← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 113

Sashe 68

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce "matu'kar muna tare kin san ba zan iya wannan jarumtar ba".

Ya sassauta ya ce "ki dinga addu'a sannan ki bar komai a hannun Ubangiji. Abin da nake so ki fahimta, wallahi na fiki shiga damuwa da tasku, kawai ni jarumta na fiki saboda kasancewata Namiji! Sannan ba zan ta'ba sauya hukuncin da na yi mana ba, har sai kin fa'da mini gaskiya koda hakan na nufin rushewar farin-ciki na gaba'daya, duk lokacin da kika shirya fa'da mini gaskiyar magana, ki mini magana".
Da haka ya kashe wayar gaba'daya.

Ta yi sororo da waya a kunnen ta, tana kallon agogo da ya nuna uku da rabi da minti biyu.
'
Har aka fara 'kiraye 'kirayen sallah barci bai iya surarta ba, tana ta tufka da warwara, ta yaya zata iya fa'da masa Khalil ne ya bata wadannan kayan? To akan wanne dalilin zai mata kyautar su ta karba? zuciyarta ta shiga harbawa, bare da ta tuno waccan kato'barar maganar da ta yi.

Ta yi amanna har da wancan laifin ya sake girmama wannan laifin a zuciyar Mk, sai ta yi kamar ta fa'da masa gaskiya sai ta tsorata, a yadda tasan ya tsani Khalil zai iya 'kararsa ko dan ya ci mutuncin gidansu tunda mahaifin Khalil fittacen 'dan siyasa ne, ita kuma ta hadu da zubewar mutunci a idon dangi dama duniya gaba'daya tunda tasan suna chatting da shi, ha'kika Sa'a na cikin hali irin na canka ca kare.

A fili ta dinga fa'din "Allah na tuba! na cuci kaina, son zuciya ya janyo mini 'bacin rai da damalmalewar lamura! Na keta alfarmar shari'a shiyasa na ke 'dan'danar 'bacin rai mai azabtarwa".

Tamkar mahaukaciya take surutai, tana sake cewa "Na yi al'kawari idan har na koma 'dakina bazan sake yin wani abu na rashin gaskiya ta kowacce fuska ba, sai da nace wa su Halima ina jin tsoron abin da zai biyo baya ta mini ingiza mai kantu, na biyewa 'kawar zuciyata na gasgata su, waiyo waiyo! Lah ilah ha illah anta subhanaka inni kuntu minan zalimin".

Duk akan kunnen Inna take wannan koke koken, da suratai duk da bata fahimci me take fa'da ba, da farko tsorata ta yi, ta 'dauka gwaiguna ne, sai daga baya ta fahimci daga 'dakin Iyah ne, a hankali ta fito, kasancewar Baffah yana Gogel.
Har ta isa bakin 'kofar dakin, sai kuma ta fasa, ta juya a zuciyar ta kuma tausayin'diyarta ya fara kamata, ta dinga mata addu'ar samun sassauci a zuciya.

Haka kwanaki suke ta shudewa, fargabar Sa'a na sake girmama, ba ta sake tuntunbar Mk ba, sai ana gobe za ta kammala iddarta, duk yadda ta kada billenta ta dinga ro'kon kar ya bari ta fita a matarsa bai ji ba, ya nan akan bakansa sai ta fadi gaskiyar lamari.

Washagari ta tashi da zazzabi ga kuka ya ki yanke mata. Inna ta kasa jurewa yanayin da ta ganta a ciki, har 'dakinta ta shiga ta zauna kusa da ita, ta ta'ba jikinta.
Zafi zau ta ji, ruwa ta samo da tawul ta dinga goge mata jiki. ta taimaka mata ta canja Riga, ta zubo mata kunu a kofi ta matsa mata ta shanye, sai dai tana gama shan ta amayar da shi tas.

Haka Inna ta sake gyara mata jiki, da kuma wurin, tana fatan inama ace ciki ne da ita wata'kila hakan yasa mijinta ya mayar da ita.

Baffah da bai fita ba, shi ya nemo Usaini mai chemist ya duba ta, ya kawo mata magungunan da zata Sha.

Tafi kwana uku tana mukurkususu, kafin ta fara warewa, saboda yanzu Inna ta sassauta mata, damuwar ta dan yi sauki.

Sati biyu da kammala Iddarta, tana tsakar gida tana wankin kayansu dana Inna sai ganin Jawad suka yi ya shigo a guje kamar yadda ya Saba.

Kai tsaye ya nufi uwarsa ya rungume ta, ita kuma idon Inna ya hana ta rungume shi, sai ta bige da fa'din wa ya kawo ka?

Yana jikinta yace " Malam ne, kullum sai na yi kukan gurin ki zan zo shine yau Hajiyar Bichi tace sai ya kawo ni, tunda jiya anyi hutun boko".

Inna da ta ke zaune tana fere doya tace "wato Jawad ba ka ganni ba ko, Anya kuwa za ka yi al'kawari?"

Kafin ya yi magana sallamar Hajiyar Bichi ta cika kunnuwansu tare suka shigo da Baffa, Inna ta mike da azama tana fa'din lale da Hajiyar Jawad, ashe tare ku ke tafe?"

Falo suka shiga! Inna ta gabatar mata da ruwa ta zauna Don gaisawa, sai taga Hajiyan na share hawaye Baffa na cewa "to ya za'a yi, sai ha'kuri, komai rubutacce ne, idan rabo bai 'kare ba za su koma, idan kuma ya 'kare sai duk mu yi ha'kuri, mu bisu da addu'ar fatan alheri! fatana dai ki cire damuwa a ranki.
Wallahi bamu 'kullace ku ba, Ni ko Mutari har yau ban ga laifinsa ba, Allah shine shaidata, kawai dai zan so ace sun shirya kansu ko dan rayuwar 'dansu ta inganta".

Murya a dakushe Hajiyar ta ce " Nima abin da nake ta hango musu kenan ban da dole yaushe za'a raba yaro da uwarsa! kome za'a masa ba zai gamsu ba idan ba uwarsa yake gani ba. Haka nan ba kowacce mace bace zata ri'ke'dan da ba nata cikin adalci da kyautatawa ba, akwai su amma sun yi 'karanci 'kwarai da gaske".

"Allah ya musu za'bi mafi alheri" Baffa ya fa'da yana barin falon.
Hajiya da Innah suka ha'da baki wurin cewa " AMEEN".

sannan suka shiga gaisawa tare da jajanta 'kaddarar da ta fa'dowa yaran su. Jikin Hajiya a sanyaye yake sosai, tunda abin nan ya faru take son zuwa, amma kunya da nauyi sun hanata, sai yau ta yi shahadar zuwa, ha'kuri ta bayar yafi cikin kwando, karbar da ta samu daga iyayen Sa'a yasa ta sake jin nauyinsu ainun, karamci a jininsu yake, tabbas Mukhtar ya yi asarar irin zuri'a me yakana da alheri.

Ganin Baffah ya fita ya Sanya Sa'a dauko Hijabinta ta saka ta shiga falo Jawad na binta tamkar jela.

Daga gefe ta tsugunna, ta gaida Hajiya kanta a 'kasa.

Hajiya ta hau fa'din taho ki zauna kusa da ni Sa'a.

Da rarrafe ta karasa kusa da Hajiyan, amma kanta a 'kasa tana Jin kunyar Hajiya na kamata irin wadda bata ta'ba ji ba.

Sosai Hajiya ke kallon yadda ta lalace ta yi ba'ki sosai, 'kwalla ta cika idonta a sanyaye ta ru'ko ta jkinta, hawaye ya gocewa Sa'a ba tare da ta shirya ba, tana yiwa kanta jajen rashin suruka irin Hajiya! Ta tabbatar samun uwar miji irinta a Yau zai yi matu'kar wahala.

Itama Hajiyar kukan take yi, tausayin Sa'a da Mukhtar da tilon dansu na matu'kar sa ta zubar da hawaye. Wacce irin ba'kar 'kaddara ce ta afka musu haka?

Mussaman yanzu da taga irin bibiyar da Jawad ke yi wa uwarsa, duk inda tasa 'kafa nan yake mayarwa, duk irin gatan da take masa, duk yadda ubansa yake masa siye-siyen kayan wasa da na ciye-ciye kala kala, bai hana ya yi kukan neman uwarsa ba, yanzu da ya ganta kuma ita ka'dai yake bibiya duk kuwa da yasan ubansa na 'kofar gida a zaune.

Duk dabarar Hajiya dan Sa'a ta fa'di musabbabin rabuwar ta su ta 'ki!kuka kawai ta ke yi mai tada hankali, Jawad kuma na ta goge mata kamar yadda ya saba yi mata idan tana kuka.

Tausayinta ya sake cika zuciyar Hajiya, ta dinga rarrashinta da kalmomi masu da'di.

Da zasu tafi Hajiya ta kalli Jawad taga ya ri'ke Sa'a sosai, sai ta yi nufin tsokanar sa ta ce "to zo mu tafi Jawad".

Ai kuwa nan da nan yasa kuka yana nuna dukkan yatsun hannuwansa yana cewa "Malam fa ya ce kwana haka zan yi?"

Hajiya ta yi gaba tana cewa "yi shiru da bakinka wasa nake maka".

Har zaure ta yi wa Hajiya rakiya, Mk na bakin kofar gidan a jingine yana waya, take zuciya ta ayyana wa Sa'adah da Farida yake waya a kofar gidansu.

Hawaye ya sake kwace mata, Hajiya da ta zaci ganinsa yasa ta kuka ta hauta da fa'da sosai tana cewa "wanne irin sakarci ne wannan Sa'a? Kina bada ni, banda bayar da kai menene ba zaki warware ki saki ranki ba, kina kallon kanki a madubi kina ganin irin lalacewar da kika yi?"

Ita dai Sa'a kuka kawai take yi 'kasa 'kasa, Hajiya ta nisa ta cigaba da cewa "ki kwantar da hankalin ki, kin ji!komai zai wuce kamar ba ayi ba, so nake nan da wata daya na ga kin dawo Sa'adatun nan mai birge yara da manya, Allah ya shiga lamarin ki, ya baki miji nagari, da zai wanke miki dukkan ba'kin cikin da kika kwankwa'da".

Wani irin kishi da Mk bai yi zaton zai sake ji akan Sa'adah ba, ya kama shi, takaici yasa shi barin bakin 'kofar ya nufi mota ya shiga yana ta a'uziya, saboda yadda ya ji takaicin Hajiya ya kama shi matu'ka da gaske.

Yana tuki amma zuciyarsa tamkar ta fashe, a gabansa Hajiya ke wannan fatan. ita kuma da ta lura da yadda yake ta 'dacin rai, tunda ta shigo motar ta gane kishi ne ya turnike shi, dan ayiwa matar da ya saka, ya ki mayar da ita fatan samun wani mijin.

Ta dinga kallon yadda ya fusata tamkar kububuwa, Hajiya ta tsinci kanta da mamakin kishin maza, ka saki mace, kace ba za ka dawo da ita ba. Sannan baka son kowa ya aureta alhalin tana cikin shekarun da take bu'katar auren.

Itama haushinsa ya kamata da ya kasance cikin masu son kansu, sannan har ita zai yi wa wannan fishin?.

Dan haka Yana shan kwanar layin 'Dan Hassan da shine layinsu amma a ciki suke sosai, sai an hau abin hawa.

Murya a dake ta ce samu wuri ka tsaya! Bai yi musu ba, ya gangara ya yi parking.

Ba jinkiri Hajiya ta fito cikin sa'a kuwa ta tsayar da dan adaidaita da zai shiga ciki, ba 'bata lokaci ta shiga suka tafi.

Ba'kin ciki ya sake kama Mk idonsa ya yi jawur, ji yake tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu, Hajiya da Sa'a su huta da ganinsa.
Chapter 68 · 0% Book details