin tashiga kallo tana tuna abinda yafaru the last abu data tuna is suna wajen golf ta karbi magani tasha that s all data tuna ta dago kanta a firgice ganin tana dakin babanta karaf suka hada idanu da Daddy da bata taba ganin ya hade mata rai hakaba, babu wasa kan fuskansa yace stand up go to your room, brush, shower, sannan kiyi sallolin dake kanki farawa tundaga azahar, idan kin gama ki sauko ki sameni a falo kasa ma amsa Dady tayi ta shiga sauka daga gadon tai layi zata fadi da sauri Daddy yariketa tadan kalleshi sai kawai yafauke kai yabude kofa yafito da ita yabude kofan dakinta ya shiga da ita ciki har zuwa bayi yasauke shigan da ita bayin gabanta sai faduwa yake ganin ran Daddy abace, shower yabude da kanshi yana tara hannu saida yaji ruwan yadawo zafin da yamai sannan yasata a kasa yace kiyi wanka yawuce yafita. Sosai gaban Ziora ke faduwa ruwa na sauka a jikinta tana tunanin abinda yafaru takasa tunawa kaman asiri ko amman dai tasan it has something to do with maganin datasha ohhh takai hannu bakinta ta ciza yanzu zasu fara blaming su Anna da Bella yanzu yazatayi? Ta tambayi kanta kafin tasan saki ranta cus tasan Daddy na nan, kaya tacire tai wanka tana mamakin waya cire mata kaya ma tagama tai brush tafito tazo tasha mai ta feffesa spray tadauki wani short gown white iya knee nata tasaka ta kulle igiyoyin hannun a shoulder tadauki dogon hijabinta har kasa tasa tai salloli tai azkar sannan ta cire hijabin tashiga neman wayanta dan kiran kawayenta taji meya faru? But bataga wayan nata ba, dan tahowa wajen kofanta tayi tabude kofan kadan kaman mara gaskiya tadan leko karaf tahada idanu da Ya Khaleel Obinna yamata wani mugun kallo yace Daddy na kiranki turo baki tayi bata wanijin tsoro as long as Daddy na nan tasan babu abinda za a mata, Yayanta na gaba tana biye da shi abaya suka shiga sauka kasa inda Daddy yake zaune kan one sitter haka ma Mommy, sai Ya Chidi duk suna kallonta da dan riganta iya guiwa gashi tayi shegen kyau tazo falo bata yarda ta kalli kowa ba tazo gaban Daddy ta tsaya tace gani Daddy yanda Daddy yaga bata damu bane ma yakara batamai rai, anatse yace me kawayenki suka baki kikasha jiya? Turo baki tama Daddy cikeda tsiwa danta dauka yau rannan wasa ne tace why do you feel like my friends always have something to do with my condition? Stop calling their names Dad yanda Mommy ke kallonta kaman ta dauketa da duka amman tana danne zuciyanta yayinta ma kaman su tashi su tattakata, Daddy yadaka mata tsawa yace you think I m joking? I said what did they gave you? Dan matsawa baya kadan tayi still tana turo baki tace ni babu abinda suka bani, I just wanted my head to be light tunda damuna kuke a gidan nan especially Mommy shine nasaya tawani kara turo baki ashagwabe tayi tace you guys are so annoyin Tasssss! Daddy ya dauketa da mari da saida tai tangal tangal dan batada karfi ko kadan Mommy taji kaman tazuba ruwa kasa ta shanye, wani irin kallon Daddy Ziora tayi dan ta firgita iya firgita har bargon kashinta kawai jikinta yafara tsuma cus Daddy baitaba dukanta ba tunda tasan kanta. KAUNA DA SO
Chapter 11 · 0% Book details