← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 113

Sashe 99

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalleta ya ce "Bari na kewayo dai, so nake mu yamutsa shimfidar can."
Ya yi nuni da gado.

Kunya ta kamata ta yi murmushi, ba tare da ta sake cewa komai ba.
Ya juya ya fita.

Hakan kuwa aka yi, domin bai wani jima ba ya dawo, hakanan duk yadda yake jin rashin kuzari, sai da ya zartar da kudirinsa. Duk yadda take ro'kon ya bari ya warware sosai, amma bai ji ba.

Sai fa'di yake "kewar ki na yi sosai, har addu'a nake na samu sauki na dawo gida, ba dan komaai ba, sai dan na kasance tare da ke".

Da'di ya matu'kar kamata, ta tabbatar tana da matsuguni a zuciyar mijinta. duk dai abin da Sa'adah ta yi mata a asibiti, yasa ta gane har gobe tana da karfi a zuciyarsa.

Yini guda bai fita ko ina ba, da aka yi azahar ya ci abinci, ya sha magani barci ya yi sosai.

Dan haka bai fita ba, sai a washagari, ya fita zuwa gidan Hajiya, fa'da da Jan kunnen da ta yi masa akan ya ri'ke Sa'a da girma ba ka'dan bane.

Fa'di take "ubanta mutum ne har da rabi, ka ji tsoron ubangiji ka ri'ke ta da Amana, na sha fa'da maka ba hankalin ku daya ba".
Ya amsa da zai kiyaye.

Daganan ya leka shagonsa, ya kuma gaida Baffah.

Baffah ya ce "wannan karon ma sadaki kawai zaka bata"

Da sauri ya ce "A a Baffah bar ni kawai na yi mata komai, gatan zai mini yawa, yanzu Ina da halin yin dukkan abin da ake yi, na gode sosai da karamci, Ina fatan kar Allah ya sa na sake kunyata ka Baffah".

"A a ni ba ka kunyata ni, bare ka nemi tsari da sake maimaitawa, ba komai tsakanin mu sai karramawa, domin tunda kaki fa'dar abin da ya hadaku, kuma kowa ya gane itace mai laifin, sai na gane kai din jarumine, adaline, mai kuma kaunata ne, Koda ha'kurin ka ya kwace amma ai hankalinka bai kwace ba, domin baka tozarta mini Iyah ta hanyar fa'din aibunta ba, dan haka Ni baka mini komai ba, sai alheri."

Ya zarce da cewa "a farko da zan baka ita, sai da na jaddada maka kar ka bari ta kangare maka, duk kuma wadda ka ga tana mu'amala da su, hankalinka bai kwanta da su ba, ka shata musu layi, Ina jin dai baka dauki wannan shawarar ba shiyasa kuka tsinci kanku a halin da kuke ciki, ba fa zan rufe ka ba, kaima kana bari soyayyarta na rinjayar ka a gurare da dama, a farkon rikicin banyi magana bane saboda yadda ka boye komai ka sata itama ta rufe komai"

Mk da ya san Baffah gaskiya ya fa'da sai ya sunkuyar da kansa kasa, ya kasa cewa komai.

Tsawon lokaci kafin Baffa ya sake cewa "Na horeka da yin adalci a gidanka, ka yi iyakacin bakin kokarinka, ka yi adalci, sai kuma ka barwa Allah ya taya ka. Domin a yanzu ma ina sake fa'da maka duk abin da bai maka a tare da Iyah ba, tun kafin ku yi nisa ka taka burgi akansa, su mata da ka gansu idan ba a kula da tarbiyar su ba, nan da nan zasu halaka kansu su halaka mazansu".

Jikin Mk ya yi sanyi, domin kuwa a kullum dabi'un Baffah na fahimtar da shi bai gama saninsa ba, har yau din nan bai ci karo da mutumin da ya fi mahaifin Sa'a karamci da fadar gaskiya ba, ko da kuwa gaskiyar akan kansa ne.

Mk da ya rasa mai zai ce sai kawai ya sunkuyar da kansa kasa ya ce "Madallah da zuciya irin taka, dama ka sha fa'da mini ba Sa'a ce ta hada mu ba, ba kuma zata zama dalilin rabuwarmu ba, tabbas na gasgata hakan".

Mk ya zarce da fa'din
" Alherinka yawa ne da shi Baffah! A duk lokacin da nake gabanka sai nake jina tamkar ina cikin shekaru irin na Jawad. Saboda zuciyata tana samun nutsuwa, domin tana tare da wadda yake girmamata, yake ganin kimarta. Kai ka'dai ne baka ga laifina akan kaddarar rabuwarmu ba, Kai ka'dai ne ka yi mini shaidar fin 'karfina al'amarin ya yi, haka kai ka'dai ne a duk tsayin wannan tafiyar bai juya mini baya. Haka nan yanzu kowa jan kunne yake mini akan na rike Sa'adah komai zata mini na yi hakuri, kar na ce komai.
Kai ka'dai ka ce na yiwa 'daya matar tawa adalci, kai ka'dai ne ka ce kar na yi hakuri da Sa'adah a inda zata kuskure ko ta sab'awa ka'ida.
A yau na sake ganewa kai din ba uban Sa'adah bane nawa ne"

Ya yi shiru saboda yadda yake jin rauni na shigar sa, ko mutane nawa ne irin Baffaha a Yau?

Ya tuna kwanakin baya yadda ya zaunar da shi yana fa'da masa tsananin son da yake yiwa Iyah! Amma a yau ya ture wannan soyayyar ya fa'di gaskiya, ayiwa Farida adalci, kar kuma ya bawa Sa'a damar da zata halaka, ta halaka shi.

Ya dago idansa da suka ka'da ya ce "Baffah kwanakin baya ka ce mini baka ta'ba mallakar abin da kake so kamar Iyah ba".

"Eh"
Baffah ya amsa a taikace .

Mk ya ce "Nima yau zan fa'da maka ban ta'ba son wata mace a duniya kamarta ba. Zan yi iyakacin kokarina na dauki shawararka na kar na bari ta halaka mu, Amma fa'da mini maganin rikicinta Baffah! Ita din sarka ce mai rikicin gan-gan".

Dariya ya yi ya ce "ai ba zata daina ba, Amma ina tabbatar maka zata rage da yawa daga cikin rikicin nata mussaman na dogon buri da kawaye yan karya domin ka shayar da ita mamaki. Abin da na san ba zata daina ba, shagwaba, saurin kuka, da kishi. Wannan kuma kaine zaka kiyaye motsuwar kishin, shagwaba da kuka kuwa idan ta yi ai sai ka rarrashi abarka".

Kunya ta kama Mk ya kasa cewa komai

Sosai ya yi godiya sannan ya mike yana cewa "Makaranta zan tafi".
Da sigar tsokana Baffa ya ce "Ba zaka leka ku yi tozali ba?"

Kunya ya ta sake kama Mk ya ce "Ai mun yi fa'da Baffah, ba zan nemeta ba, sai ta neme Ni".

Dariya sosai ya yi tare da cewa "Anya kuwa ka yi gaskiya Mutari? Amma dai ba ruwana".

Ko wayar Sa'adah bai nema ba, bare ya je gidan wurinta, ya wuce makaaranta.

Sa'adah ganin kwanaki biyu da sallamo Mk amma bai nemeta ba, ya sake hauhawar fishinta, yayin da shima fishin yake yi da ita mai tsanani, kawai ya samu salama ne na tabbacin zata dawo hannunsa, amma ganinta da ya yi da Khalil ba 'karamin haushin ta ya ji ba, kullum da aikinta yake kwana, yake tashi tunda shine sanadin da yasa take mua'amala da ahalin Khalil.

Kwanaki uku ya rage daurin aurensu amma babu fahimta a tsakanin su lamarin da yake ciwa Sa'a tuwo a kwarya, wani sashi na zuciyarta ya ce saboda yana da wata matar ne, wani sashen kuma ya kore wannan tunanin tare da tuno mata, tana budurwa ma haka ya dinga Wannan wula'kancin har ta yi zaton soyayyar ne bai iya ba.

A daren Mk na zaune a falon sama yayin da Farida ta yi filo da cinyarsa, yana wasa da dogon gashinta tamkar mai yin kitso, sai fama yake da bugun zuciya adalilin yana son fa'da mata, juma'a mai zuwa daurin aurensa da Sa'adatu.

Sau uku yana yun'kurin fa'da sai ya kasa, da 'kyar ya yi kundubalar cewa " My ferial tashi ki zauna magana zamu yi da nake bu'katar nutsuwar ki'.

Ta tashi da sauri kuwa, ta zauna sosai tana fuskantar sa.

Cikin karfin hali ya ce " Ranar juma'ah mai zuwa idan muna cikin rayayyu, za'a mayar da aurenmu da Sa'adah".

Wani irin tashin hankali ya ziyarci Farida, irin wadda bata ta'ba hasashen zata ji shiga ba, ta dinga yun'kurin bude baki ta yi magana amma hakan ya gagari Kundila.

Ta dinga karanto addu'a, amma duk da hakan sai da hawaye ya goce mata, wani irin tukuki ya mamaye zuciyarta, ta dinga jin tamkar ta mutu ta huta.

Da sauri ya janyota jikinsa ya rungume sosai, ya dinga fa'din sorry a hankali, wannan rarrashin ya sanya kukan ya kwace sosai, ta dinga yi, shikuma yana saka tissue yana goge mata. Ta jima a hakan, sannan ya ce "Ya isa haka, Yi shiru ki fada mini menene ya kidima ko haka".

Cikin kuka ta ce "Tsoro nake ji kar na rasaka, tsoro nake ji kar juya mini baya, tsoro nake ji kar ka kasa yin adalci ka halaka".

Cikin rarrashi sosai ya ce "Na ta'ba fa'da miki ba macen da zata sa na rabu da ke saboda ita, sai idan tamu ce ta hado mu, ba yadda za'ayi na juya miki baya Farida! Ina mamakin har yanzu da muka yi shekaru uku baki fahimci iri son da nake miki ba zai tan'kwabu bisa 'karamin dalili marar tushe ba.
Ba zan miki 'karya ba, da gaske an jarrabeni akan Sa'a! Amma ki taimake ni ki fa'da mini shin ina miki wani abu da kika kasa gamsuwa son da nake mata, ba zai hana na so ki ba"

Ta yi shiru tana ajiyar zuciya! Ta sani bai ta'ba mata wani abu da zata ce baya sonta, ko ya tauye ta ba, amma da ace zata iya da ta ce so take ya fi sonta akan Gogel, sai dai ba zata iya ba, shima kuma bata jin zai iya hakan, tunda ta san ubangiji ne yake cusa soyayya a zukatan bayi.

Ya sake rungumeta tsantsan ya ce "fa'da mini mana ke nake sauraro"

Ta girgiza kai ta ce "Babu"
Ya ce "Zan fa'da miki gaskiyar magana! Wallahi ina sonki, Ina tsananin sonki, hakuri da kawaicin ki ya 'kara miki 'kima a idona da zuciyata, kar ki bari kishi ya kwace miki wadannan halayyar, domin kina jan hankalina da su, ina jin kunyar bata miki. Sannan zan ro'ke ki arziki! Ki bani hadin kai ta yadda zan yi muku adalcin da zaki gamsu, idan na kuskure dan Allah ki mini uzziri wallahi ba zanyi abin da muzanta ki da gangan ba".

Ta saki ajiyar zuciya taare da cewa "To".
Chapter 99 · 0% Book details