← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 113

Sashe 53

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin Sumayya ya sake mutuwa, shiyasa kwana da kwanaki tana gwada layin Iyah baya shiga, ta damu kwarai da rashin jinta, sai da Inna tace mata, lafiya ce take buya, Ni kaina an kwana biyu bamu gaisa ba, da kuma wata matsalar ce ai da mun ji, tunda mijinta kusan kullum sai yazo unguwar, kowacce juma'ah kuma zai shigo ya gaishe ni, ya bar Jawad sai zai tafi ya zo ya dauke shi, na fahimci Iyah! indai naji ta shiru haka, to cikine da ita.

"Yanzu kana gida ne?"

Ya girgiza kansa tamkar tana ganinsa "Ina makaranta, sai da yamma zan koma".

Ai kuwa da yamma yan isa gida ba jimawa, Kiran Sumayya ya fado wayarsa, bai dauka ba, ya bawa Jawad wayar tare da cewa" sauri ka kai mata, Maman Gombe ce" dake tuni sun bar Jos tun shekaru biyu da suka wuce.

Da gudu kuwa Jawad ya fita sai dai kafin ya isa inda take ya danna ok, ya fara yiwa Sumayya surutu, ita kuma ta biye shi, duk da ba komai take fahimta a hirar tasa ba.

Fada sosai Sumayya ta yiwa Sa'adah, ta yi shiru tamkar tana jinta, sai da ta gama ta saka mata kuka tana fadin
"Yana zaune da yan'uwansa kalau, amma ni yana ba'kin ciki da hadin kan dake tsakanina da ke, Ina zaune da shi ne kawai, amma ba irin wulakancin da baya mini, ya fifita farin cikin yan matansa akaina, ya koyo wata dabiar da ba tasa ba, ko kukan jini zai ga inayi ba ruwansa, shine har ya kawo karata?".

Mamaki ya kama Sumayya tace "Ni kike fadawa wadannan maganganun? Eh na tabbatar Mijinki ba karamin ha'kuri yake da kaifin harshen ki ba, amma ki saurare ni da kyau, wlh idan baki canja ba, za ki jefa kanki a nadama mai yawa, wato ke har yanzu baza ki yi hankali ba? Kowacce mace da akwai inda take ha'kuri, ance miki auren wasa ne, ke naki ma wallahi ba matsala bace, kawai dorawa kanki kika yi, Ina ruwan ki da yanmatansa, ko aure yace zai kara Ina ruwan ki? Tun zuwan ku Jos na lura sai kin koya masa bagarar da lamarin ki".

"Dan ke mijinki ba mai hayaniya bane, ba mai kule kulen mata bane shiyasa kike ganin bani da matsala" Sa'adah ta fada a tunzure.

Cikin bacin rai sosai Sumayya ta ce "shikenan ki yi duk abin da kike so, ya dauka ina da wata kima a wurin ki! shiyasa yake ganin zan iya muku sulhu basai iyayen mu ba, amma tunda ban isa ba shikenan! Rayuwarki ce, kina da ikon yin duk yadda kika so, sai dai ki sani wadda bai ji bari ba, ba zai ki ganin hoho ba". daga haka ta kashe wayar ta, ta bar Sa'adah ri'ke da waya tana kunshekin kuka.

Jikinta ya yi sanyi, tana Jin Aunty Sumayya uwace ta wuce ta yi misayar yawu da ita! Dan haka sai ta sake kira, Sumayya ta daga tana cewa "menene?" Cikin kuka Sa'adah tace
"Na ji! kiyi ha'kuri".

Sumayya da bata da zafi, tace "yauwa Iyata, ni nasan indai a cikin Innarmu kika fito ba zaki 'ki jin abin da na fa'da miki ba, saboda kinsan nan duniya bani da kamar ki, mu kenan iyayen mu suka haifa, ki daina duk abubuwan da mijinki baya so, ki kara hakuri, idan ma ke yake zalunta ki yafe masa, ki yawaita addu'a sai kiga Ubangiji ya warware miki komai, fiye da yadda kike zato! Yanzu abin da nake so da ke, ki bashi ha'kuri, kar kuma a sake tada maganar koma wacce iri ce".

Sai da Sa'adah ta ja majina murya na rawa tace "Anty shine fa yake fishi da ni, yake ta share ni, ba abin da banyi dan mu shirya ba, ya ki bani fuska, kuma sai ya kawo karata?"

Cikin rarrashi Sumayya ta ce "bafa kararki ya kawo mini ba, nasan dai kuna zaune kalau ba zai barki ba waya ba, nice dai na tambaye shi Kuna lafiya kuwa, yace na miki magana baya son ya shigo da Baffa cikin matsalar, iya haka ya fada min wallahi".

"To Anti na ji fa'danki, amma shima ki fa'da masa idan ina kuka, ya daina cemin na dame shi da kukan banza, ko na iyashege, ya bar komai ya rarrashe ni".

Sumayya ta 'kunshe dariyarta tace "Zan fada masa, amma ki bashi ha'kuri first, nasan kafin ki yi tuba sai tura ta kai bango, kullum ina fada miki hakan sifface ta girman kai.

"Anty sanin da, kika mini, wlh na bashi hakuri, ta hanyoyi da dama, ai ba sai na fada da baki ba, shi da kansa yasan na bashi hakuri, kawai dai ya runtse idanuwansa ne".

"To yanzu ki fada da bakin ki yasan Ina da mutunci a gurinki, idan na fada miki zaki ji! Idan kuma kin ki, shikenan, kin wula'kanta Ni, kin wula'kanta kanki".

Da haka Sumayya ta risinar da Sa'adah, sun dade suna magana har sai da kudin wayoyin ya kare tas, sannan suka ha'kura.

Da kanta ta kai masa wayar, duk da Jawad na cewa ta bashi ya kaiwa Malam! ta bashi wayar ta zauna gefen gadon Sannan tace " Malam ka yi hakuri dan Allah".

Idonsa a rufe, bai bude su ba yace "Ni dama barcin da kike hanani yi da daddare ne, bana so, hakuri na zai iya :kwacewa, idan zaki yi kukan ki ban hana ki ba, amma pls stay away from me, na riga na gane ban da mutunci ko ka'dan a gurinki, zaki iya zagina kan ki tsaye, zaki iya fada min duk maganar da ta zo bakin ki, na zuba miki ido ki yi duk abin da kika ga dama, amma ki jira sakamakon zagin da kika min, na rantse miki! ba zai tafi a banza ba".
Ya karasa da rawar murya saboda 'bacin rai.

Hankali Sa'adah ya yi mugun tashi, mussaman yadda ya yi maganar da dukkan zuciyarsa, ta zuba masa ido tana ganin yadda yake numfarfashi tamkar wadda ya yi gudun fanfalaki, dan tsananin bacin rai.

Ta zame ta durkusa a jikin gadon ta ru'ko hannunsa "ka yi hakuri, ba zan sake ba".

Ya bude ido da suka yi jah yace "wallahi za ki sake, ba dai kin bada kofar da wasu suka shigo cikin rayuwar aurenmu ba? ba kin fi gaskata maganganunsu, sama da nawa ba, nace ban son su zo min gida, kin nuna ban isa ba, saboda kina jin isar gidan na ki ne, na sha jan kunnen ki akan kaifin harshen ki, amma kullum sake koyon dabarun ba'kaken magana kike yi, ki rubuta ki ajiye wañnan *HALIN YAU* din da suke cusa miki, kina dauka babu nazari bare tsinkaye, ba inda zai kai ki sai nadama, na fara gajiya da halin ki, hakuri na ya fara kaiwa geji gaskiya, Menene bana miki da kike wulakanta ni haka?"

Jikin Sa'adah ya yi wani irin nauyi, zufa sai karyo mata take yi ta ko Ina, ta kasa bude baki ta yi magana, dan hatta harshen ya mata nauyi ainun, hawaye kuma tamkar an bude famfo, Jawad da yake tsaye yana kallon su, ya karaso ya fara goge mata hawayen, Yana cewa "biskit za ki ci? ko Malam ne ya doke ki?"

Ta kasa magana kamar yadda hawayen ya ki yankewa,ya zuba musu ido yana ganin yadda Jawad ke goge mata hawayen,yana kuma fa'din ta yi shiru, zai goyeta a kekensa, wani irin abu mai kama da tausayi ya tsirga masa yana ayyana karfin soyayyar da ke tsakanin uwa da 'da.

Murya a dashe Mk yace "ki ci gaba da kukan, so kike ya 'kullace ni, ya zaci kamar Ina gallaza miki ne, idan girma ya cimmmani ya'ki jin 'kaina"

Da sauri ta dago manyan idanuwanta ta zuba masa, a fili akan idonsa tace " Malam plz ba kai bane, ka dawo wancan Malamin nawa! mai yawan yi min afuwa, mai tausasa mini".

Ya mayar da idonsa ya rufe yace "shikenan ya wuce, dauki "danki ku tafi gurinki barci zan yi".

"Ka yafe mini?"

"Nace ya wuce" ya fada a gajarce.
Taja hannun Jawad! amma yaron ya coge alamun ba zai bita ba, ta tsaya tana kallon sa ya hau gadon ya kwanta jikin Babansa, Mk ya rungume shi yana ji a ransa shima fa Jawad na sonsa sosai😀Mk manya.

Kwana biyu, Sa'adah ta sauko, tana komai yadda ya kamata, ta bangaren Mk shima yana iyakar kokarinsa na bai sake yin wata maganar ba, zai ci abincinta, idan ta masa magana, yana amsawa kadaran kadahan, kawai a shimfida ne ba ya kulata, ta gama shure shurenta, ya yi biris, duk da shima fama yake da shan lemon tsami.

Tana zaune tana tunanin mai zata masa ya ta'ba ta, hawaye na siraro mata, saboda yadda abin ya dagula mata lissafi, mussaman yadda ta san shi da rashin ha'kuri a wannan harkar, idan ta hasaso ko a waje yake samu sai ta ji tamkar ta sume, ta sake ramewa ta yi zuruzuru, kamar ance kunna radio, aikuwa nan ta ji sanarwa a gobe litinin hukumar zartarwa ta kwalejin tarayya ta kano (F.C.E.) zata rufe yin registration.dan haka duk dalibin da bai yi ba ya hanzarta kafin a rufe.

Ta yi shiru, ta tabbatar Malam yasan ranar da aka bude dan farawa, dan kuwa yana da aboki da yake aiki a gurin, duk da ba lakcara bane.(Non academic staff)ne.wani sashi na zuciyar ta yace kika sani ko ya biya miki ne? Da haka ta samu sukuni kadan.

A ranar bai dawo da wuri ba, dan haka ta danne komai ta barshi ya gama komai cikin nutsuwa, sai da suka kwanta ta bijiro da maganar da ta ji a radio.

Tsawon lokaci ya mata shiru, zuciyarta ta sosu da wulakancin nan da ya tsira, ashe haka yake jin rashin dadi idan ya mata magana ta share? ta daure tace "kana tare da ni kuwa?".

"Ina jin ki, na sani, har na biya miki, yasa hannun ya ja drowar gefen gadon ya fiddo da teller ya nuna mata, farin ciki ya mamayeta, kafin ta yi magana sai taji yana maganar da ta kasa gane manufarsa.
Chapter 53 · 0% Book details