Sashe 47
Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na karasowa wajen yakalli Mami datamai mugun kallo tace idan na duba Amrah zamuyi magana mahaifinka ya kirani gyadamata kai yayi, Imam daya kosa yaga Ziora yace muje Yaya gaba Aliyu yayi suna biye dashi har wajen dakin batare daya shiga ba yace I have a patient bari naje Mami ta gyadamai kai tanasa hannu tabude dakin da sallama Daddy ne kadai adakin zaune kan gadon Ziora na kwance tayi pillow da kafan Daddy tadaura kanta akan kafafunsa idanun nan luhu luhu, Daddy na ganin Mami yace come inside Madam come inside please jin maganan Daddy yasa Ziora tabude idanunta dasauri tana ganin Mami tawani zabura ta tashi daga jikin Daddy kaman yar yarinya dataga Mamanta tawani bude hannu irin Mami tazo tai hugging nata Daddy kawai ya tsare diyarsa da kallo yana tashi daga gadon sabida Mami tazama comfortable, Mami itama cikeda kaunarta tazo tace Amreery na Patient oyoyooo hugging Mami tayi sosai tafashe da kuka tace Mami everything is paining me, my bombom is sore Mami kunya Imam yaji, Mami tace s okay za a sallameki sai agasa jikin da hot water now stop crying tasaketa tace tsaya na gaisa da Babanki takalli Daddy cikin harshen hausa tace ina yini mai gida ya mai jikin Amrah Daddy daya gane abinda tace sosai yace lafuya lafuya Hajiya Anatse Imam ya duka yana sunnar dakai yace good evening Sir stand up stand up he s your son too? Ya tambayi Mami data gyadamai kai alamun eh, Mami tace ga tea namiki tabude Stanley cup din tabata dasauri ta karba tafara sha Daddy sai kallonsu yake, Mami tace nasamiki waina zakici? Gyadamata kai tayi, Mami tabude flask din Daddy na kallon wainan that looks so rich tasama Ziora ta karba tanaci tadan kalli Imam dake kallonta tace ga Maheer baku gansa ba kallonsa Ziora tayi ahankali tace ina wuni murmushi yayi yace Mami Besty ya jikin ? Gyadamai kai tayi batai magana ba danyau takanta take, Mami ta wanko hannunta ta karba da kanta tadinga bata wainan abaki tanaci sosai duk suna ahaka, Obinna yadawo tareda Chidi ma suka shigo duk gaida Mami sukayi suna mata godiya ta amsa suka gaisa da Imam daya kasa daina kallon Ziora da Mami ke feeding like a baby. Suna ahaka Chidi da wayansa yayi ringing yafice bai wani jimaba sai gasa yashigo dakin Mommy datai zuru zuru hankalinta atashe biyeda shi tashigo dakin kowa juyowa yayi ya kalleta especially Daddy daya mata kallo daya yadauke kai, Mami dakeba Ziora abinci ganin Ziora ta tsaya tana kallon waje guda yasa Mami tajuyo, Maman Ziora tagani taganeta sabida saloon that first time, tana sanye da wani half gown ga wig akanta mai kyau, anatse Mami ta ijiye plate din tamike tasauka daga gadon tace toh bari mutafi, make sure you take your drugs okay hannunta Ziora tarike tana dauke kanta daga kallon Mommy tace Mami don t goo Mami tai murmushi tace zan dawo soon ta karbe hannunta tawuce ta wanke hannunta tanama Daddy murmushi tace sai anjiman ku, Muhammad, Khaleel sai anjiman ku, Allah kara sauki atare dukansu sukama Mami godiya banda Mommy dake kallon Mami sosai, Mami tace barka da zuwa Maman Amrah sannan tabi gefenta tafice Imam biye da ita. Mommy takalli dukansu yan dakin tace and who is this woman ? Cikin zafin murya Daddy yace the woman that has been taking care of your daughter for you Ziora ta kwanta akan gado tana turo baki itama cus she s angry with Mom tace I am going to marry her Son Dr Aliyu and live with them forever karasowa gaban gadon Mommy tayi tace what did you say? Dasauri Daddy yace this girl is sick banson trouble zama Mommy tayi bakin gadon batamasan mezatayi ba gabanta sai faduwa yake tana kallon Ziora data nuna ko oho da ganin ta danta Aliyu take yanzu. Aliyu Imam yakira kan sun gama zasu tafi, yace su jirasa wayansa yadaga yakira Beeba ringing daya tadauka dasauri cikin yar karaman muryan nan yace where are you? Come and greet Mami zata wuce gida haderai tayi amman tasaki murya tace okay okay gani nan tana office dinka ne ? Ahankali yace no parking space dasauri tace tom gani nan zuwa ficewa yayi a parking space yasamesu saiga Beeba itama tana wani murmushi Mami tajuyo tsareta da kallo tahowa tayi ta tsaya dab da Aliyu taduka tace Mami sannu da zuwa ina yini dubiya kukazo ne ? Ahankali Mami tace diyata Amrah ba lpy shine nazo gaidata Beeba tace Allah kara sauki, Yaya Imammu ina yini murmushi yamata yace Dr ya patient tace Alhamdulillah tana murmushi, Mami takalli Aliyu tace yaushe zaka dawo gida? Ahankali yace nan bada jimawa ba Mami gyadamai kai tayi tace okay I will see you at home, sai anjiman ku ta shiga mota Imam na rufewa Beeba na musu bye Imam yaja motan Aliyu yajuya suna komawa cikin asibitin tare Mami ta tsaresu da idanu. Around 6:30 akai knocking, dakin is just Mommy da Daddy zaune a dakin da Ziora datake bacci mai nauyi dan tuntuni ta addabesu da rigima, Aliyu yabude kofan ya shiga tareda wani Dr Balarabe da nurses guda uku zai musu handing over cus yanzu zai tafi gida, Daddy yace Dr Aliyu sannu da aiki batare daya hada idanu da Daddy ba yace good evening Sir bai kallo Mommy data tsaresa da idanu ba yace good evening Ma hadarai Mommy tayi taki kulasa Daddy yace yanzun nan tai bacci ko atadata ne ? Aliyu yace no, no need, I just wanna handover everything to night Dr here, Dr Balarabe Daddy yace okay while Mommy na kallon yanda Aliyu ke magana da Dr and nurses din using English da Medical terms, tundaga kan takalmin kafansa Mommy ke kallo gaskiya ba karya Dr yahadu ga kyau gashi baya turenci like all those local hausa people cus tanama all Hausawa kallon marasa ikili da basu iya turenci ba, gamawa tsaf yayi sannan yakalli Daddy yace good night Sir Daddy yayi murmushi yace good night Aliyu, thank you so so much May God bless you gyadamai kai Aliyu yayi yajuya yafita Daddy yabisu da kallo same with Mommy data kallesa tace wlh wlh I m warning you cus naga the way you re looking at the Dr, even in your wildest dream ka aurama yarinyar nan bahaushe saina maka tashin hankali, this girl that doesn t have sense can not choose husband for kanta especially hausa men that marries plenty wives and suke divorce like it s nothing I m telling you ooo now Nwunye, hausa men don t respect women, and my daughter can never be a victim kadakai Daddy kawai yayi yamata shiru sai kawai yace lemme go it s time for Magrib yafice dakin yarage daura Mommy kadai da Ziora dake bacci hannu Mommy takai tana shafa gashin Ziora tana kallonta damuwa fal ranta tace Moses is the best Man for you, he s the best for you kinji EPISODE 4 Fitowa Aliyu yayi yashiga mota yana jiran Beeba daya gayama zai sauketa agida da kansa tafito tana murmushi sosai tashiga motan ya kunna yaja har gidansu yasauketa takama hannunsa tana murmushi tace thank you you ve made me so happy today gyadamata kai yayi yace gud night I need to head back home now gyadamai kai tayi tace agaida Mami tafice yaja motan yatafi Sauda ya tsaya yayi ishai sannan yatafi gida. Yana shiga a falo yaga Imam na hira da Mami yanashan pepper soup yace yauwa Yaya kadawo bari natafi gida gyadamai kai yayi yawuce sama yace lemme shower wanka yayi yasaka simple 3-quarter da tahirt yafito babu kowa a falon bazai kara fitaba hakan yasa yawuce yakulle kofa yatafi kitchen coffeee yahada tarike a hannu yafito yawuce dakin Mami yabude kofa yayi sallama Mami ta amsamai kasa kasa. Tana zaune bakin gado da hijab da Al Qur ani hannunta shiga yayi yamaida kofan yarufe shima yazauna bakin gadon yanashan tea yana sauraron kira an Mami harta gama tarufe tajawo drawer ta tamaida Al Qur anin tarufe takalli Aliyu dake kallonta yace gani Mami ajiyan zuciya ta sauke tace mahaifinka yakirani yau munyi magana na kusan 1hr dazu duka agaban Imam, yace yabaka takardun wasu gida ? Gyadamata kai yayi, tace mesa baka gayamin ba ? Ahankali yace sabida konayi abinda yakeso anan gidan zan zauna not that house, I will never leave you alone kizauna ke kadai Mami tai shiru tana kallonsa, anatse tace kanada wacce kakeso ne Aliyu? Dan sunnar dakai Aliyu yayi shi baisan mesa ba the way Imamu ke zama yama Mami hiran banza yana bata labarin this budurwa da that budurwa dayayi shi baitaba ba, Allah yadaura mai wani irin kunya da jin nauyin mahaifiyarsa when it comes to that angle, ganin yayi shiru yasa Mami tace answer me, yace yabaka one month koshi zai duba dangi yasamo maka wata Mami tadanyi shiru kafin a nutse tana kallonsa tace akwai wacce kake gani ne yanzu haka dakakeso ka aura? Yakai kusan minti daya bai magana ba sai chan murya chan kasa yace yes Mami ahankali Mami tace wacece Aliyu? Kaman maganan namai nauyi yace Habiba yayi shiru yakasa dago kansa kafin ahankali yace Dr Beeba Mami Mami tadade tana kallonsa kafin calmly tace kanason Dr Beeba ne Aliyu? Maisa Mami tamai tambayan nan? Shiru yayi kaman abu yarikemai baki Mami tace look at me Aliyu ahankali yadago kansa yakalli Mami, Mami tace kafadamin gaskiya, kanason Beeba? Sauke kansa kasa yayi yay shiru chan kaman dan karamin yaro yace ve been together tun Harvard more than 5yrs ago yayi shiru ko ansa wuka awuyansa bazai taba iya gayama Mami yataba ketama Beeba haddi ba, Mami knows danta tambaya daya tamai har yanzu bai iya yabata amsa da yes ko no ba, cikin muryan dazai nuna da gaske take tace Aliyu dago kansa Aliyu yayi yakalli Mami, Mami na kallonsa itama right in the eye tace bana sonka da Dr Beeba ko kadan! Dasauri Aliyu ya kalli Mami cus Mamin sa is one kind of mutum da babu wanda bataso tanada wani irin kyakkywan zuciya dake kaunar kowa so is soo unlike Mami tace batason mutum, anatse tace kwata kwata jinina bai aminta da Beeba ba