Sashe 54
Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sweet abaki tace Alhamdulillah Babanka yakirani ya daura maka aure da Amrah dasauri Aliyu ya kalli Mami yana dakatawa da lasan sweet na bakinsa dayakeyi Mami na farin ciki sosai tace an daura muku aure Aliyu yanzu Amrah matarka ce Halak malak dasauri yace but Mami why? Daga zuwa tambaya ? Dasauri Mami tamai dakuwa tace mai garinku Aliyu, I m happy da aka daura an daura muku aure ne sabida Allah ya kaddara yau za a daura muku auren ayaune Amrah zata zama matarka ko kana wajen ko baka wajen did u see wat I tell you nagaya maka Amrah matarka ce saida ma tashigo rayuwana, none of us yayi tunanin yau za a daura aurenku kai kana nan kana bacci ni inachan ina abin gabana but an daura maka aure Aliyu so Alhamdulillah Mami tazauna tana kallonsa ganin fuskansa yanuna he s not happy at all tawani hugging nasa ta side tace kasan menakeso yanzu inaso ayi bikin kutare cikin one week hade fuska yayi yakalli Mami kaman zaiyi kuka yace Mami I m not yet ready to start living together with that girl dawa zanji please dake ko da ita da kanta ke rawa? Besides za a fara trail naki we are going to hospital today once Dr Moh calls Sosai Mami ke hararan sa tace eh muje zan mai magana inhar abinda zai dauki sama da sati daya ko biyu ne abari saina gama bikin yarona sai afara trail din, Aliyu I m so happy kayi aure, yanzu ci, sha, sutura, kulawa da komi na Amrah yakoma kanka, ka kare hakk nda da kyau kar Allah ya hukuntaka lemme even go and call my baby, ka kunna wayanka ka shiga watsapp Abban ka yatura maka video daurin auren da komi anjima kaje ka gaishesa kamasa godiya Mami tana maganan ta tashi tafita Aliyu yabita da kallo ganin yanda she s so happy harda yar wake takeyi kaman ba Mami ba, wallahi he s not happy at all da auren nan all lisaafjn sa yau akaje tambaya su kara bada rana da zasu koma asa rana maybe one month ko two month, amman first day na zuwa gidan yarinya kawai Anba yaje ya dauro masa yarinya, that girl that is senseless da batasan komiba he s not happy duk ransa yakara bac daman gana rannan dayake fama dashi. Mai machine bai dire Imam a ko ina ba sai gidansu sauka yayi ya kwaso iban kudin dake pocket nasa yabasa kawai yashiga gida idanunsa sunyi jazur yayi flat nasu da gudu gudu yabude kofa kaman mahaukaci Mommy na zaune tareda mai zuwa mata gyaran kuma a palour taga Imam yashigo azuciye idanunsa sunyi jazur ko kallonta baiyiba ba sallama yayi stairs da gudu tace Maheer Maheer, Imam, Imam lafiya ? Tamike tana kallonsa amman harya kai sama mai gyaran kumban ta kalla tace ina zuwa please jirani ba lafiya bantaba ganin Imam hakaba bene tayi tawuce sama direct zuwa dakin Imam din tabude kofan dakinsa ahankali tanajin sheshekan sama sama ga dakin duhu faduwa gabanta yayi yamaida kofan tarufe ta kunna wuta Imam dake zaune abakin gado yajuyo da idanunsa jazur yace leave me alone Mama, leave my room Mama da hankalinta yatashi sosai cus kap yaran babansu babu happy child like Imam baya fushi he s always full of life ga fara a ga wasa ga barkwanci seeing him like this ya tsananin tada mata da hankali tazo wajen gadon taja kujera ta zauna tana facing nasa tace Imam what happened to you? Bayan hannu yasa yana g e fuskansa bayama magana sai ijiyan zuciya dayakeyi, Mama takama hannunsa ahankali tace Maheer nine fa, mahaifiyarka Akwai abinda bazaka iya gayamin a duniya ba, mwya faru Maheer, menene my Imam ? Kallon Mama yayi da jajayen idanunsa abun is eating him up wayanda yadauka sune suna sonshi and consider them family betrayed him, saikawai ya sauka daga gadon yazube akasa yana daura kansa saman cinyan Mama hawaye masu zafi suna fitowa Mama tace Imam talk to me ko menene I m sure baifi karfin Allah ba and I m still alive tell me dago kansa tayi ta goge mai fuska tasss tace gayamin ahankali yace Mama nine mutum na farko dana fara haduwa da yarinyar nan sunanta Amrah amman Igbo ce Mama ta tsaresa da idanu tana kallonsa tadai daure karta hanasa magana yace akwai wata rana muna Golf club tareda Nabeel rannan ne first time Dana hadu da ita, something happened ta Mami ta suma a saloon dasauri Mama tace wace Mami? Ahankali yace Maman Aliyu da kyar Mama tai controlling kanta tai shiru Imam yace tadawo da Mami gida still dani tahadu har mukai magana dayasa Mami tagane nasan yarinyar nan daga wani waje, Mama all this while ko kallo yarinyar nan bata ishi Ya Aliyu ba, ko yarinyar tazo gidan cus itada Mami na shiri sosai dani kadai take hira har naman sauketa a makarantan su, Mama k m ina gidan nan fa, ko ranan nan bata da koy ninakai Mami asibiti ta duba yarinyar, yau Abba yamin text na shirya zai rakasa wani waje muna zuwa naga gidansu yarinyar ne wai yaje nemawa Aliyu aurenta anama daura auren nabar wajen Mama kuma Aliyu nada budurwarsa likita fa Dr Beeba, nikeson Amrah, I ve been wanting to tell her amman rashin lafiyan nan datayi dakuma match dana buga made me got so busy I even gave her ticket I was planning tazo rannan zan fadamata amman sai bata zo ba Mama do you know wat is paining me? Mama ta girgixamai kai, Imam yace yanda dagashi har Mami suka boyemin komi wlh wlh bantaba ganin Aliyu yama yarinyar magana ba ma, sannan Mami bata taba gayamin Aliyu na son Amrah ko wani abu ba, danaga Aliyu gidan nan I was asking him Meyazo yi yaki kulani that means dukansu sunsan inason yarinyar shine suka biyemin especially Mami datasha ganin wasana da yarinyar har ina sata kuka, Mama why will they do all this to me bayan everything dana musu? I do everything for Mami, o take care of her, I baby sit her amman nizasuma haka su boyema wat is going on ? Budan bak n Mama tace Allah yakara Dudda harga Allah tasan cewa bazata taba bar n danta ya auri wata kabila ba indai ba bahaushiya bace but taji dadi sosai, tace sanda nace cemaka karabu da mutanen nan kajini? Gani kake kishi ne na tsani uwar Aliyu ne kawai amman gashinan sun gwadamaka halinsu, duk zaman dakayi kana musu boyi boyi duk rannan duniya kana gidansu amman suka maka wayau suka aure budurwan ka yarinyar dakkaeso sukai hakan without coughing anything out sAbida karma kasan meke faduwa good for you, kai kasan waye bil adama kuwa yanda Mama ke maganan kaman Imam ya hadiye zuciya yamutu sai goge kwalla yake Mama tace munafikin miskulun yaga kanason yarinya yabi ta kasa ya aureta mutanen nan makirai ne goge idanunsa Imam yayi yamike kawai abinsa mikewa yayi yana huci yace Wlh wlh bazan yardaba nina fara sanin Amrah kuma nina fara sonta Mama cikeda son tunzurasa tace to ya zakayi? Mezakayi aure anyi an gama? Amrah tazama matar Aliyu? An riga an cuceka an aure maka yarinyar dakakeso my dear kwanta kai bacci ka lallashi kanka tommorow is another day ai yanzu ka kiyayesu before Aliyu ya kwace maka har club din ball dinka cikin zafinrai yace wlh wlh Mama bazan taba yafewa Mami and Aliyu ba and I will make them pay dearly for this thing dasuka min you will see yana maganan yajuya yafice. EPISODE 5 Dakin Barrister tashigo ta tarar da Ziora na tsaye tana kiciniyar kwance daurin lafayan da ta mata na kugu takasa budewa amman harta cire rigan ko bra babu ajikinta ba kunya Barrister tamaida kofa tarufe tace wai bazaki dena tsirara haka kiyi tumbur ba bakisan you are married ba yanzu? Kwata kwata bata maganan take ba tace Step Mom I can t open this help me please hannu step Mom tasa ta kwance mata abin tadauki yar half gown nata tabata tana dauke kai tace ungo nidai sa kaya kije falo Babanki na kiranki dasauri tazura rigan tafito tayo falo da saurinta zaune taga Daddy a falo da Chidi da Obinna duk suka kalleta Daddy yace zo nan Princess dasauri tawuce wajen Daddy zata zauna kan cinyansa as usual Daddy yace no you re a married woman now all this things kidena kinji dasauri tace okay Daddy tazauna gefen Daddy tana kallonsa Daddy yace I don t want any of you to tell your Mother about what happened dakaina zan sanar da ita anjima da daddare and explain everything to her, no matter wat your mother is your mother and I will want her to bless your marriage Ziora ta gyadamata kai, Daddy yace when you want to greet your inlaw in Hausa land you don t hug them, you bend and greet them, kinajina? Gyadama Daddy kai tayi tace yes Daddy Daddy zaiyi magana tace Daddy me I don t even want the celebration the one we did today is enough for me since I don t have any friends the ones I had kunce baku sonsu, I will pack all my clothes today and you and my brothers will take me to my husband house please kowa kallonta yake Daddy yace okay but I will have to discuss that with your husband first Ziora tawani washe baki tamike tace okay lemme go to my room and call my Mami tamike bata jira amsansu ba ta fece da gudu Chidi ya dafe kai Obinna ya kwashe da dariya Daddy yamike kawai yabita, Obinna ya matso kusada Chidi yakawo bakinsa saitin kunnensa yace if I m that Dr ko, I swear I will show her wat marriage is da kanta zata fara kuka batason auren again duk rawan kan nan zata bari Chidi yamai wani kallo kawai yatashi yace natafi hospital yawuce yafita yanama Aliyu text congratulations Brother I will be at the hospital any moment from now Shigowa Aliyu yayi gidan bayan yaje yayi la asar yakalli Mami data riga ta shirya cikin hijabinta sky blue tasaka lace tayi kyau sosai abinta yace s go