← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 113

Sashe 63

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta zama very speach less, bugun zuciyar ta ya karu, wani irin zazzabi mai zafi ya fara kokarin kai mata caffa. ta koma ta kwanta a jikin kujerar tana jin duk wani tashin hankalin duniya yau ita aka ha'dawa shi.

Tsawon lokaci suna haka, shiru ya ratsa, sai fama suke da radadi a zukatan su.

Cikin 'karfin hali ya tayar da motar ya hau titi, karon farko da Sa'adah ta yi fatan inama su yi hatsarin da zai zama ajalinta, ta huta da azabar ciwon da ke damun zuciyar ta.

Bai tsaya ba, sai a kofar gidan su, gabanta ya yanke ya fadi, ta tuno maganganun Baffa a ranar da zai kaita dakin aurenta.

Ta kalle shi ta ce "Baffa korata zai yi, kar ka barni anan, mu tafi gidanmu Malam, na yi al'kawarin ba zan sake ri'ke kowacce irin waya ba".
Ta ru'ko hannunsa ta sake fa'din " Na amince ka yi amarya ka tafi da ita karatun da za ka tafi, Ni ka barni zan jiraka, fatana kar ka barni".

Magana ta ke yi ba kuka, sai tsananin bacin rai da tashin hankali.

Ya kalleta sosai "a karon farko da ya ganta cikin NADAMAR gaskiya, sai dai nadama marar amfani ta ke yi domin ta riga ta yi a 'kurarren lokaci.

Baice komai ba, ya bude motar ya fita, haka ta bude itama ta fita sanin akan titi suke, a zaure ya tsaya ya ciro wayarsa ya 'Kira layin Baffah, ya sanar masa ya zo yana zaure.

Cikin rashin sa'a ya ce "dazun nan na tafi Gogel, sai jibi kuwa zan dawo, ko akwai matsala ne?"

Kai tsaye Mk ya ce "akwai Baffa Amma zan zo na sameka anan din"

"Ba sai ka zo ba Mutari, in sha Allah zan juyo a yau ba sai gobe ba".

Ya yi godiya, sannan suka kashe wayar.

Sa'adah na rakube a jigin bango, ta matso ta tsugunna guiwa biyu ta ce " Rashin samun sa alamun ubangiji bai son rabuwarmu ne, Dan Nabiyur Rahamati ka dauke ni mu koma gida".

Ya kalleta sosai ya furzar da iskar bacin rai ya ce "wa ya siya miki Wannan Agogon da kuma waya?"

Hawaye ya balle mata, ta rasa mai za ta ce.

Ganin ta yi shiru ya sa shi cewa tashi ki shiga gidan zan je shago na jira dawowarsa.

Ya fita da sauri, ya yin da ita kuma ta durkushe a 'kasa tana kuka sosai.

Ta jima tana kukan da 'kyar ta tashi ta shiga gidan ta tarar da mahaifiyarta tana zaune tana Jin radio.

Tana layi ta 'karasa kan tabarma sabon kuka na kaico iri iri na sake ku'buce mata.

Tambayar duniya ba wadda Inna bata mata ba amma ta 'ki tankawa, lamarin da ya dagula hankalin ta.

Kan dole ta 'kira wayar Baffah ta sanar da shi ga Iyah ta zo tana ta kuka, kuma ta ce mijinta ne ya kawota da kansa.

Ya amsa mata da gashi nan ya juyo.

Ta ajiye wayar cikin sanyin jiki ta kalli yadda ta ke kuka jikinta har 'bari yake yi, ga wata irin rama ta yi, har ba'ki ta ga ta sake yi mata sosai.

A hankali ta;ce "kin tasa ni a gaba kina irin wannan kukan mai tayar da hankali, amma kin 'ki bu'de baki ki fa'da min mai ya same ki, ba Kya jin tsoron ciwo ya kada ni, kinsan fargaba da zullumin da nake ciki?"

****
Mk na zaune a shago, amma jinsa yake tamkar a cikin rijiya saboda tsananin yadda ya takura ga wani irin matsanancin kishi ya matse kofofin numfashinsa, ya sababa masa azabben ciwon kai mai tsananin. Yawun bakinsa ya kafe sai daci yake ji har makoshinsa! ya ciro wayarsa ya kira Mahmoud ya sanar da shi, yana cikin matsala ya zo gidan Hajiyan Bichi ya same shi.

Ya fito kai tsaye ya tari mai acaba(A lokacin ba a hana ba) ya kai shi gidansu, dan bashi da sukunin da zai iya tu'ki, domin al'amarin na nisa damuwar sa na 'kara girmama, wani abu ne mai tsananin ciwo ya tokare a 'kahon zuciyarsa mai azabtarwa.

Yana isa kai tsaye can cikin dakin Hajiya ya shige ya wuce ta a falo tana yanka kankana.

Mamaki ya kamata, ba zata iya tuna yaushe rabon da ya shigo ya ganta a falo amma ya zarce uwar daki ba.

Ta yi jim, tana sauraronsa ganin fitowarsa, amma abin mamaki mintina fiye da goma sun shude bai fito ba, dan haka sai ta mike ta bi bayansa dan jin ba'asin wannan sabuwar dabi'a.

Yanayin da ta tarar da shi ya tabbatar mata akwai matsala, da azama ta isa gareshi tana cewa lafiyar ka kuwa?

A hankali ya ce"kaina tamkar zai fashe Hajiya"

Da jimami ta ce "Ai da Abbas ko Akil ka kira wani ya raka ka asibiti, a kwanta da ciwo ne ba a sha magani ba?"
Dai dai lokacin Mahmoud ya iso suka gaisa da Hajiya da ta fito falo tana masa iso.

"Shiga! yau zuwa ya yi ya mini sake sake a gado da sunan ciwon kai".

Mahmoud na dariya ya mike yana cewa " Hajiya ai gara ya kwanta ya more da zarar kunga mun yi aure shikenan sai ku dora mana dukkan girma alhalin matu'kar kuna raye mu yara ne 'kananu".

Ya shige cikin dakin.

Kallon Aminin nasa ya yi ya tabbatar yana cikin tashin hankali babba. Yasan karfin zuciyar Mk duk abin da ya bayyana a jikinsa tabbas ya yi tsamari ne.

Da gaggawa ya shiga ya zauna a gefen gadon, ya na fadin "me ya ke faruwa ne?"

Cikin rawar murya Mk ya dinga yunkurin magana amma ya kasa yi, ga mamakin Mahmoud sai ganin kwalla na gangarowa ta gefen idon Mk.

Take hankalin Mahmoud ya yi tashin gauron zabi, murya kasa kasa cike da tsantsar aminci da kulawa, ya ru'ko hannuwansa ya ce "Yi hakuri Mukhtar! Fada mini damuwarka in sha Allah I will stand for you".

Da rawar murya Mk ya dinga ambaton Sa'adah, Sa'adah".

A hanzarce Mahmoud ya ce" me ya same ta, me ta yi?"

Da 'kyar ya bude baki ya ce "mun rabu, na saketa Mahmoud"! ya karasa da murya mai cike da tashin hankali.

Wani irin zabura Mahmoud ya yi ya mike yana cewa"How comes, akan me? subhanllah!"

Shiru ya ratsa dakin! kowa tunani, na katantanwa da shi.

A kasan makoshi Mk ya ce " ka
fa'dawa Hajiya, tashin hankali na yadda zan fa'da mata, da yadda za ta karbi lamarin".

Mahmoud ya zuba masa ido, yana kallon irin yadda Aminin nasa ke zu'ko numfashi da 'kyar tamkar mai fama da cutar asma.

A hankali ya koma ya zauna yana jin tashin hankali shima na ziyaryartar sa.

Tausayin Mk ya ratsa shi ya sake ru'ko hannuwansa a karo na biyu ya sassauta murya ya ce," Ina fatan sakin sunna ka yi, ina fatan mu gyara wannan matsalar kafin su Hajiya su ji, yanzu ina ita Sa'adah ta ke?"

Cike da rashin kuzari ainun ya ce "Na kaita gidansu, saki daya na yi mata, abin da nake so ka fahimta, da abin zai gyaru da ko kai ba zan raba 'bacin ran da kai ba".

A hankali Mahmoud ya muskuta ya ce "Kar ka yi haka, ka yi hakuri mana, da wanne irin ido za ka kalli dattijon arziki irin Baffah?"

Wannan karon Mk ne ya tamke hannun Mahmoud ya zarce da cewa "shine babban tashin hankali na, fiye ma da yadda nake jin fargabar da Hajiya za ta shiga, amma kuma bana jin zan iya cigaba da zaman mu tare, iya adadin zaman da 'kaddara ta hukunta za mu yi kenan, ka fa'dawa Hajiya sai muje ka raka ni wurin Baffah, duk da bana jin dadin jikina".

Ya fada a sanyaye cike da yankewar Buri.

"Mukhtar Nima ba zan iya fa'da mata ba, da wanne baki zan fadi wannan 'bakin labarin?"

"Cike da rauni ya ce " daurewa za ka yi Mahmoud".

Shiru ta ratsa dakin a karo na biyu, nazari soasai Mahmoud ya ke, yana tunanin wacce irin 'kaddara ce mai zafi ta raba Mk da Matar da ya shaida yafi sonta akan kansa?

Yana son jin menene ummul aba'isin wannan matsalar, amma kuma tunda Mk bai bu'da masa ba, shikuma ya yi al'kawarin ba zai tambayi komai ba, zai kuma yi dukkan mai yiyuwa dan ya sulhunta tsakanin su.

A dabarance Mahmoud ya 'daga murya ya ce "Sam bazan iya fadawa Hajiya wannan tashin hankalin ba, kai da ka yi, kaine mai fa'da ba Ni ba".

Ai kuwa wannan kalamin na Mahmoud ya janyo hankali Hajiya, da azama ta fa'da 'dakin tana fadin " menene ba za ka iya fada mini ba Mahmoud! wanne tashin hankalin ya rakito?"

Dukkansu suka yi shiru aka rasa mai bakin magana, ta zauna da'bas a 'kasa tana salati, da fatan ba wani rashin gaskiya Mk ya aikata ba.

Ganin irin damuwar da ta shiga yasa Mahmoud yin 'kundunbalar fadin "Hajiya ki yafe mu, ina ba'kin cikin sanar da ke yau Allah ya 'karar da zamansa da Sa'adatu".

Salati mai 'karfi Hajiya ta rafka, tana cewa "Kar ka jinginawa Allah'karar zamansu, jingina masa, dama ya da'de yana fatan rabuwar, ganin ya kasa samun damar shine yanzu ya murde zaman da 'karfin tsiya."

"Oh ni Rabi'atu ina ganin tasku, da wanne 'bakin ciki zan ji? da wadda yan'uwanka suke guma mini, ko da naka? Alhaji da Hajiya Babba sun mutu sun barni da ku, kuna neman kashe ni da ba'kin ciki".
Ta fara hawaye, tana gogewa da hannun zaninta .

Da ga Mk har Mahmoud sun yi laushi tubus da jin kukan Hajiya, hankalin su kuma ya sake tashi matu'ka, da rawar murya Mk ya ce "Na roke ki, ki daina zubar da hawayen nan dafi ne a rayuwa ta, da kinsan azabar da nake 'dan'dana na tabbatar da sai kin sassauta mini, ki yi hakuri Hajiya ba yadda zan yi ne, abin ne ya fi karfina, ki mana addua ki kuma yafe mini".

"Yanzu ina Sa'a din ta ke?"

Mahmoud ya ce "tana gidansu, yanzu ma komawa zamu yi dan bamu sami Baffan ba".
Chapter 63 · 0% Book details