← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 113

Sashe 94

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ka cire kanka cikin maganar kawai, ka barmu da ita, yanzu ne zamu kafa alkalamin mu cikin tawada, jikina yana bani bakin alkalamin mu bai bushe ba".

Baffah ya nisa ya ce "To Ubangiji ya dafa muku, ya yi zabin alheri".

Kwanaki uku kenan 'Karfi ya kasa fa'dawa Mk sakon Baffa adalilin har yanzu jikin nasa ba kwari, jiyama sai Mahmoud din ne ya mayar da Jawad makaranta, da hutun ya kare a jiyan.

Sai da aka sake yin kwana biyu'Karfi ya tarar da Mk har gidansa suka tattauna sakon Baffah! A farko maganar gaba'daya rikicewa ya yi, amma 'Karfi ya shawo kansa ta hanyar fa'din ina tare da kai Bichi banji a raina zamu rasata ga'badaya ba, fatana mu yi addu'a, mu bi hankali kar kuma mu sare, mu yi ta binta tunda mu muke nema, sannu a hankali har mu samu mu damketa".

Mk ya nisa, ya ce" tunda na rabu da yarinyar nan wani abu mai tsananin nauyi ya tokare ni a kirji da makoshi, har yau din nan bai fada min ba, sai kara girmama da abin ya yi a yanzu da nake ganinta da wasu, wai ya zanyi ne? Wallahi na fara debe kauna da rayuwa domin Ni ka'dai nasan azabar da nake hadiya mussaman ace dare ya yi lokacin da zan samu na huta, a lokacin ne nafi shiga tasku bana iya barci, yanzu kuma abincin ma baya shiga".

'Karfi ya nisa ya ce "ka daina damuwa komai zai wuce, idan ka ga ka rasata, to kawai ka dauka babu alheri ne a kasancewar ku, ubangiji ne ya karar da zaman. Sai ka duba ai ka rayu shekaru bakwai babu ita, kuma baka mutu ba, idan har ita zata iya yin jarumtar hakuri da kai gaba'daya, bayan ta sha dukkan ba'kin ciki da tashin hankalin son komowa gareka, to kuwa kaine ka fi cancanta da irin wannan jarumtar".

Mk ya yi shiru yana gasggata Sa'a ta fi shi jarumta, tunda har zuciyarta bata buga adalilin aurensa ba, don kuwa shi yanzu ya gama yin imanin duk ranar da aka daura aurenta da waninsa tabbas a ranar ajalinsa zai sauka adalilin bugawar zuciya, ko hawan jinin da ya zarce kima.

A raunane ya kalli 'Karfi ya ce "Ai ita mace ce, ubangiji ya sanya musu wani irin karfin jure dukkan kalubalen tarbiya da kishi, amma mu ba a bamu wannan ba, namiji karfin gwagwarmaya aka bashi, da karfin tsayawa iyalinsa akan dukkan bu'katun yau da kullum".

'Karfi ya nisa ya ce "Hakane! Abin da nake so yanzu da kai shine, ka dora jarumtar gwagwarmaya a zuciyar ka, tunda ka gamsu muna da karfi da juriya anan bangaren, to idan kuwa hakane, zamu yi gwagwarmaya har mu samu mu kwato abin da yake namu ne".

Tun daga ranar suka fara yiwa Iyah wani irin naci, mai cin rai.

A Rana su kanje sau uku, kowanne lokaci zuwa suke yi, tun Inna tana ganin zasu gaji su daina, har ta fara ganin ba zasu gaji ba, domin kuwa kullum zaryar kara gaba take yi, ba baya ba.

Haka gidan Sumayya, hatta Idris a yanzu tausayin Mk yake ji, shiyasa ya fa'dawa mai gadin gidan matu'kar Mk ne suka zo, to ya bude masa gate kai tsaye.

Tsawon sati uku ana wannan zaryar bai fi kuma sau biyar suka samu nasarar ganinta ba, a cikin zuwa fiye da arbain.

Duk inda hankalin Mk yake a tashe yake, yayin da Mahmoud yake ta karfafa masa guiwa duk da shima bai yi zaton kafiyar Sa'adah ta kai haka ba.

Ranar alhamis da hantsi suka isa gidan Sumayya, sun shafe lokaci mai yawa a zaune, sannan ta fito, sanye da hijabi fuskar nan a daure, ta iso, da alamu tilas aka yi mata.

Dr Karfi ya mike ya na fa'din barka da fitowa sarauniyar mata. Ta yi shiru tamkar ba da ita yake ba, domin ta lura shine jagoran wannan nacin da suke mata kamar ba'kaken mayu.

Ya ce "Allah ya huci zuciyar giwa kuma gimbiyar Mata, ba zamu gaji da bada hakuri ba, ba kuma zamu gajiya ba, har sai kin dawo mana da walwalar da ta yi mana tutsu. Ki yi ha'kuri, ki zo ki haska mana zuciyar aminina da gidansa gaba'daya, Ina rokon ki, badan mu ba, sai dan ubangijin ki, ni shaida ne na irin tsananin son da yake Miki".

A tunzure Sa'a ta ce "ka dinga jin tsoron ubangiji Baban Dady! Sai yanzu! Sai yanzu! Sai yanzu zaka tirsasa ni, me yasa a wanccan lokacin baka tirsasa shi ba, me yasa ka bari na wulakanta, na tabbatar ba zaka so ayiwa kanwarka abin da aka yi mini ba. Amma yanzu da yake farin-cikin abokinka kawai ne a gabanka, ka na'de 'kafar wandon yi mini dole, kasan ina jin nauyinka, akan me zaka takura ni irin haka, an ta'ba yin aure dole, to ko Baffah ma na tabbatar masa bana son wannan mutumin, kaima na fa'da maka, ka sakar mini mara, na ro'ke ka".

Ta karasa cikin kuka sosai, Dukkan su sun yi laushi, mussaman Mk da yake jin tamkar ya hadiyi zuciya saboda yadda yake jin ciwon yadda take fadin bata sonsa, a gaban kowa.

Mahmoud ya kalli Agogon hannun sa, ya ce "hakuri zaki yi, ba yadda zamu yi ne, ki 'kara hakuri, ubangiji zai baki ladan masu hakuri.

Ya kalli Mk ya ce " ina da appointment nan da mintina talatin a makaranta, zan wuce, idan ka gama kawai mu hadu a gidanka bayan azahar".

Daga haka ya fice da sauri, da mukallin motar Mk a hannunsa.

Tana tsaye tamkar soja. A hankali Mk ya ce "zauna mana Dan Allah".

Bata yi musu ba, ta zauna.

Ya zuba mata ido yana kallon yadda ta ke cika tana batsewa ya saki ajiyar zuciya mai zafi ya ce "A gaban kowa kike fadin ba kya sona, Ni kike wulakantawa haka? Kada kishi yasa ki manta ke ce kika mini laifi?"

Da kuka ta ce "Ni na maka laifi tabbas, ka kuma hukutan ni, to menene kuma ba sai a barshi a hakan ba, gaskiya kun matsa mini, tsakani da Allah kun shiga rayuwata, sau nawa zan fa'da maka bana sha'awar sake rayuwa da Kai? Na ha'kura, na bar mata, Ni ma ka bar ni, Dan Allah".

Kafin ya yi magana ta sake cewa "kafin ka aure Ni ka kira ni Ballagaza, na yi hakuri saboda ina ta'kama da Budurci, yanzu kuma ka ce ina ha'intarka, fa'da mini dame zan kare kaina, tunda ba ni da Budurci a yanzu?"

Da sauri Mk ya karaso kujerar da take zaune, ya zauna a hannun kujerar ya sassauta ya ce " Na da'de ina fada miki, bacin rai ne, ba ina nufin haka har zuciyata ba, ki yi hakuri. Na janye kalamina, wallahi tallahi ke din katangaggiya ce, ki bar wannan maganar, ko tunawa bana so, hankali na tashi yake yi. Na janye! Na janye! Na janye Dan Allah a rufe wannan maganar har abada".

Ta dinga kuka sosai mai cin rai, ta kasa cewa komai.

Ya nisa ya ce" kukan ya isa haka, ki yi hakuri ina fatan wannan ne kukan ki na karshe akan wannan matsalar".

Ta kifa kanta a dayan hannun kujerar tana sake tsananta kukan sosai, Ta ce "indai baka rabu da ni ba, na tabbatar zan dauwama ina kuka ne, domin zan rayu ina raba ka da wata ne, Ni kuwa da haka gara na auri me mata uku na zama ta hudu".

Mk ya rasa mai zai yi, ko ya ce, gaba'daya tunaninsa gaba'daya ya kulle.
Ya tabbatar auren Farida ne cikas dinsa a gurinta, shine yasa ta kasa amincewa da shi.
Ba yadda zai yi akan Farida kuwa domin bai aureta dan ya saketa akan wani 'karamin dalili ba.

Ya sassauta ya ce "Yarda da 'kaddara na cikin sharuddan cikar imani, ki ture komai, ki kalle ni har yanzu ba abin da ya canja na soyayyar ki a tare ni, ki bani amanar kan ki wallahi ba zaki yi nadama ba".

"Ko yanzu kika amince mini, wallahi na sha wahala, na azabtu, yanzu haka ina daf da kamuwa da ciwon zuciya, ba komai bane ya janyo mini ba, illah ganin ki da wasu mazan".

Ya sauko ya dur'kusa a gabanta karon farko ya ce "Ga ni akan guiwata, ki yi hakuri, ki yafe mini, ki sake bani wata damar, ni na san kina so na. Plz Sa'adah let Gone by gone, ba zan iya wannan rikicin ba, na horu hakanan, ki fa'dawa Baffa mun shirya, na kuma kawo miki Baba Isa gaban ki, ki fa'da masa mun shirya, kin yafe mini, Ni kuma na miki al'kawarin zaki rayu cikin soyayya mai wuyar samu a Yau".

Ta dago ta kalle shi a durkushe a gabanta, da'di ya kamata, amma sai ta waske ta ce "Ni fa ba zan yafe ba, matu'kar ba wani ne ya aure ni ya ta'ba ni kamar yadda kake ta'ba wata macen ba".

Ya mike da sauri ya ce "shikenan, dama ke ai ba'a taba rarrashin ki, kin gamsu cikin da'din rai ba, kaddara ce ta hau kaina ban kuma isa na kauce ba, tunda kin kasa fahimta shikenan, amma ki sani idan fa 'kaddara ta gwada iko akan ki, kika dawo mini, ba zan gamsu kin mini uzziri ba".

Ta tura baki gaba sosai ta ce " Da ikon ubangiji ma ba zata faado kaina ba".

Ya koma ya zauna a inda yake zaune tun farko yana tunanin mai kuma zai yiwa wannan yar darun ta fahimce shi, shi tashin hankalinsa daya ya ganta da wani, ba dan haka ba, da ya daure ya kyale wannan yarinyar da take neman manna masa ciwon zuciya.

Sun Jima a zaune ba um bare um um.

Ya mike ya ce "zan tafi ina fatan idan na kira wayar ki, ki dauka.
Allah ya huci zuciyarki".

****
A cikin wannan yanayin shari'ar Sanata Ibrahim Hassan ta sake zagayowa, bayan doguwar muhawara da tarin hujjojin lauyoyinsa, kotu ta wanke shi daga dukkan tuhumomin da ake yi masa.

Sa'aadah ta bukaci a bashi naira miliyan hamsin a matsayin diyyar bata masa suna da lokaci.

Jajircewar da Sa'a ta yi a wannan shari'ar yasa sunan ta ya shahara, ta yi farin jini.
Chapter 94 · 0% Book details