← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 113

Sashe 49

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya abin ya bawa Hajiya, amma sai ta dake, ta dinga salati tana fadin "kice cin fuska ya miki? banga laifin ki ba, dole ki guji magani, ko nice haka zan yi".

Shi dai Mk ya zama tamkar gunki, yana kallon shari'ar son rai a wurin Hajiya.

Ba zato Hajiya ta ce yaje ya siyo wasu maganin.

Ya ce " Bafa su bane, tunda take wannan bala'in na zubar da su, na siyo masa wasu, amma ta "ki bashi"

Da rawar murya ta ce "Billahillazi, baka canjo wasu ba, duk abin da ya fito ta hannunta, na tsane shi, zan kuma gane".

Jin haka yasa Hajiya fadin "Bar Wannan gadddamar je ka siyo wasu a bashi ya dan sami sauki"

Bai q musa ba, ya mike, ya dauki ledar maganin, ya fita.

Sai da ya fita Hajiya ta dinga mata nasiha, tare da cewa "ki rage nuna masa kishinki a fili, sai ya samu dalilin da zai dinga musguna miki".

Ta kalleta tace "tunda da wuta jona ruwan zafi kuyi wanka".

Ta mike ta cika buta ta jona, mintina kalilan ta kashe kanta, ta juye, ta sake maida wani, kafin ta fito, Hajiya ta wanki Jawad a bandakin tsakar gida.

Ta dama musu kunu, ta juye a flask din shayi, ta zubawa Jawad a kofi, ta bashi, ya shanye tas har da kari, ta tabbatar shima har da yunwa ta sake gigita shi.

Sa'adah ta fito sanye da riga da zani na atamfa, dinkin ya zauna sosai, mussaman da bata cika daura zani ba.

Ta mikawa Hajiya kayansa, sai da ya koshi ta koge masa baki sannan ta saka masa kaya, dai dai lokacin kuma, Mk ya dawo dauke da magungunan, leda biyu, ya mikawa Hajiya, sai da Sa'adah taga na wurin Farida, ga kuma wadda ya sake siyowa, sannan ta saki ranta, a ransa fadi yake masifaffiya kawai.

Take Hajiya ta bude ta bashi, ta shafa masa na shafawa, barci ya dauke shi mai nauyi.

Sosai Hajiya ta musu fada, kuma duk na Mk yafi yawa, jan kunne 'daya, ta yiwa Sa'adah, kar ta sake saka Jawad a cikin fa'dansu, ta ki cin abinci, shi akan mai zata hana shi?

Ta cika kofi, da kunu ta mika wa Sa'adah tace "Shanye ki bani kofin".

Ta karba, ta fara sha, ya mata dadi sai kamshin kayan yaji yake yi.

Shi dai Mk yana kallon ikon Allah, anbawa Jawad, da Sa'a, shi ko oho.

Sai da Sa'adah ta shanye sannan Hajiya ta mike ta ce "zan tafi nasan ki da jin magana, na kashe wannan magana kar a kuma tada ta"

Da sauri ta amsa da "in sha Allah ta wuce".

"Na gode Miki Sa'a, Allah ya miki albarka".

Sa'adah ta amsa da "Ameen Allah ya kara girma" ta tashi tana mata rakiya hanyar waje.

Tare suka fita da Mk zai kaita, a hanya tana sake masa fa'dan, lallai ya kiyayi zungurar Sa'a, ta dora da cewa

"Kana ganin irin yadda take mutunta ni, tana haba haba da yan'uwanka, iyayenta mutanan kirki, lallai ba zamu shirya da kai ba, idan kace zaka wulakanta ta, mussaman ma akan wacce bata zo hannun ka ba".

Har ya kaita gida, kashedi take masa iri iri.

Da za ta sauka ya ce "kin basu kunu, amma Ni baki bani ba".

"Ina sane, kai Sa'a ce mai ba ka".

Murmushi ya yi, tare da cewa "Hajiya kar kisa na fara kishin yarinyar nan, naga tana neman zarta ni a gunki".

Ta yi murmushi tace " maza ka juya ka sake rarrashin ta, ka tsaya a hanya ka siya musu dan wani abin, kunu kadai bazai ri'ke ta ba, ta tara yunwa".

Haka kuwa, ya biyo ta titin Hausawa bawo road ya siyi wainar shinkafa da ake yi mai dadin gaske, a falo ya tarar da ita, tana zaune tana kallo.

Bata dago ta kalle shi ba, ta amsa sallamar sa, daga haka bata kara magana ba.

Ya tsaya ya ce "Ba ki mini sannu da zuwa ba fa".

Ba tare da ta kalleshi ba, ta ce "inace ka ce kowa ya yi harkarsa?"

"Na fa'da! amma dai Hajiya ta kashe maganar, ta ce kar a kuma tada ta".

"Ita maganar maganin Jawad ta kashe".

Ya zauna, yana cewa "ga waina na siyo miki, tashi ki zubo mana".

Kanta a kasa ta ce" ci abinka".

Ya kai kicin ya adana, ya zubo wadda zai iya cinyewa, tare da kunu a kofi, yaso ya shiga dakinsa, sai kuma yafi zumudin zama kusa da ita.

Ya zauna yana fadin "dan Allah sauko ki taya ni ci".

"Ba zan sake cin abinci da kai ba, tunda muka yi aure, baka taba kaini restaurant munci abinci ba, amma ka dauki wacce kake so kun je! ba ruwana da sabgarka".

Ta fa'da hawaye na balle mata, ya yi shiru, yana jin sabon tashin hankali, ya rasa da bakin da zai kare kansa.

Ya yi shiru, ya kasa cin abinci, ko kaffara ba zai yi ba, su Safina ne suka kawo mata wannan labarin.

"Ki yi hakuri kin ji Sa'adan Uncle".

Kamar ya watsa mata garwashi, ta zunkudo ta ce " ta Ina ka zama kawuna?"
Kai ba 'kanin Baffa bane, bare na Inna, daga jiya ba zaka sake jin bakina ya kiraka da Uncle ba, ita dai da kuka hada dangi, sai tayi ta fa'da na bar mata"

"Ashe lokacin da kace min dole kayi kishin mace, idan ka ganta a gaban motar wani da ba Muharraminta ba, 'karya ka fada tsagwaronta? To ita mai kuka hada daka dauketa a gaban motarka?"

Kansa ya kulle, ya kalleta ya ce "Na yarda ban kyauta ba, ki yi hakuri, ki bani wata damar, ko banci albarkacin komai a gunki ba, naci albarka cin mahaifiyata da tazo ta baki ha'kuri, ta kashe maganar".

Jikinta ya yi sanyi, ta ce shikenan na ha'kura".
Da'di ya kama shi, ya matsar da kwanon abincin kusa da ita, ya ce to sauko muci".

Ta girgiza kai, "Na hakura, amma ba zanci da kai ba".

Ya tura mata, "to ci wannan, bari na zubo wani," ya mike ya fita da sauri.

Cikin sa'a ranar bashi da lakca sai 'karfe daya, dan haka, bai fita ko ina ba, yan tare da ita, yana ta kokarin wanke mata zuciya, shi da kansa ya tabbatar a duniya ba abin da yake so sama da Sa'adah da 'danta, idan aka cire Hajiya.

Sai dai duk nacinsa bata yarda da shi ba, kan dole ya 'kyale ta.

Kwana biyu tana mai yawo da hankali, kafin ta ha'kura ta sallama masa kanta, cikin rawar jiki yake komai, yana ayyana distance fa yana da amfani, domin ji yayi ta dawo masa sabuwa.

Yana samun kudi kuwa, ya dauke su ita da Jawad suka je restaurant din Royal Tropicana suka ci abinci, suka yi hotuna, irin wadda ake wankewa a take, take & wash, suka zarce country mall, ta zabi abin da take so.
A hanya ya ce "shikenan yanzu na dawo Uncle?"

"Hmm! magana ta wuce ka daina dawo mini da ita".

Ya shagwabe fuska ya ce " idan har da gaske ta wuce, then called me Uncle".
Ta fara dariya, tana cewa "ashe son girma ne da kai ban fahimta ba?"

Shima ya taya ta dariyar sannan yace "tsakanin ki da Allah! Idan nace Miki Sa'adatu ba kya jin wani iri? ke da kike kanwata nasan kina jin ba dadi, bare ni ki gatsa sunana gatsal"

"Amma ai tun ranar ban sake fada ba".

"Eh baki sake ba, sai dai kimin ta kurame, kiyi maganar ki ba tare da kin kama sunana ba".

"Nifa Wallahi na tsani, waccan sunan da kake kulafacin sai na cigaba da kiranka da shi".

"To shikenan zabo min wani, mai sweet, kika rufe ido kika cemin wai baki hada dangi da Ni ba ko?"

Ta ce "eh mana ai ba karya na fada ba".

"Ni Malamin ki, Ni Mijin ki,Ni Baban danki, duk wannan ha'din kin raina shi?".

Ta tura baki gaba, ta ce "shikenan, ka zabi sunan da zan fada maka a cikin wadannan,Malam, Miji, ko Uban 'da"

Dariya ta kwace masa sosai, cikin dariyar ya ce, "ke yanzu sai ki dinga cemin Uban 'da?"

*Surayya Dahiru*
✍🏼✍🏼✍🏼
26/03.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

*Lafazi writers*.

*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*

*Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*.

*GODIYA*
*Ina matu'kar godiya ga wadanda suka yi mini addu'o'in samun lafiya ga warwarewar lamura, tunda ga kan masu kira ta waya, da masu text, da masu yi mini ta dandalin WhatsApp, dukkanku na gode madallah, ubangiji ya fini yabawa*.

65-66.

Ta yi murmushi ta ce " mai zai hana na fada maka idan kana so?"

Ya bugi sitiyari ya ce "my sweet Sa'adah, sometimes you are so funny".

Ta yi shiru ta kyale shi, ya sake cewa " ke yanzu ko inkiya da Jawad baza kimin ba, naga yanzu daga mace ta haihu take karawa Mijin ta matsayi ta hanyar yi masa alkunya da sunan yaronsu".

Ta tabe Baki, ta yi shiru, sai kuma ta kasa hadiye maganar.

"Akan mai zan maka alkunya da Jawad alhalin wadda ta fini cusa kai ta riga ni? Inace Farida Abban Jawad take kiranka? Kasan Ni kuwa har abada bazan bi ra'ayin ta ba, banda azarbabi, ba sai ta bari idan ta haifar maka nata sai ta yi komai ba, amma dan son sai ta nuna ita gwanace akan kayan da ba nata ba yasa ta ke yi mini katsalandan, ai na so ta yi kataborar ce min Iyah Basiru, wallahi da jikinta ya fa'da mata domin kuwa ba abin da zai hana na mata 'kamshin mutuwa".

Ganin za ta tunzuro da yawa sai ya share maganar da cewa "Na zabi miji, amma Zauj za ki dinga fad'a maimakon miji".

Yana rufe baki ta ce " duhun fata ta kadai, ya isa ka gane ni ba balarabiya bace, dan haka nafi kishin yarena".

"Amma duk musulmi dole ya dau larabci yarensa ne, domin yaren kura'ani ne, duk sallar duniya kuma a larabce muke yinta".

"Wannan daban" ta bashi amsa a takaice, daidai lokacin kuma suka iso gida.
Chapter 49 · 0% Book details