Sashe 66
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka sosai Sa'adah ta yi a wannan daren, kafin ta tashi ta 'doro alwallah ta fara sallar nafila, idan ta na addua a fili take fadin " Allah ka rufa min asiri, ka mayar da ni 'dakina, Allah na tuba".
Sumayya kawai kallon ta take tana sake jin tsoron ubangiji na kamata, yau Iyah ke wannan haukan akan Mk, Ashe duk wani kau'di da ginshirar da take yi shine kanta ya dawa?
Ko yau Mk ya mayar da ita, ta yi amanna ya karya duk wata fuffukar da take ji da ita, za kuma ta nutsu ta daina fitinarsa, tun lokacin da ta haihu amma ya iya hana ta zuwa ta dubo ta, ta tabbatar Sa'adah ta fara kai shi bango ne, ta kuma koya masa rashin kirki.
Washagari kuwa ya kawo Jawad har kofar gidan Baffa da 'yar karamar jakar kayansa da kuma ledar biskit da alawowi ga su Ayman.
Da gudu ya shiga cikin gidan! Mk na tsaye yana jin rashin dadi, yana son ya shiga ya gaida Inna, amma kunya ya ke ji, hakanan ya ke ganin rashin kyauta wa idan har bai shigan ba, saboda ya saba duk sadda ya kawo shi zai shiga su gaisa sannan ya tafi, haka idan zai dauke shi.
Har ya juya sai kuma ya dawo ya shiga, ya dade a tsaye a zauren, yana tuna moments dinsa da Sa'adah a cikinsa.
Dukkansu suna tsakar gidan Suka ga Jawad ya shigo a guje, suka rungume juna da Ayman 'din Sumayya, duk da Ayman din ya bashi shekaru biyu, amma abota suke yi sosai.
Inna ta tashi ta dauko hijabin ta da ke rataye a bakin 'kofa ta saka tana tambayar Jawad wa ya kawoka?
Yace "Malam ne", ba ta zauna ba ta dauko tabarma ta shimfida a inda ta saba shimfida masa, tana ayyana
tasan zai shigo, aikuwa kafin ta dago ta ji sallamarsa.
Ganin Sumayya lullube ta ke da mayafi, Sa'adah ce kawai a zaune ba mayafi daga ita sai doguwar rigar atamfa wadda wuyan ya mata yawa tsabar rama, kanta ba dankwali asalima tsifa take yi, ga tulin gashinta a gefen ta wadda ya ke zuba tamkar wutar daji.
Inna ta amsa masa tare da bashi iznin shigowa, Sa'adah da tun jin sallamarsa ta daskare a zaune, ta rasa me za ta yi duk kuwa da yadda Jawad ya saki Ayman ya zo ya haye cinyarta yana taba wuyanta, alamun ramar da ta yi shima ta bashi mamaki.
A hakan Mk ya shigo, idonsa ya fada cikin na Sa'adah, gabansu ya buga a tare da azama ya dauke idanuwan sa, ya isa ga tabarmar da yasan dan shi aka shimfida, a ransa ya dinga godewa ubangiji da 'kaddare shi ya shigo, da ya kunyata Inna.
Suka gaisa cike da kunya da girmamawa tamkar komai bai faru ba, haka suka gaisa da Sumayya.
Da Sa'a ta gaishe shi ya amsa mata ba yabo ba fallasa, amma yanayin da ya ganta ya matu'kar bashi mamaki da tausayi, mussaman da ya ga Jawad ya lafe a jikinta.
Ba ta ji kunyar Inna ba,
bare Sumayya, ta ajiye Jawad ta mike ta dauki hijab ta bi Mk hanyar waje, a zaure suka tsaya, ya zuba mata ido, bai ji so ko tausayin yadda ta lalace ba, domin tare suke shan bakin cikin, kawai dai shi Namiji ne, namiji kuwa da juriya aka san shi.
Ya daure ya ce "har yau ba ki fara cin abinci bane? kin ga irin ramar da ki ka yi kuwa?"
Hawaye ya 'balle mata ta ce " Ka yi hakuri , na 'kira Jawad ka tafi da mu, ka mayar da ni gidanka, ba sai ka kulani ba, zama tare da kai 'karkashin inuwar aure ya gamsar da Ni".
Ya yi murmushin da babu nisha'di ko kadan yace " ba kya yawan addu'a, ki nemi zabin Allah a tsakanin mu, ba son rai ba, sau da yawa mukan so abu 'kololuwar so, sai abin ya zama sharri ne a garemu, hakan nan muna 'kin abu iyakacin 'ki, sai ya zama alheri a garemu".
"Kar ka kwatanta ni da sharri Malam, ina hadaka da girman Allah ka yi hakuri ka yafe mini".
Ta tsugunna guiwa biyu a 'kasa
Ta cigaba da cewa "saura 'kiris na kammala idda, ka taimake ni, ka ji 'kaina."
Daidai lokacin Baffa ya shigo zauren ya kewaye su ya wuce ba tare da yace uffan ba.
Jikin Mk ya yi mugun sanyi, bai so Baffa ya gansu a haka ba, ya dubeta ya ce " ki koyi karban rayuwa a yadda ta zo miki, ki kuma daina wasa da damar da rayuwar za ta baki, na so ki, iyakacin so, amma menene amfanin son da babu kwanciyar hankali ko aminci a cikinsa?"
Da haka ya juya da sauri yana fadin "ki yi murna kin zama 'yantacciyar macen da ki ke fata".
Ta jima tana kukan zuci da na fili, sannan ta shiga gidan, ba ta tsaya a tsakar gidan ba ta shige daki ta kwanta tana cigaba da rizgar kukan da ba ya amfana mata komai.
Ganin wulgawar Jawad ya dan rage mata kewa, ga Sumayya da take tausarta.
Ranar lahadi suna zaune, Sumayya na mata kitso bayan Ahamad 'kanin Mk ya zo ya tafi da Jawad, kawai suka ga ana ta shigo da kaya, kallon su kawai Sa'adah ta yi ta fahimci kayan ta ne Mk ya Aiko musu, tunda ya ga an'ki zuwa a debo.
Abin mamaki sai ba ta ji kuka ya zo mata ba, ko dan ta yi kukan har ta gaji ne?
Tsakar gidan sai da ya cika da kaya, domin duka gadajen nan uku ya Aiko mata haka nan kujerun falo da tv plasma hatta freezer da bai 'dade da siya ba, ya ha'da ankawo mata.
Ga wasu bakko guda uku sha'ke da kaya, Sumayya ta bude biyu duka kayan Sa'adah ne, ya yin da 'dayar labulaye ne da zannuwan gado a wanke a goge, sai lokacin 'kwallah ta zowa Sa'a, wato ya da'de yana shirya mata kaya, tunda ga labulayen da suke dakunanta ma ya cire su anwanke su. Haka akwatunanta duka kayanta ne a ciki, ba kayan da ba' a wanke an goge ba, a cikin fishi ma Mk ya iya alheri, ta ayyana a ranta.
Gwala gwalan ta ne kawai ba ta gani ba, indai ba a tsakiyar kayan ya 'boye su ba. Ilai kuwa cikin katon akwatin ta ya saka mat su a tsakanin kaya.
Dukkansu jikin su ya yi sanyi da ganin kayan, hatta Baffa da yake nuna mata bai damu ba, ganin wannan kayan ya tayar da hankalinsa, balle Inna da take ta faman goge hawaye a fuskarta.
Ganin hakan Sumayya ta roki Baffan su, za ta tafi da Sa'adah Gombe, ta kwana biyu, idan ta 'dan warware sai ta dawo.
Ya kalli Sumayya, a sanyaye ya ce "kin manta ba ta kammala iddarta ba? har yanzu a matsayin matar Mutari ta ke, bani da ikon da zan turata wani guri alhalin ba hakki na bane yin hakan".
"Baffa dan Allah ka bari mu tafi, mutumin nan, ba mayar da ita zai yi ba, gaba'daya ya fita a kaina wallahi".
Murmushi ya yi ya ce " Ban sanki da son zuciya ba, Sumayya! Kar son 'kanwar ki ya mayar da ke mai son kai, kinsan me ta shuka masa ne? Ruwa ba ya tsami banza, har yau ya 'ki fadan me ta yi masa, maimakon haka sai ya 'dorawa kansa laifi, Ina rantse miki da Allah! Iyah ce ta yi wani abu marar 'dadi, ko shekaranjiya na ganta durkushe a gabansa, Ni na fara tsoro da wasiwasi akan lamarin ta, Allah dai ya sa ba wani mugun abu ta yi ba"
Sumayya ta kasa magana, tausayin Iyah na ratsa ta.
Ko da shiga dakin a zaune ta sameta, ta tsurawa gefe 'daya ido, idonta a soye, sai da Sumayya ta kirata sau uku sannan ta amsa a firgice.
"Ki fa rage dogon tunani Iyah Ina jiye miki ciwon farat 'daya.
Ta dago ta dubi 'yar'uwarta ta ce "Dama na mutu Aunti".
Da sauri Sumayya ta ajiye Anis ta 'karasa kusa da ita ta rungumeta ta ce " idan ki ka mutu, ki barni da wa Iyah? ke ka'dai gare ni bayan Innah, ko da na haifi mace ba zata cike min gurbin ki ba, bare ban haifa ba, me yasa ba za ki duba wadda farin cikinsu na 'damfare da ke ba? Yanzu Mukhtar din da ba ki san shi ba sai da kika mallaki hankalin ki ne, zai sa ki yi fatan mutuwa ki bar Baffah, ki bar Inna, ki bar Jawad, ki bar Ni?"
Sai lokacin kuka mai ciwo ya gocewa Sa'a.
Sumayya ta cigaba da cewa ki fauwalawa Allah lamarin ki, ina tabbatar miki zai kawo miki mafita, ki ha'kura da Mukhtar yadda ya ha'kura da ke, ba sai da shi za ki rayu ba, ba sai da shi za ki yi farin ciki ba, ki dube mu, ruwa da iska ba zamu canja ki ba, shi kuwa ko gobe kina iya jin ya auri madadin ki, ya shayar da ita soyayya irin ko ma ta zarta wadda ya miki, fatana dai ki 'dauki darasi, kar ki sake maimata irin kuskuren da ki ka yi idan kin samu wata damar".
Ganin maganganun na shigar Sa'adah sosai, Sumayya ta zarce da fadin "gaba'daya aure ha'kuri ne da kawar da kai, duk macen duniya da ki ka ga ta tsufa a 'dakinta ta shiga 'kalubale kala kala, amma idan aka yi ha'kuri aka danne sai a cimmma babban matsayi, ki cire buri, da son 'kyale 'kyale ki rabu da 'kawayen banza na tabbatar wadannan abubuwan sun taka muhimmiyar rawa wurin mutuwar aurenki".
Sosai ta ke kuka a 'kirjin Sumayya karon farko tun bayan rabuwar su da ta samu ake rarrashinta cikin tausayawa.
Haka suka shafa lokaci mai yawa Sumayya na lallashinta, tare da 'karfafa guiwarta.
Kwanaki goma Sumayya za ta yi tare da yaranta, adalilin Yaran suna hutun zangon karatu na uku, sannan kuma mijinta na cikin tawagar da aka zaba zuwa New York din 'kasar Amurka akan sanin dabarun inganta bankunan 'kasashen Africa.