Sashe 44
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MK ganin ba irin ha'kuri da rarrashi da bai yi mata ba, yasa ya zuba mata ido, shi yake yin komai na gidan har girki, ya ki yarda ya biye mata, ya tabbatar tana cikin halin da za a tausaya mata, duk da abin nata har da rashin mutunci, amma da zarar ya tuna abubuwanta na alheri sai ya mata uziri, babban abin da ya dame shi, rashin shayar da Jawad musamman da yake ana ba shi supplement na yara mai sa su kuzari da saurin girma, akai-akai yake jin yunwa, don ma yana shan madara da fricso cream.
Washegari da yamma ya dawo da ga wurin aiki tun daga waje yake jin kukan Jawad, a sukwane ya shigo cikin gidan, ya tarar da ita, tana zaune a falo tana ganin sa, amma ba ta dauke shi ba.
Bai taba jin haushin ta irin na yau ba, ya jima yana tsaye ya zuba mata ido, yana kallon ta, yana jin tamkar ya rufe ta da duka.
Kwafa ya yi, ya dauki yaron ya hada masa abincinsa, ya ba shi ruwa sannan ya kwantar da shi, yana ta shure-shuren 'kafa, tamkar ba shi ne mai kukan nan ba, da ma shi ba mai fitina ba ne, indai ka ji kukansa to dayan biyu ne, ko yunwa ko rashin lafiya, tunda ya yi kuka kafin su yi arbain shike nan ya daina kukan banza.
Wanka ya yi, ya fito ya zauna a falo, ya dube ta ya ce "Na gaji fa da abubuwan da kike mini, na yi iya hakurin da zan iya, na ga abin naki babu mutunci ko kadan".
Kai tsaye ta ce "Da ma ai so nake ka gajin, matu'kar kana son zaman lafiya, sai dai ka zabi daya cikin biyu, ko dai a yaye Jawad gaba'daya, ko a cire cikin nan".
Ransa ya yi matu'kar baci ya kalle ta ya ce "Ni ban san inda ake cire ciki ba, ke da kika sani sai ki je, ai don kin ga na damu da ke shivyasa kike mini wannan iyashegen, mafi yawa idan mace ta samu ciki da wuri irin haka, daga wurin mijin take fuskantar kalubale, amma ke don samun guri ni kike yiwa wulakanci".
Ya nisa sannan ya ce "Ba zan kai kararki ba, amma daga yau ba zan sake rarrashin ki akan wannan matsalar ba, idan kin ga dama ki bar cikin nan, idan kin ga hagu ki zubar a rariya, Jawad kuma In sha Allah yau an yaye shi, Ubangiji zai raya mini shi, ina ce idan mutuwa kika yi ma ba zai fasa rayuwa ba?"
Daga haka bai kara cewa komai ba, ya tashi ya shiga kicin ya hada cornflakes ya shige dakinsa, bai dawo falon ba, yana kudire ba zai sake dafa abinci ba.
Bai wani jima ba ya shigo, ya tashi Jawad ya canja masa riga, ya samo leda mai kyau ya zuba tarkacen da Jawad zai bu'kata, ya nade shi a shawul, ya saba shi a kafada ya fice, ba tare da ya kalli gefen da takep a zaune ba, bare ya yi mata sallama.
Kawai sai ta ji kuka ya zo mata, bakin cikinta daya yadda bai dafa musu abinci ba, kuma yunwa take ji, ta kalli agogo biyar da kwata 5:15pm, kan dole ta shiga kicin din ta hada tea ta dauko biscuit din super2 ta hau ci.
Gidan Samira da yake Dan'agundi ya tsaya ya ba wa yaro ya kai mata Jawad, sai da ya kira ta a waya ya tabbatar ta karbe shi, sannan ya tari Adaidaita ya wuce shagon askinsa, yana tafe yana tunani biyu, na yadda zai bullo wa Sa'adah, da na sayan motar da yake shirin yi.
Tana zaune har taran dare ba MK ba Jawad, hankalinta ya tashi, ga wata muguwar yunwa na addabar ta, ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji dadi, kewar Jawad ta addabe ta.
Sai goma saura ya dawo, a dakinsa ya ci burki, ya kwantar da Jawad da yake ta barci, tunda Samira ta masa wanka ya yi barci. Sai da ya gama komai tunda ga wanka, har shafa'i da wutiri, ya nufi gurin Sa'adah, tana zaune a falo ta rasa me yake damunta.
Sallama ya yi bai jira amsawarta ba, ya shige daya dakin inda nan kayan Jawad suke, akwati babba ya dauko, ya hau zuba sabbin rigunansa da ba a kai ga bude su ba, sannan ya zuba na cikin drower kayansa, hatta bargonsa sai da ya saka cikin akwatin, da kyar ya zuge sannan, ya kashe fitilar, ya ja akwatin zuwa dakinsa, da ido ta bi shi, tana sake jin tashin hankali na kamata.
Dakin ta shiga, ta hau dubawa, ta tarar ba kayan Jawad sai tsirarru wadda suka fara yi masa kadan, sai dryar shanya.
Kuka ya kwace mata, tana raya duk bala'i, ba inda za'a kai mata yaronta.
Tana fitowa shi kuma ya shigo, ya zauna a kujera ya ce "Zo ki zauna, magana za mu yi."
Ba ta ki ba, ta zauna din, yana kallon yadda ta lalace tsabar fitinar da sanya a ranta.
"Gobe zan yi Asubanci zuwa Lagos, jirgin karfe shida zan shiga, kafin sallar Asuba Mahmoud zai zo ya kai ni Airport, zan kai Jawad wurin Anty Hafsa."
Kafin ya karasa ta fashe da kuka tamkar yarinya karama tana cewa " Billahillazi ban yarda ba, jaririn yaron za ka kai har Lagos?"
Dariya ta so subuce masa, ya cije yavce, "Ba yardaki na nema ba, fada miki na yi, saboda kina da hakkin ki sani".
"Idan na yarda Allah ya tsine mini, ai da ma na san yanzu ba ni da wani muhimmanci a gurinka".
Ficewa ya yi ya bar ta, ba tare da ya ba ta amsa ba, yana jin farinciki, da dukkan alamu shawarar Mahmoud za ta yi tasiri.
Kwanciya ya yi, bayan ya kashe fitila, addu'a ya fara yi, kawai ya ji ta shigo masa ba sallama.
Tasa hannu ta kunna fitilar dakin, suka kalli juna, na tsawon sakwanni, wani abu na taso musu a zuciya.
Shi ya fara dauke idanuwansa, murya ba amo ya ce, "Kin san dai ba na iya barci da haske a kaina ko? Yanzu kuma na gama fada miki Asubanci zan yi, don Allah ki bar ni na yi barci".
"Ka tashi mu yi magana".
"Ki adana maganar ki, idan Allah yasa na dawo lafiya, gobe irin wannan lokacin sai mu yi maganar".
"Wallahi yanzu za a yi ta". Ta fada cikin rawar murya hadi da kuka.
Ta zauna kusa da kafafuwansa, tana cewa " tsanar da ka mini har ta kai ka kaurace mini, sannan ka raba ni da yarona?".
"Ni ban kaurace miki ba, ba kuma zan raba ki da danki ba, kin taba jin inda aka raba uwa da danta? ko'ina na kai shi, ina tabbatar miki wataran da kansa zai neme ki. Ke kika ce idan ina son zaman lafiya sai dai a yaye shi, zaman lafiyar nake so".
"Wallahi ba zaman lafiya kake so ba Uncle, kawai so kake ka sake jefa ni cikin wani tashin hankalin, ai ba a nan kake kwana ba, sannan mene ne na kai wannan dan kilifin halittar har Lagos?"
"Kin ga Sa'adatu ni kwana a nan dakin ba ina nufin wani abin ba ne, kullum ni nake bin ki dakinki for more than a year, ke mai yasa yau ba za ki zo nan ba, ko kin zo na kore ki?"
Jikinta ya yi sanyi da jin kalmar Sa'adatu a bakinsa ta san fushi yake da ita.
A hankali ta furta, "So nake ka fasa tafiyarku Lagos".
"Ba zai yiwu ba, na riga da na fada mata gobe tasa a tare ni a Airport, kuma sai na koma nace na fasa zuwan?".
Ta fara kuka tana fadin, "Ba na son tashin hankali Uncle, na roke ka kar ka raba ni da yarona".
"Yau kusan sati ina fama da ke, ba irin ha'kuri da rarrashi da ban miki ba, amma kin runtse ido kina mini diban albarka, ko daukar yaron nan sai na miki wuta-wuta kike yi, dazu ga ki, ga shi, amma kika bar shi yana tsala kuka, zan zauna kullum a gida ne? Dole zan fita. Bayan haka kin daina yin komai a gidan nan tun daga kan shara, da girki, duk ban ce komai ba, ina yi, duk da haka ban tsira ba, duk maganar da ta zo bakin ki fada mini kike yi, har ki kalli idona ki sa mini sharadi idan ina son zaman lafiya sai na yi kaza".
Jikinta ya sake yin laushi, bai ba ta damar yin magana ba ya zarce da fadin, "Kin yi strike din wanka, da yi mini magana, akan cikin da ba ni kadai na samar da shi ba, ikon Allah ne. Kin san adadin matan da suke jika filon su duk dare a dalilin rashin haihuwa? Kin san adadin matan da suke fuskantar tashin hankali akan rashin haihuwa, ALLAH kadai Ya san adadin ba'kin cikin da irin wadaccan matan da suke cikin jarrabawar rashin haihuwa suke ciki, ke Allah ya ba ki, ba tare da kin sha wahala ba, ya sake kara miki, maimakon ki zama cikin bayi masu godiya, sai kika zama cikin masu butulci".
Zuciyarta ta yi sanyi, salama ta shige ta, ta fara fadin, "Astagafirillah!" A zuciya.
A fili kuma sai ta tsinci kanta da cewa "Ka yi hakuri".
Dadi ya lullube shi, amma bai nuna ba, ya ce "Ya wuce." A gajar ce.
Ya zuba mata ido yana ganin yadda idonta suka fada ciki, bayan rashin lafiya ya tabbatar har da yunwa ke sakadar ta.
Kafin ya yi magana ya ji tana cewa yunwa na ke ji.
Ya basar ya ce, "Babu kayan abinci ne a gidan?"
"Kwana biyun nan fa ba ni da lafiya, na san kuma idan ba na jin dadi kai ne kake dafa mana".
Ya harareta kadan sannan ya furta, "To na daina yi tunda ba kya gode mini, ba kya ganin kokarina".