← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 113

Sashe 95

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har gida Mai girma Sanata ya aiko mata da dankareriyar mota kirar Toyota Camry new modern.

Direbansa da wasu yaransa ne suka kawo, suka danka a hannun Baffah. Bayan sun yi godiya a madadin Sanata.

Washagari asabar Khalil ya mata wayar zai zo ya mata godiya tare da ban gajiya.

Saboda jidalin Mk ta masa kwatancen gidan Sumayya dan kar ya zo shago ya hango ta da Khalil, duk da a gidansu ta kwana. Sai bayan azahar ta tafi gidan Sumayyan tunda ya ce sai bayan la'asar zai zo.

Aikuwa ana idar da Sallar la'asar ba jimawa ya iso, sosai suka sha Hira, wani lokacin kuma suyi ta jifan junansu da kallon kauna sai kuma a waske da murmushi, tabbas soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa.

Amma Sa'a ta 'kudire ba zata auri Khalil ba, domin ta san komai na iya faruwa da Mk a sanadin hakan.

Da zai tafi ya ajie mata envelope mai dauke da dalar amurka, wanda idan a kiyasin naira zasu iya kaiwa dubu dari biyar.

Ya yi ta mata godiya tare da cewa "Na so kwarai ace na aure ki, sai dai jiya Mum 'dina ta tabbatar mini Yar kanwarta ta zaba mini, bijirewa ta kuma na nufin lalacewar al'amurana, na sani har na mutu ba zan daina son ki ba, sannan tsayiwar ki, kadai kan mahaifina ya tabbatar mini da cewa tabbas baki manta ba, duk irin kaini 'kasa da Mk yake ko wa, da ya yi"

Tana dariyar wai ya manta sunan Mk ta rako shi har wajen da ya ajiye motarsa, Suka sake tsayuwa a wajen adalilin ya ce zai shiga gidan Madugu wurin abokin karatunsa a Egypt.

Suna tsaye motar Mahmoud ta tunkaro su, zuciyar Sa'a ta buga, kafafuwanta suka dinga barazanar kada ita. Mk dake gaban motar ya ji tamkar ya sume, mussaman da ya tabbatar Khalil ne wannan zabgegen saurayin ya girma sosai.

Suka hada ido amma Khalil sai ya dauke kai bayan ya galla masa kallon raini tamkar shekarun baya. Har zuwa yau bai ji zai iya kallon Mk a matsayin malamin sa ba, sai dai a matsayin dan fashi a soyayya.

Wannan kallon ya sake rikita Mk, domin yasan na rainine tsantsa. Yayin da Sa'a bugun zuciyarta ya tsananta, tana raya ina ma motar Mahmoud ce mai tint?

Mai gadi ya bude musu gate Mahmoud ya ja suka shiga, ya juya ya ga Mk yana wani irin numfarfashi, tamkar ya samu attack na asthma.

A farko 'karfi ya dauka abin Wasa ne sai da ya ga Mk ya sume sai kawai ya ja motar a kidime zuwa asibiti.

SURAYYA DAHIRU.
✍️✍️

*HALIN YAU*!

*NA*

*SURAYYA DAHIRU*.

*Lafazee writers*

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*

*GAISUWA GA DUKKAN MAMBOBIN*
*HALIN YAU FANS*
*_Na gode sosai da yabawar ku, comments din ku na matu'kar sa ni Nisha'di, Allah ya bar zumunci_*.

102-103.

Suna tsaye suka ga mai gadi ya bude musu kofa, Mahamud ya fito a guje kana ganin tukin da yake yi kasan babu sukuni a tare da shi.

Hankalin Sa'a idan ya yi dubu ya tashi, Khalil ya kula da yanayinta ya ce, ina son ki sosai, ke kuma kina son wanccan wicked man din.

Ya'ke kawai ta yi, ba tare da ta ce komai ba.

Ya juya ya fara tafiya yana cewa" sai wani lokaci, muna godiya, kwarai da gaske".

Da azama ta juya itama tana jin tamkar ta yi ta zunduma ihu, ya ya zata yi ne?

Ta san ganin Khalil tare da ita means alot a wurin Mk.

* **
Suna isa Asibiti aka shiga da shi dakin agajin gaggawa wato (emergency). Likitoci suka rufu akansa ana kokarin shawo kan matsalar, tsawon lokaci kafin a samu numfashin sa ya dawo, sai dai ba dai dai ba, Dan haka dole aka saka masa na'urar sau'ka'ka zukar numfashi (oxygen).

Sai dare 'karfi ya sanar da Farida da Abbas halin da ake ciki.

Dukkansu sun yi jigum jigum a asibiti suna kallon Mk a kwance bai san wanda yake kansa ba.

Farida sai fama take da tissue tana goge hawayen da ya kasa tsayuwa a idonta, ta dade da sanin mijinta bashi da lafiya, ta Dade tana jiye masa shiga irin wannan halin, adalilin kullum yana cikin rashin sukuni, ta dinga jin haushin Sa'adah na kamata, ta tabbatar ita take son kaishi barzaku dan kawai ta musu biyu babu.

Hajiya kuwa sai da gari ya waye aka sanar mata, ta isa asibitin cikin tashin hankali, ta kalli yadda ya ke shimfide akan gadon asibiti, ya zabge sosai, dama ya dade a rame Amma yanzu ramar ta bayyana karara.

Haka suka tasa shi a gaba masu addu'a na yi, masu share hawaye na yi.

Sai da aka kwana biyu Baffa ya samu labarin ciwon Mk adalilin Bai ganshi ba, bai ga Mahmoud ba, haka Abbas, har shagon su ya je, anan ya samu labarin ai yana asibiti an kwantar da shi.

Akeel ne ya raka shi asibitin, ba karamin damuwa ya shiga da ganin Halin da Mk ya ke ciki ya yi ba.

Ya dinga yi masa addu'a yana tofa masa.

Har ya gama zamansa Mk bai farka ba, ya isa gida ya tarar da Innah a tsakar gida tana yanke farce, ta masa sannu, ya amsa, ya samu gefe ya zauna.

Ya nisa ya ce "Mutari ne bai da lafiya rabona da shi yau kwanaki uku kenan, dazu na je shagonsa jin ba'asi sai ake fa'da mini bai ji da'di ba, na je na gano shi, Amma ban ji da'din ganin sa ba, domin gaba'daya yana kwance tamkar gawa.

A sanyaye Inna ta ce "Assha Ubangiji yasa zakkar jiki ce".

"Ameen dai! Amm an tabbatar mini jininsa ne ya hau fiye da 'kima, na san baya rasa nasaba da bijirewar ku, Ayyah Salamatu ba zaku yiwa yaron nan sassauci ba, ko bai ci arzikin kowa ba, ya ci na tilon 'dansa mana".

A sanyaye ta ce "Àllah zai bashi lafiya, Iyah har karamin hauka ta yi, amma da aka yi hakuri ai gashi nan ta mike, har ya zama tamkar ba a yi ba, shima zai tashi ne".

Ran Baffa ya fara 'baci da lamarin ta sosai, Amma sai ya mike ya fice domin ya san cigaba da zamansa a cikin gidan yana nufin rikici mai tsanani a tsakanin su, abin da ba zai iya tuna ko sau nawa suka yi a tsayin rayuwar aurensu ba.

Sa'a da ke daki take jiyo su, hankalin ta yayi tashin gauron zabi, ta da'de tana wasi-wasin fishi su Dr 'Karfi suka yi, ko kuwa jikin Mk ne har yanzu domin yadda ta ganshi kwance a gaban mota da irin gudun da Mahmoud ya yi ta tsorata.

Gashi kwana biyu bata sake jin su ko a waya ba.

Hawaye ya 'balle mata, ta tuno sadda yake ce mata, yana jiye mata fargar jaji, yana jiye mata kar 'danta ya zama maraya.

Ta kasa fitowa waje dan idan Inna ta ga tana kuka akan Mk to kuwa ta kade har ganyen ta.

Ta rasa inda zata tsoma ranta.

Washagarin ranar sai ga Baba Isa sun zo har da su Baba umaru, daga asibiti suke, ganin Halin da Mk ya ke ciki, yasa suka ji tausayi, suka saka Mahmoud ya kawo su, su zo ko Allah zai sa a samu yarinya ta huce .

Amma wani abu da Sa'adah ta kasa gane menene ya daure mata baki da zuciyarta, ba abin da take hange sai Mk da Farida cikin mayafi guda, duk tambayar da suke yi mata ta kasa amsawa sai kuka take yi, tana satar kallon mahaifiyarsu.

Hade ran da Inna ta yi, yasa ta ce "Na yafe masa, amma ni bana sonsa da aure".

Jikin su Baba Isa ya mutu kwarai da gaske, dan haka suka ha'kura domin dai sun san yarinyar ta hadiyi ba'kin ciki kala kala.

Ran Baffah bai ta'ba baci irin na yau ba, gaba'daya ya ji Sa'adah da mahaifiyarta sun kunyata shi, sun tozarta shi.

A daddafe ya sallame su, ya dawo gida, ya dinga surfawa Inna sababi, yana fa'din "Ban san ladabin karya kika yi mini ba, a tsawon shekarun da muka kwashe ba sai yanzu".

Ya nisa ya ce "wallahi Salamatu kin yi 'karko irin na kifi ace wai ke kika raba mini gida zuwa jami'iya biyu, kin hana yarinya zabin zuciyarta, saboda son rai irin naki.
Yanzu haka yaro yana gadon asibiti rai a hannun Allah! Tabbas idan ya mutu, ke ce sila, kin bada muhimmiyar gudunmawa wurin kisan rai"

Ta fara kuka ta na cewa "Eh ai da yake shi ka damu da lafiyarsa, shiyasa kake akilon samo masa mafita, amma sadda ta dinga zabura tana surutai ai duk ka manta. Ina nan akan bakana bana son Muutar da Iyah".

Ya hassalo ya ce "to kuwa ba zan iya zama da ke da wannan bakar zuciyar ta ki ba, har kina iya buda baki kina ce wa wanii mai ru'ko da 'Kullaci, to ke ai zuciyar ki tafi ta kafiran farko ma tauri".

Da kuka sosai ta shige 'daki ta fara tattara kayanta tana fa'din "akan Iyah ta komawa Muutar gara na ha'kura da zaman tunda ka ce ba zaka iya zama da ni ba".

Sa'adah da take tsaye tana kukan bacin ran yau akanta iyayenta da bata ta'ba ganin sunyi ko da musu ba, suke wannan tashin hankalin.

Ta bi Inna daki tana bata hakuri amma ko kallonta ba ta yi ba, sai hawaye take yi, tana cigaba da hada kayanta.

Baffa ya shigo ya ce "daina ha'da kayan ki, yau shekaru arbain har da uku da auren mu, kike tunanin dan na rabu da ke zan tura ki gidanku? Ai ni ba azzalumi bane, ba zan karar miki da karfinki da kuruciyarki sannan na sallama ki ba".

Ya nisa sosai ya ce "mahaifiyata ita ta sha nono ta barwa mahaifin ki, kenan a ko ina ni mai tsaya miki ne, ba me tozarta ki ba.
Ni ne zan fita na barki miki gida, ki yi yadda kike so da yaranki, tunda ni ban isa na yi iko da su ba, kin riga kin zama 'Yar birni, son ya'ya kawai shine a gabanki ba tare da tunanin abin da zai biyo baya ba".
Chapter 95 · 0% Book details