Sashe 26
Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
safe din mai sanyi dasauri ta jefa syringe din cikin jakanta tafito bakowa awajen tawuce tafita daga asibiti tawuce ta shiga motanta taja tanason tai sauri takai GRA around 10 daidai sanda zai fito, shopping tama Mami sosai nagani nafada sannan tafito tasa komi a mota taja motan, wuraren 10 takai kofar gidan bata shigaba tai parking awaje. Aliyu na zaune a dinning ya shirya tsaf yau yadi yasaka ash color tamai bala in kyau saidai baisa hula ba, yana sipping coffee, Imam shima zaune awajen yanashan nasa coffee wayansa yayi haske, daga wayan yayi yakalla dayake shi baida password awaya message ne Beeba ta turomai. m outside your compound nazo gaida Mami na shiru yayi yana kallon sakon sai ga kiranta bai daga wayan ba yamike tsaye batare daya kalli Imam ba yace Habiba is outside dasauri Imam yace wooo yayanmu kace Inlaw Mami na waje, finally yau Mami zataga budurwan yay Juyowa yayi yamai wani kallo hakan yasa maganan ya makale yana murmushi, Aliyu yawuce yabude dakin Mami yashiga yasameta zauna sai matse idanu take tana faman karanta chats na Ziora, ahankali yace Mami anzo gaisheki dasauri Mami tadago kai tace Amrah danake chatting da itane wai hartazo? Ahankali yace s Habiba from hospital namu yana maganan yajuya yafita, yabude kofa yafita gaban flat nasu, da hannu yama gateman alamu yabude gate, bude gate, gateman yayi tashigo da motan yana tsaye a compound yamata wani irin kyau sai kallonsa take fuskan nan ahade ba yabo ba fallasa. Parking tayi tafito tana sanye da lace mai bala in kyau mai red da milk tayafa wani milk gyale akai taci gayu sosai, tarike wani Zara bag, bayan mota tabude tadauko babban ledan super market tarike ta rataya handbag dinta tana kallon Dr daya tsaya daga wajajen entrace na flat nasu yana mata wani kallo ba yabo ba fallasa harta karaso wajen, cikin sassanyan murya Beeba tace baraka min murmushi ba? I said sorry noww haba Mijina juyawa yayi baice komiba yabude kofa yashiga yana bude mata kofa ya koma gefe danta shigo, Mami na zaune kan sofa tasaka lace mai kyau itama ga charbi a hannunta tana murmushi mai kayatarwa tace bismillah bismillah shigowa Beeba tayi tana sunnar dakai, Aliyu yamaida kofan yarufe yawuce dinning abinsa, while Beeba na shiga falon ta duka agaban Mami tana boye fuska tace Mami ina kwana coffee dinsa Aliyu yadauka yawuce staircase yayi sama abinsa Imam yasaki baki wai wani kalan bahaggo ne Yaya, yakawo budurwa yatafi sama abinsa kuma, tasowa yayi yazo falon yace Dr Beeban Ya Haidar ne agidan mu yau ? Mami ta kalli Imamu dan ita batasan Aliyu da kowa ba, Aliyu baitaba gayamata yanada budurwa ba, ko taga yayi waya dawata mace agabanta ba. EPISODE 1 Beeba taji kunyan maganan da Imam yayi tarufe fuskanta da gyalen data yafa, cikeda so na iyayi tace ina kwana Mami ya karfin jikin ? Cike da karamci Mami tace tashi daga kasa kizauna kan kujera maza batai musu ba ta tashi tazauna saman kujera kanta akasa tanajan gyalenta gaba tana boye fuskanta kaman wata Amarya, Mami ta kalli Imamu tace Maheer duba kitchen sa akawo mata breakfast dasauri yace okay Mami Beeba tace Mami nayi breakfast agida ai da baki sa ba Mami tace a kinzo gidana dole kiyi kari, ya su Mama ya kowa agidan naku ? Ahankali Beeba tace duk sunce agaisheki Mami fitowa Imam yayi daga kitchen din, Chef din Mami biye dashi rikeda tray da kayan shayi kekai tazo ta daura akan coffee table takawo mata, takoma kitchen Imam shima yasami waje yazauna Beeba ahankali tace ina yini Yaya Imam murmushi yayi yace Alhamdulillah ya patient ya clinic? Murmushi tayi tace lafiya lau daidai Chef din nakawo tray na pepper soup, da masa sai kuma chips da fried egg, tajuyo takalli Mami tace am do you need anything ? Dasauri Mami tace no thank you tawuce takoma kitchen, Mami takalli Imam tace jeka kakiramin yayanka naji kaniyan me yaje yi asama, kunyan banxa kunyan wofi dan karamin dariya Imam yayi yawuce sama abinsa, knocking gaban dakin Aliyu yayi, daga ciki Haidar yace come in bude kofan Imam yayi dakinsa nawani irin kamshi mai bala in dadi, ga AC na aiki kaman kankara, dakin ko ina a gyare tsaf yana zaune gaban desk dinsa ga laptop agabansa yana sipping tea din, cikeda iskanci Imam yadan sosa kai yace kai Ya Haidar ka kawoma Mami mata kawani gudo sama to kunyan wa kake ? Dago kansa Aliyu yayi yama Imam wani kallo dayasa Imam ya kwashe da dariya harda rike ciki yace toh Mami tace kazo come and explain, baka taba gayama Mami you are seeing Beeba ba, koni badadan nazo hospital naku naganta office naka ba I wouldn t know, come and explain wani hada rai Haidar yayi hakan yasa Imam yafita da sauri yana dariya, yadan bata lokaci kafin yamike yabude kofa yafito, Kansa akasa ya shiga saukowa daga staircase Mami tadago kanta tana kallonsa tana karantan sa, forget Aliyu nada zurfin ciki but tafi kowa sannin waye yaron nan aduniya, karasowa cikin falon yayi yace gani Mami ahankali Mami tace sami waje ka zauna ahankali yawuce kan kujeran da Imam ke kai yazauna gefensa kansa akasa, kallonsa Mami tayi ahankali tace Aliyu dago kansa yayi yakalleta, cikin hikima da magana irin na iyaye manya masu dattaku tace munyi bakuwa baka gayamin wacece ba kai tafiyan ka sama sabida mugun hali, wacece ita? Mami tamai tambayan asanyaye, dan kallon idanun Mami yayi sai yadan sunnar da kansa yace she is Habiba Mami calmly Mami tace Imam ya fadi wasu abubuwa da ban gane ba, kasan waka abakin mai ita yafi dadi, who is she to you? Dan dago kansa yayi kadan yakalli Mami, baisan mesaba saiya kasa magana, anatse Mami na kallonsa ido cikin ido tace wacece Habiba agareka Aliyu? Gaban Beeba sai fadi yake jin Mami tamai irin tambayan nan baice komiba, yanda Mami ya tsaresa da ido yasa yakasa magana yadauki kusan good one minutes kafin ahankali yace she is my colleague Mami, we work in the same hospital wani kalan zafi zuciyan Beeba yahauyi yanzu Aliyu bazai iya gayama uwarsa itace yarinyar dazai aura ba? Bazai iya gayama Mamansa itane budurwarsa ba? Almost 5yrs yanzu una dating fa, shi kansa Imam saida yadan kalli Aliyu jin abinda yace, wai mesa Ya Haidar is so strange ne, kunya da nauyin yagayama Mami budurwarsa ce yakeyi ko mene? Mami data gama nazarinsa da amsan daya bata baki tabude zatai magana taji muryan Ziora daga compound ta kwalamata kira. Mami my best friend, I m hereee tana maganan kanajin step na gudunta daga gate tsabagen bala i harta iso, tana bude kofan falon, tana sanye dawani pink gown mai bala in kyau, bai gama saukan mata kasa ba yakai kusan idon sahu but kana ganin gown din kasan it s very expensive, tasaka wani sneaker very simple and light mai bala in kyau white, ga veil na chiffon white shima data daure kanta da shi, taja dan kwalin baya kana ganin kanta da fine edges nata da sukai kaman an saka gel kuma batasa komiba, sai black jakan makaranta abayanta ta goya, baya yafa gyale ba kwata kwata, but ka kalleta saika kara kallonta she looks like a baby doll, tayi wani irin kyau that is breathtaking, ko kadan bata lura da mutanen falo ba kawai tai wani tsalle tahau jikin Mami da fara a yagama lullube fuskanta tai hugging nata kaman wata yar yarinya, ta manna bakinta a kumatun Mami cikin zakin muryan nan tace muahhhh Mami na, oyoyoooo tai hugging Mami da tuni ta washe baki tana murmushi from kumatu to kumatu, duka yan falon kallonta suke especially Imam, while Aliyu yawani kirne fuska cus baison yara like her, mahaukata, marasa natsuwa, busybody, da rashin kunya, Mami tashafa bayanta cikeda so tace daga ina kike haka waya kawoki ? Dasauri tace daga school Mami I took bolt, Mami where have you been I ve been chatting you up no response , Mami dake kallonta tace mayafin kuma fa Amrah dawani irin sauri tazare gyalen kanta gashinta datai parking da pink ribbon yayi kyau ya bayyana tace you see Mami I carried veil, I tried to do that rolling dakikamin jiya shine Mommy said I look funny she removed it ta dauramin akai, she dropped me a school and went to Church Mami tai shiru tana kallonta har lokacin Ziora na saman cinyan Mami, Mami tace ga yayyinki baki gaidasu ba dasauri ta juyo, ganin Imam ga Aliyu saikuma wata da bata ganin fuskanta sosai sabida gyalen data jawo gaba yasa da sauri ta sauka daga jikin Mami takoma gefenta takai hannunta takama na Mami tarike, tarage muryanta chan kasa kaman mara lafiya tace good morning Yaya Imam, Good morning Yaya Aliyu tadan turo baki sannan takalli matan tace good morning saikuma takalli Mami murya kasa kasa kaman munafuka baruwanta da zuciya daya tace who is she Mami? Mami tace s Yaya Habiba, greet her properly dasauri Ziora ta kalleta tace good morning Yaya Habiba mikewa Aliyu yayi dasauri Ziora ta kallesa, wani mugun kallo yamata batasan sanda tashiga jikin Mami da gudu ba tai lamooo, Mami tabata rai tace wai me hakane Aliyu, ina dalili? Jan gyalenta Beeba tayi baya dan taga ma wace yarinyar ce haka daga shigowanta attention yakoma kanta ana cikin mahimmin magana, kallo daya tama Ziora tagane yarinyar from mall that day, faduwa gabanta yayi, meya hada yan gidan nan da arniyan kabilan yarinyar nan eh? Car key Aliyu yadauka yayi kofa kawai yafice abinsa, Imam yadan saci kallon Ziora datai lakur gefen Mami yace Mami nafita jogging Mami tace adawo lpy yana ficewa Beeba ta sauke gyalenta baya ahankali tamike tadauki jakan super market din tace Mami gashi bayawa dasauri Mami tace ahhh nan fa daya ina dalili zaki kashe kudi yara daku eh Habiba Beeba tai murmushi tace Mami dan Allah ki amsa Mami tace tom Allah amfana Allah kuma yayi albarka gyadama Mami kai tayi tace Mami meza a daura miki for lunch or akwai wani abu dazan tayaki yi ? Murmushi Mami tayi Ziora tawani kwanto jikinta tana kallon fuskan Beeba sosai dan ita ta iya kallon mutane