← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 113

Sashe 33

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahmoud ne ya hado wa Sa'adah kayan shan ruwa da kayan sallah masu tsada har set biyar da takalmi da jaka set uku sai tarkacen kayan kwalliya da turaruka. Tare suka kawo mata, da za su tafi kuma ya sake ba da kudin 'dinki wanda ta 'ki karba sai da MK yasa ba ki sannan ta karba.
Yawan kayan da kuma tsadarsu ya dan rage mata damuwar rashin lefe musamman idan ta tuna tana da kayan wurin Alh Mamman a ajiye.

Ana yin sallah da sati 'daya iyaye da 'yan'uwan MK suka hada kudadensu, aka sayo dukkan abin da za a bukata, tun daga kan gado da kujeru masu kyau da aminci suka sayo aka shirya gida ya fito sosai, labulaye da carpet suka ajiye sai satin biki za a zo a saka.

MK da ya je ya ga irin kayan da aka zuba masa sai da ya yi hawayen farinciki, ya duba ya ga an 'kawata dakin Sa'adah da dan'kareren gadon da duk fariyarta ba za ta raina ba, ga kujerun ma masu kyau, ba irin gama gari ba, dayan dakin ne kawai aka malale shi da carpet aka bar shi empty, bai sha mamaki ba sai da ya shiga dakin dake tsakar gida wanda shi ne mallakinsa, an saka masa gado amma bai kai na dakin amarya ba, kowanne gado kuma da dimemiyar katifar Vitafoam a kai.

Ya zauna a bakin gadon yana goge idonsa, yana mai yin addu'a ga dukkan ahalinsa, sun masa zumunci ba ka'dan ba.

Ya zauna yana ganin TV da Fridge kawai ya rage wanda su kuma yayarsa Hafsatu ta ce ta aiko da su. Isowa ne ba su yi ba tunda a Lagos take.

Alhaji Isa shi ya sake komawa wurin Baffa ya ce idan ba damuwa suna son a yi auren a cikin sati biyu masu zuwa.

"Yadda ka ce ba ka bu'katar komai a gurinmu sai sadaki, mu ma muna ro'kon ka!Yarinyar kawai muke so don Allah!"

Suka rabu cikin walwala, tare da addu'ar albarkar Ubangiji a cikin auren.

Duk da Baffa ya ce ba zai mata kayan 'daki ba, kan dole ya karbi tsalelen gadon da mijin Sumayya ya aiko masa. Sumayya na zuwa ta nunawa Inna ku'din da za ta kashewa Iya, ita ma ta fito da nata ajiyar ta hada suka shiga kasuwa tare da Sa'adah, suka zabo kayan kicin na garari duk a 'ko'karinsu na kwantar mata da hankali, tunda sun san halinta na son kayan 'kawa.

Hatta kayan fitar biki masu kyau aka tanadar mata shike nan sai hankalinta ya kwanta. musamman da Sumayya ta ha'kur'kurtar da Baffa ya yarda za a kai mata gadonta 'kirar Dubai.

Kafin ranar 'daurin aure gidan amarya ya fito fes komai ya ji, Sumayya ta yaba 'kwarai da kokarin MK da iyayensa, saboda haka sai ta sa aka mayar da gadon dake dakin MK zuwa dakin dake cikin falon wanda babu komai a ciki, shi kuma aka saka masa hadadden gadon Dubai.

Kicin aka sake 'kawata shi da tsirarrun kayan alfarma, aka rufe gidan ana jiran isowar TV da Fridge da kuma amarya! don Mk tuni ya tare a cewarsa gadi yake yi.😁

*05/06*

Ranar aka daura auren Mukhtar Kabir Bichi da Sa'adatu Bashir Gogel, a Masallacin Sahaba dake Kundila, kamar yadda Baffa ya ce ba za a yi party ko ka'de-ka'de ba hakan ce ta kasance.

Amma kuma ya tsaya an yi abincin 'daurin aure da yini na fitar kunya, duk wanda ya halarcin auren Sa'adah mace ko namiji ya ci abinci mai rai da lafiya don kuwa Bijimin sa Baffa ya yanka, duk tanadin Baffa a shirya abincin fita kunya ya kare. A lokacin sarkar gold din dubu hamsin babba ce, ita ya siyawa amarya da shawarar Sumayya da take ta 'koda irin kokarin da MK da iyayensa suka yi. Sai kuma 'dinkunan da ya mata na kwalliyar amarci.

A Daren da aka daura aure suna zaune a gabansa ita da Sumayya da mahaifiyarsu, bayan ya yi addu'a ya ce, "Duk wani burina a yau ya cika Iyah, ina kyauta zaton na dan'ka ki a hannu na gari don Allah ki bi mijinki, nasan kinsan idan mijinki, ya yarda da ke to Ubangijinki ma ya yarda da ke, idan kika ri'ke wannan kadai za ki gane komai za ki yi a 'dakin mijinki ibada ne.
Ibada kuwa sai an daure domin za ka ci karo da abin da kake so da wanda ba ka so. Na ro'ki ki yi koyi da yar uwarki wurin boye sirrin aurenta, har yau din nan Sumayya ba ta taba fa'din ga laifin mijinta ba, mun sani ba fa don ba ya mata laifin ba ne, haka shi ma yana ri'ke da ita cikin ha'kuri da girmamawa. Ina sake miki nasiha ki zama mai ha'kuri, baki da'yan aure wallahi hakuri ne ya fi yawa, ina fatan ki yi ko yi da mahaifiyarki wurin ha'kuri da biyayyar aure!"

Ya janyo ledar dake gabansa ya fito da sallaya da kur'ani ya mi'ka mata, ta miko dukkan hannunta biyu da suka sha adon lalle ta kar'ba, yace "Ki rike ibada da kyau ita ce za ta jagorance ki duniya da lahira."
Ya kalli Sumayya yana fadin "Ina abin da nace ki ajiye?"

Da sauri ta mi'ka masa dama ta shigo da shi ya karba ya sake mika wa Sa'adah yana fadin, "Ki rike tsabta da kwalliya da ma ba na jin ki a wannan bangaren. Inda nake da shakku akan biyu ne. ki 'karanta buri Iyah kin dai san ni ubanki ba kowa ba ne, ki yi alfahari da abin da yake hannunki, ki daina sha'awar wanda suka fi ki ko kuma wanda ba tsarin tarbiyarku daya ba, a yanzu da za ki koma 'karkashin mijinki, ina hada ki da Allah kar ki dinga dora masa hidimar da ba zai iya ba, ko ba ra'ayinsa bane. Da ace za ki rabu da harkar kawaye to ina tabbatar miki za ki 'karantawa kan ki buri saboda ba kya hangensu. A karshen karshe na yafe miki dukkan kurakuran da kika mini, ina fatan Allah Ya lullube rayuwarki da albarkaSa, ya ba ki zuri'a mai albarka, ya kuma hore miki ha'kurin zaman aure."

Daki ya yi shiru sai shesshekar kukan Sa'adah, Baffa ya nemi Inna ta ce wani abu, ta girgiza kai tare da cewa, "Duk abin da zan fada na dade ina mata bita indai mai ji ce ai ta haddace su. Fatana Allah Ya albarka ci aurenta."

Cikin soyayya mai yawa Baffa ya kalli Sumayya ya ce, "Saura ke babbar yaya uwa ta biyu!" Ta yi murmushi cikin sanyin murya ta ce, "Komai kun fada Baffa, fatana a ce duk ta ji ku da kunnen basira, ta kuma ri'ke 'yan'uwansa da girma, musamman iyayensa. Ki rike su da mutuntawa komai za su miki kar ki nuna kin ji haushi ki yi hakuri, ki sake ninka kulawarki a kansu, duk kuma wanda ya je gidan, ki karbe shi da sakakkiyar fuska su ji tamkar a gidan yar'uwarsu mace su ke saboda sakewa da walwala."

Baffah ya nisa yace " idan Kika bi maganganun mu kin tsira! Idan kuwa kika je kika biyewa 'kawayen banza da son zuciya ki tabbatar ke 'kadai za ki dauki 'bacin ran da zai same ki, ki bi mijinki ko zaluntarki yake yi ki bishi da addu'a idan abin ya gagara, sai mu shiga, amma idan ke Kika bijire to fa kisani baki da wurin zama a gidannan".

Ya rufe zaman da doguwar addu'a ya kuma rike ta a hannunsa ya tafi kai ta 'dakinta da kansa a motar Alhaji Isa da ya zo daukar Amarya.

'Yan'uwan Baffa da na Inna da suka zo, sai mamakinsa suke yi da ya hana su zuwa kai amarya, ya tafi da kansa ya kai 'yarsa dakinta.

A lokacin kam ya zo da sabuwar dabi'ar da ta sha banban da al'ada, ashe shi yasa yasa aka kai su suka ga gidan amarya tun jiya?

*SURAYYA DAHIRU*.
✍️✍️

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*

*TUKUICI GA*
_*AISHA IBRAHIM BAFARAWA*_
(*BEAUTY*)
*MK DA SA'ADAH NA GAISUWA*
👍

49-50.

*GIDAN AMARYA*

A gidan su Baffa suka tarar da su Baba Umaru da Baba Idi da kuma MK. Tunda Baffa ya fa'da musu a wurin 'daurin aure cewar shi zai kai amarya 'dakinta kar a turo mata, sai suka fasa komawa Bichi a yau, suka ce su za su karbi amarya da kansu.

Haka Baba Umaru ya tisa MK da jan kunne iri-iri akan ya ji tsoron Allah ya ri'ke matarsa cikin tausayi da adalci, komai za ta yi ya dauke kai ya fahimtar da ita cikin ruwan sanyi.

Baba Idi ya nisa ya ce, "Sannan zan fa'da maka gida naka ne, amma kayan ciki na matarka ne, kana dai ganin irin mutunci da karamcin da aka maka, to ina ro'konka! ka nuna kai ma ka san mutunci ta hanyar zama da yarinyar nan da kyautatawa, ba hankalinku 'daya ba, mata lamarinsu yana da gigitarwa.
Amma idan aka yi ha'kuri da su, aka musu afuwa sai a ji dadin zama da su, saboda masu rauni ne, kuma masu tausayi ne".

Alh Isa kuwa cewa ya yi, "Abin da zan fada muku ni ne uban Mukhtar, ni ne uban Sa'adatu, sannan ni ne alkalinku dukkanku 'daya kuke a gurina. Ba zan saurara wa duk wadda ba shi da gaskiya ba".

Ya kalli Sa'adah da take gurfane a lullu'be cikin lafaya, "Sa'adatu duk da ba na fatan matsala, amma duk abin da ya taso na rashin jin dadi, ni ne Babanki, ni za ki fadawa kar ki ji nauyi ko kunya, waya kawai za ki mini, ni kuma zan miki maganin ko mene ne, domin duk girman Mukhtar yaro ne karami a idonmu, na san kuma mun isa da shi".
Chapter 33 · 0% Book details