← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 113

Sashe 58

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai yi nauyin baki ko kunya ba, ya ce "Zan zo na kai ku Baffah amma ita daga baya zata je".

Godiya sosai Baffa ya masa tare da fadin "ko bata je bama ai kai kaje , ka wakilceta".

Haka akayi tafiyar Sa'adah ko labari bata ji ba, a ranar Baffa suka juyo da Mk, da kuma Hajiyar Bichi da ke ta bisu, suka bar Inna dan ta kula da Sumayya, kafin Umma fanshekara ta je sai Innan ta dawo.

Ganin da innah ta yi har washagari Iyah bata 'kira ta yi jajen mai jiki ba, sai hankalin Inna ya tashi tana tunanin ko itama ba ta da lafiya ne?

Tana Shirin 'kiranta, sai ta 'kira suka gaisa, mamaki ya sake kama Inna ganin ba alamun ta samu labarin halin da 'yar'uwarta take ciki, dan haka sai tace "mijinki bai fada miki Ina Gombe ba?"

"Wallahi bai fada mini ba, wani abin ne ya faru?" ta tambaya a kidime.

A sanyaye Inna ta ce "yayar taki aka yiwa tiyata ga yaro nan lafiya lau, sai itace bata Jin dadi, amma dai da sauki".

Cikin muryar kuka ta ce" shine ba ki fada mini ba Inna?".

"Mijinki ne fa ya kawo mu, jiyan suka juyo da Baffanku, Kinga ai bana yi zaton ba ki ji ba, duk yadda akayi ba zaman lafiya kuke yi ba Iyah, tunda da bakinsa yace baza ki zo ba, sai muka dauka ko kema ba Kya jin dadi ne ya rufe mana, har da Hajiyar Bichi muka zo, duk jiyan suka juyo".

Kuka kawai Sa'adah ta ke yi, irin kuka na rashin madafa, sosai kukan ya ta'ba Inna, tashin hankalin ta ya 'karu ga na Sumayya da ta ke kwance bata san wadda ke kanta ba, ga na Iyah da ba tasan ha'ki'ka in matsalar ta ba.

A sukwane ta kira Baffa tace lalle akwai matsala tsakanin Iyah da Mijinta, cikin rashin daukan maganar da muhimmanci ya ce "Mijin ta bai kawo 'kararta ba, ita ba ta ce ga laifinsa ba, sai kawai naje na hau bincinkarsu, tunda sun iya 'boye sirrinsu, sai a bisu da addu'ar Allah ya daidaita su".

"Ka shiga maganar nan, da alamun fa abin babba ne, hatta zuwan nan da ya yi Gombe bata sani ba, kar a zuba musu ido fa".

"To" ya ce mata a gajarce ya katse wayarsa! yana cewa lamarin mata yana da ban mamaki, kawai dan kina so a tursashi ya barta taje inda baya so taje sai kice naje na shiga tsakanin su, duk tsawon lokacin da suke tare waya ya san yadda suke zaune?

Haka kwanaki suka yi ta shudewa a cikin Wannan hali tsakanin Mk da Sa'adah, kullum 'kara nesanta kansa yake da ita, zuwa yanzu da suka cika sati biyu cikin wannan halin, wadda ko a mafarki bata yi zaton zai iya shareta har haka ba, domin tun ranar da ta yi wannan katobarar bai sake bin takanta ba, asalima ta lura bai son ganinta ne har zuciyar sa, tana ganin idan ya dawo a gaggauce yake shigewa dakinsa ya rufe kofa, hakanan idan zai fita a hanzarce ya ke ficewa, duk yadda bai son ya ji kukan Jawad amma a yanzu duk kukan da zai masa ba ya tsayawa ya bi ta kansa.

Ta shiga damuwa da tsoro irin wadda bata taba shiga ba, tsoron ta 'daya idan iyayenta suka ji mai ya jawo wannan tashin hankalin, wanne irin kallo zasu yi mata,?

Ta 'kudiri aniyar yau zata bashi, ha'kuri ta kuma nemi ya barta taje ta gaida Aunty Sumayya.

Haka akayi, taran dare ta yi wanka, ta shirya cikin kwalliya ta burgewa, tana jin dirin motarsa da kiciniyar bude gate, ta fita a hanzarce ta shiga kicin mai ma'kwabta ka da 'dakinsa ta tsaya.

Ai kuwa ya shigo da sauri, ganinsa rungume da kayan wankinsa da ya kai wanki, jikinta ya sake yin sanyi, komai zata yi masa, idan zai kai wanki zai shiga har 'dakinta ya hada kayanta akan nasa ya kai musu wankin amma banda Wannan karon.

Kafin ta yi yunkurin shiga dakin nasa sai ta ga ya fito ya fita da alamun ya yi mantuwane, dan haka sai ta yi wuf ta shige 'dakin, yana shigowa kuwa ya rufe 'dakin bayan mukulli har da sakata ya sanya.

Yana shigowa ya ganta lafe jikin wadirof, ga mamakinsa sai yaji kwalliyar da ta yi, bai ji komai na burgewa akanta ba, hakanan kamshin ta da ya cika masa hanci bai yi tasiri a jikinsa ba, kyakkawar fuskarta da ke sanya shi nisha'di, a yau ba'kanta masa rai ta yi, hakanan surarta da ke jefa shi cikin shauki, a yau takaici ya ji ya maye gurbi.

'Bacin ransa ya dawo sabo fil tamkar yanzu take gasa masa maganganun da suka zame masa tamkar 'digar dalma a zuciya, suka yi awon gaba da kaso mai yawa na matsananciyar soyayyar da yake mata.

Baice mata komai ba, ya shiga rage kayan jikinsa, ya shige wanka, tana tsaye ya fito ya shirya, ya tada sallar shafa'i da wutiri.

Sai da ya idar ya zauna bakin gado ya kalleta, ya ga duk ta takura, ta susuce, ta lalace, idonta ya fada alamun dai tare suke 'dan'danar 'bacin rai.

Kafin ya yi magana ta rigashi! Ta tsugunna ta ri'ke gadon ta ce "Dan Allah Malam ka yi ha'kuri, ban taba jin nadama irin wadda nake ciki ba".

"Ba ki mini komai ba, abin da ke zuciyarki ki ka amayar, sai dai ina so ki sani wallahi ba ki fara nadama ba, ina tabbatar miki za ki shiga NADAMAR da ta zarce wadda kike ciki, da kinsan yadda na tsani ganin ki da hakan ka'dai ya isa ya saki nadama, da kinsan yadda kika wanke kanki a zuciyata da kin gane asarar da kika yi ba ka'dan bace".

Kuka ya goce mata, ta rarrafo da nufin ri'ke shi, ya zabura ya mike tsaye cikin bacin rai ya ce "idan kika yi kuskuren sa hannun ki a jikina, na rantse miki sai na miki abin da za ki gamsu ba ki da sauran 'kima a gurina. domin duka zan miki irin yadda ake na'dawa 'yantattatun matan bariki idan angama cin moriyar su".

Kukan ya tsaya mata! da gaske ta yi kuskure, irin kuskuren da ake yi sau daya amma sai an nemi hanyoyi gyara dari bai gyaru yadda ake so ba. daga jiyo magana a bakin shedanun mata ta ara ta yafa, har ta zo ta fa'dawa mijin aurenta wadda da gaske samun irinsa zai yi wahala.

Ta zauna 'dabas tsakanin gado da wadirof ta dinga kuka, mai cin rai, na tsantsar nadama.

Daga inda yake ya ce "Ta shi ki bar mini 'daki ban bukatar ki a cikinsa".
Ta kasa koda kwakwkwaran motsi. tace "ka yi hakuri ba dan ni ba, ka dubi girman Allah ka yi hakuri".

Jikinsa ya yi sanyi yace "Na ji, amma dai tashi ki fita, ina bukatar ka'daici ne, duk sadda nake da bu'katar ki a dakin I will let you know".

"To ka daina rufe 'dakin, na yarda duk sadda na zo ka kore ni, amma ka daina rufewa".

Ya zuba mata ido yana jin takaicinta na sake kama shi, amma da yake so yake ta fita ya shaki iska marar takura sai yace mata to a takaice.

Ganin ya amsa mata sai ta tashi ta bude 'kofar ta fita tana fadin " ka yi hakuri, ka yi barci mai cike da walwala".

Ya bita ya rufe kofar, ya dawo ya karanto adduar barci ya kwanta.

Washagari da sassafe ta shirya masa abincin karyawa ta zauna zaman jiran ya bu'de 'kofar, ai kuwa yana budewa ya ganta da tiren abinci, a bakin kofar dakin, yasa kai zai wuce ta ce, " Ina kwana?"
Ya amsa a gajarce, "ga abinci na gama". ya girgiza kai ya ce
"ki daina wahalar da kanki wurin yin abinci saboda Ni, na riga da na 'yanta ki daga dukkan yi mini hidima kowacce iri ce".

"Cikin rawar murya ta ce "kace fa ka yi hakuri?"

"Da ban yi hakuri ba, da baki ganni akan 'kafufuna ba, da ina can akan gadon asibiti saboda ba'kin cikin ki, da ban yi ha'kuri ba, da ban tsaya ina miki magana ba".

Ta goge hawaye ta ce "ka kara hakuri dan Allah nasan na yi ba dai dai ba".

Ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba, ya fara tafiya, da azama tace " Malam! Umman fanshekara gobe zata tafi Gombe, dan Allah ka bar ni mu tafi tare, ni sai na dawo ko jibi ne".

Ya juyo a zabure tamkar wadda ta fadi mugun abu ya nunata da yatsa ya ce" dama nasan duk wannan saukar da kan da kika yi, kina da bu'kata ne, ba kya tashi mutunta ni, ko kwantar mini da kai sai kin ganni da kudi, ko kina son na barki kije wani guri".

Cikin kuka sosai ta ce "Haka ka dauke Ni?"

"Kin wuce hakama ke kam, saboda ke ciki ce mai manta kyautar jiya, mai manta alheri, da kina da hankali, da baki cemin za ki tafi yawo Gombe ba, kawai tafiya za ki yi kanki tsaye".

Ta zuba masa ido ta ce "dubo Anty Sumayya ne yawo?"

A kausashe ya ce "ke kika san Sumayya, ni mai na hada da ita! ko dole nace?"

Tashin hankali 'baro 'baro ya bayyana a jikinta gaba'daya, lalle da gaske Mk ya shiryawa tashin hankali iri iri, wai Anty Sumayya ce yake fadin sunan ta gatsal, duk da ya girmeta da shekaru biyu amma Anty yake cemata, sannan kuma har yana cewa mai ya ha'da da ita?.

Ta kalleshi baki na rawa ta ce "Dan Allah Malam ka yafe mini, mu zauna lafiya ba zan iya kar'ban wannan tashin hankalin daga gareka ba, na rantse maka ba zan kuma maka laifi ba, zaman lafiya zamu yi, fiye da yadda ka ke so".

Ya yi murmushi ya ce "na la'anci zaman lafiyar da ki ke so mu yi Sa'ade, zuciyarki bata da alheri, kwakwalwarki ba ta da tsinkaye, harshenki yafi na maciji dafi, ba sauran zaman lafiya tsakanin mu, idan har kika zauna lafiya da ni ban yafe miki ba".
Chapter 58 · 0% Book details