← Book details Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 99

Sashe 87

Kauna Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace Allah yabata lpy ahankali yace I know you will not want me to be doing any case a police station sabida status naka, but I m doing a case with wata Doctor, she s behind everything Aliyu yadanyi shiru Abba dakeda bala in lura yace wat are you not telling me and what? Ahankali yace she team up with Matarka to send that letter Dasauri Abba yace I will meet you now a head quarter din Ahankali Aliyu yace you don t have too Abba yace I have to ya katse wayan kusan da Abba dasu Aliyu duk atare suka isa police station din Abba da security nasa, awajen suka fara tsayawa Aliyu yanuna masa komi, from video yaron dayakai letter sannan suka shiga ciki still Beeba hauka take especially sanda su Aliyu ke shigowa tace Matar Babanka da danta Imam su suna ina? Ni kadai nai laifin? Ko jiya da daddare takirani sanda Babanka nan yaje yana tambayan Imam ko shine ya rubuta letter takirani tana cemini saura kashe uwarka suna ina su ? Yanda ran Abba ke baci yasa Aliyu yaje kawai yarubuta statement shima Chidi yarubuta nan da nan aka rubuta order na aikata cell kafin a wurgata kotu daganan sai gidan yari, police ta kwashe keyanta da mari tace muje cell doctor killer Aliyu ya kalli yanda aka jata kaman haka kawai yabar wajen abinsa suka fito sukabar police station zuwa parking space. Tsayawa Abba yayi gaban motan Aliyu sai yaji yanajin kunyan yaron ahankali yace me kakeso nama Imam da Maman sa? Lumshe idanu kawai Aliyu yayi yabude yace sai anjima Abba yabude mota yashiga abinsa yacema Chidi sutafi suka wuce. Mota Abba yashiga yazauna yayi shiru kawai kansa yahau ciwo yazauna yace kaini gida har anguwansu suka tafi hakanan yace yi parking awaje yanzu zan fito parking driver yayi yabude kofa da kansa yafito yashiga gidan yawuce direct yabude kofan falo ahankali babu kowa a falon yasan su Samha daman by now suna school wannan da baiga motan Imam ba yasan shima baya gidan. Staircase yawuce yayi sama yana tafiya ahankali tun kafin yakarasa kai karshen staircase yakejin muryan Mama tace ke wlh Malamin nan ya iya aiki tunda na burne layan nan a kar kashin filonsa inhar zan kawo bukatata saiya biyata ko ransa bayaso dabaki daya nace yasaki Munira yasaka, sau nawa yanaso yaje gaidata asibiti ko gida ina cewa a a yahanu, banmai magani awani fanni na rayuwa ba sai akan Munira dan bai tauyeni da komi ba, shikuma Imam dana Lura yanason yarinyar saina sa akamai jifan mahaukaciyar soyayya saisa kaman zai haukace sabida ita saikuma namai na jin magana kome nafadi shima sai yayi saisa ai nasami information na mahaifin Amrah bakinsa nifa yanzu duka bukatuna sun biya, dayane kawai yarage adda shine akashe matar nan dan duk karfin aikin Malam har yau har gobe mutumin nan na son Munira narasa dalili .. bugawa kirjin Abba yasomayi ahankali without making a sound yabude dakinsa ya shiga yana kallon hadonsa sai kawai yadauki pillow dinsa yashiga yagawa da reza dayake dashi ya shiga zazzage abubuwan pillow saiga laya tafado kasa yaduka yana kallo ahankali yace bismillah saiyasa hannu yadauka yawuce yashiga bayi yajefa yayi flushing hakanan jiyayi kaman an warware zuciyansa dawani igiya da aka daureta dashi gawani son Mami dayaji ya sauko aransa Ya kwabe babban rigan kansa yawuce yashiga dakin Imam anan ne Mama taji karan bude kofa dasauri ta katse wayan tabude kofa tafito taga kofan dakin Imam Abyde tace Imam Imam yaushe kadawo tayi wajen dakin Abba tagani tsaye yana zazzage pillows saiga laya tafado tawani zaro idanu dykawa yayi yasa hannu yadauka da bismillah yawuce yashiga bayi yayi flushing yafito yana kallon Mama itama tana kallonsa tace alhaji lafiya naga ranka abace ? Bai kukata ba yawuce dakinsa yazauna gaban wata table yadauki paper da pen yarubuta mata saki masu kyau har guda biyu sannan yataso yafito yakalleta ya jefar da takardan akasa gabanta na faduwa yace nasakeki saki biyu karna dawo na sameki gidana Mama tadaura hannu aka. Innalillahi wa innailaihi raji un, Alhaji me haka? Saki bayan na haifamaka zangada zangadan yara harda dan talatin da tashiga biyosa da gudu a bene kawai kafanta ya turgude haba sai ihu ko kallonta Abba baiyiba yafice abinsa tana kururuwa takasa motsi da kafafu kaman an manna gum awajen. Imam yashiga kira yace yadauko Samha da Amira a school yatura masa address dazasu samesa cikin 1hr saigasu Imam yar cikin gidan Abba na zaune dawasu Malaman addini guda biyu addu a aka muzu aka basu maganin karya sihiti gabaki dayansu dakuma azkar dazasu dingayi morning and evening Malaman suka tafi Abba ya kalli yaransa yace the reason nakira ku sabida inaso kuji daga bakina cewa na saki mahaifiyar ku sabida ta cutar dani daku Abba yayi shiru saiya fada musu komi dayaji tana fadi dakuma sa hannunta a zancen Aliyu yace bazan hanaku mu amala da mahaifiyarku ba amman gaskiya na hakura da ita, bansan ko zan iya yafe mata yanzu ba, darajan ku taci da wlh tabi Beeba cell itama Around 11 lokacin su Aliyu sun riga sun fita Mami takalli Mommy dake yanka mata fruits da kanta ahankali tace My Inlaw anatse Mommy ta dakata takalli Mami tace ahankali Mami tace dan Allah ki gayamin gaskiya meyafaru why is my daughter not here? The way I saw Aliyu yaudana tashi I know something is going on, banda haka the way nasan Amrah idanda tasan yau zan dawo the only reason dazaisa nadawo gidan nan ban ganta ba must be very serious? I know kuna ganin kaman banda lpy but wlh nafi kowa iya handling pressure, barina like this dakukayi shine ma ke hurting dina not sannin gaskiya ki gayamin abinda yafaru Bakaramin tausayin Mami Mommy taji ba hakan yasa ahankali tashiga sanar da Mami komi daya faru abunka da wacce ba yare ba har sex part din, anatse Mommy tace nasan Aliyu ba shine ya aiko letter ba but at the same time nima I support abinda Chidi yace abarmin ita koda 1 month ne nakoya mata zaman aure, na gwada mata menene miji, na koyarda ita dabaru da hikima na zaman gidan miji Ijiyan zuciya Mami tasauke ahankali tace da raina da lafiyana bazan taba bari Amrah tai wata daya ba gaskiya wlh ko sati daya bazan iya bari ba tunda na shigo gidan nan banjin dadin rayuwana sabida ban ganta ba Mami tai shiru tace ve always known Beeba is not a good person, she s behind the letter I m sure Saikuma Mami tace we can t force Amrah to grow up and start acting matured immediately, Muhammad is wrong dayace yara yan 15, 16 da Amrah ta girma na ma mazajen su biyayya abinda bai ganeba shina yara daban daban kowa da different upbringing nasa Amrah is just a different girl and she s perfect just the way she is, and my Aliyu is in love with her he can t survive without her for so long, ku bar min yarinya tadawo zasu shirya anan gabana and I will train Yarinyana dakaina I miss her so much wlh, Mommy kawai tayi murmushi tace naji me yarinya nasan yanzu ta tashi tana nemana, bari naje cus zanje church anjima Mami tace drive safe Mommy tace take your drugs eat and sleep don t stress I wil calm u anjima Mami tace to tana murmushi Wuraren 12:30 Mommy takai gida shima danta shiga kasuwa ta sayo wasu abubuwa na yare dasuka gyara mata dasu babu Yaren da basu da kayan mata wasu nasu a abinci ne da ganye, tana shiga gidan tawuce kitchen batasa masu aikinta ba wani green ganye kawai ta tafasa dake yauki sosai ta tacce ruwan tazuba a cup tahayo sama zaune taga Zuora idanunta sunyi ja anan palour sama tana kallon Mom dukta fice hayyacinta Mommy tace m just coming back daga wajen Mami she s home she s fine she is cancer free, Aliyu ma is fine sun fita da Chidi I have something to tell you, wipe your face first dasauri ta share fuskanta tass tana kallon Mommy, Mommy tace kinason Aliyu ko baki sonsa? Ahankali tace I love him alot Mommy Mommy tace then you will go back to his house but before then I need to teach you plenty things, I know u can cook but I want to make you the best cook sAbida the road to your husbands heart is through his tummy, then I need to teach you who is a married woman, her behavior the way she talks to her husband, then I want to teach you how to seduce your husband, and things to take that will make u very sweet so that Aliyu will be madly in love with you Kuka fa take da amman saitai wani murmushi ta gyadama Mommy kai, Mommy tabata cup tace anything I give u u must drink it ko bazaki koma ba dasauri takai baki kaman zatai amai amman haka ta Shanye tasss Mommy tace today topic is walking and talking Mommy tafara kiyamata abubuwa Ziora kawai kallon Mommy take paying attention cus she loves the topic, sai imagining yanda zatama Yaya Aliyunta haka take. EPISODE 9 Har gida Aliyu yasauke Chidi akofar gidansu, Chidi yakallesa cikeda tsokana yace baza a shigo aga Amarya ba Dr? Dasauri Aliyu yadauke kai yadanyi little smile dayasa yawani kara kyau, Chidi kawai kallonsa yake cus he sees Aliyu na son Ziora sosai da baijin zai wani iya fushi da itaba wlh, ahankali yace maybe nazo in the night ko muhadu gobe, take care just go home and relax gyadamai kai Aliyu yayi yana kallon gate din gidan kaman Amrah tafito yaganta koyadan ji sauki aransa amman yadauke kai yakunna motan yajuya saiya wuce anguwansu, horn yayi yashiga gidansu yayi parking yana kallon motan Imam dake compound dinsu, ahankali yasauko daga motan instead of yashiga flat na Mami saiya wuce flat nasa yabude yashiga yanabin ko ina da kallo yanajin wani kewan Ziora aransa yawuce sama yabude dakinsa, bedsheet din yaja ya tattara yakai washing machine yaciro sababbi ya shinfida ya gyara dakin tsaf yawuce nata dakin shima ya shinfida new bedsheet, yayi picking everything
Chapter 87 · 0% Book details