Sashe 102
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya mata shiru ya dauki ledar zogalensa ya fice, tunda ta riga ta rantse ba zai kwanta ba.
Ya fita yana fa'din "Na tafi Hajiya, Sa'a ta ri'ke ki gam, ta tattare komai a gunki, ai shikenan, nima sai na hada kai da Farida baiwar Allah".
"Komai zaka fa'da, ka fa'da ni Farida bana ganin laifinta, bata mini komai na laifi ba, Nima kuma na sani bata kuka da Ni, sai dai kuma ko kai wallahi baka fi mini Sa'a ba".
Ya fita yana cewa "ai shikenan sai ta zuba ruwa a kasa ta sha, ta nema ta samu fitinanniyar yarinya kawai".
****
Sai da ta aka yi sallar la'asar sannan suka bude kayayyakin da Mk ya jido Mata, wadda kayan shayi, da sabualan wanka mai tsananin gyara fata na *OLAY* *(quench)* ya hado mata setin su har da bath gel dinsa, da mayukansu.
Sai kayan ciye ciye na gwangwani kala kala tamkar zata bude kanti.
Indomie da kwai suma ga su nan birjik.
Inna ta yi galala ta ce " ban gane wannan siyayyar ba, kuna nufin haka zaku zauna, ba za ki tare ba? Dan na ga wannan kayayyakin yana nuna cewa ba yanzu zaki tare ba".
"Eh Innah ni na ce ba yanzu ba, domin ai ban shirya komai ba".
Ta nisa ta ce " Kika yanke hukunci babu shawarata, ko ta Yayarki saboda kawai kin zama uwar kanki! Ki sani to ba dabara kika yi ba, tunda an riga an daura aure, ai ba abin da shari'a bata bashi dmaa ba, bijirewar umarninsa kuwa ai kin san yana nufin tsinuwar mala'iku ne akan ki.
Haka kawai sai kin janyowa kanki ya gama zumudin ki, a titi, ke dai naga sadda zaki yi aiki da lura".
Kunya ta kama Sa'adah! Amma ta waske da cewa."To yanzu Inna sai a sake kai ni ba kayan d'aki alhalin yanzu Ina da kishiya?"
Ta fa'da a shagwabe.
Dake Innar mace ce nan da nan ta yarda da ra'ayin Sa'a na bai kamata ta je babu kayan d'aki ba alhalin tana da kishiya diyar masu kambun susa.
Ta nisa ta ce " Bari Baffan ku ya zo sai a siyar da dayan filin da ya rage, sai ki hada da albashinki na watan nan tunda ya raba tsakiya, ki yi abida ya sauwaka ayi tariyar nan cikin girma da arziki".
Ta turo baki gaba Inna ki bari dai nan da wata uku, kinsan ai na ce na barwa Baffah kyautar filin, yanzu kuwa ai ba zan koma na ce na fasa ba".
To kayan Baffanki ai naki ne, Ina jiye miki tsiyar namiji Iyah! Muutar din nan fa na riga da na gane shi bashi da kunya ko ka'dan, ba abu mai wahala bane a gidan nan ma, ya yi abin da ya ga dama tunda Baffanku ya daukake shi ba ka'dan ba".
****
Kwanakin mako da zuwan Mk wurin Sa'a har yau bai sake zuwa ba, bai kuna yi mata waya ba, abin da yake ta cin ranta kenan, ya sake tunzurota, idan bata tare ba, ai dai tana da hakkin ya duba lafiyarta, wato ya kawo mata kayan abinci saboda ita ci kawai ta sani da kwalliya.
A na cikin haka wata waki'ar ta kunno a jahar Sokoto inda aka samu matasa sun kasa ha'kurin hukuma ta dauki doka, saboda an tabowa musulmi inda basa iya ha'kuri matu'kar aka tabo wannan matsayin.
Dukkan hankalin musulmai a tashe yake an zuba ido, an kasa kunne domin aga irin hukuncin da za'a yiwa wadannan matasa.
Kungiyoyin musulmai kashi daban daban sai kiraye kiraye ake yi akan akaiwa matasan nan dauki.
Kungiyar lauyoyi musulmai reshen jihar Kano ta bawa wadanan matasa lauyoyi hamsin da suje su harci zaman kotun da za'a yi a gata, su kuma basu kariya.
Cikin wadanda aka tura har da Sa'adah.
Baffah da Innah sai murna suke yau ga yarsu zata je ta kare martabar Ma'aiki, ilimin Iyah bai musu da'di iri a wannan karon ba."
Da murna Baffah ya ce " yaushe zaku tafi?".
"Jibi zamu tafi, dan mu sami zaman kotun, tunda gata da sassafe za'a fara shari'ar".
"To ki 'Kira mijinki, ki sanar da shi, tunda dai ba zaki yi tafiyar bai sani ba".
Ta amsa da to badan ta so ba.
Tun yamma take kiransa yana gani, amma ya yi biris, bai dauka ba,sai bayan magariba wadda hakan ya sake fusata, Sa'a ta botsara.😄
Ya dauka, amma ta yi shiru, sanin da ya yi dabi'arta ce ba zata fara yi masa magana a waya ba. Sai ya ce "Ina jinki, na ga 'kiranki rututu, kin gama mini shirin ne, na zo na dauke ki.?"
Ba'kin ciki ya tokare mata wuya, wato shi a haka ya barta ma?
Ta daure ta ce "Dama Sokoto zani".
"Sokoto zaki je?"
"Eh" ta amsa a ta'kaice.
"To ba zaki je ba".
Daga haka ya kashe wayar ya barta da waya a kunne.
Ba'kin cikin da ya turniketa ba'a magana.
Hawaye ya kwace mata.
A hakan Baffah ya shigo ya sameta, ta fada masa abin da Mk ya ce.
Baice komai ba, ya fita waje.
Ya 'Kira Mk a waya, ya ce "lallai ka zo ina nemanka".
Mintina ka'dan ya iso tunda dama yana cikin shagonsa.
Ko gama gaisawa ba su yi ba.
Baffah ya ce "Iyah ta ce wai ba zata je sokoto ba?"
Ya sauya fuska ya ce "Eh haka na fa'da mata Baffa?"
Ai kuwa Baffah ya dauki salati yana fadin "Lallai kuwa, ka bani mamaki, ana tsayawa garabitin mutane a gaban shari'a, balle a taba janibin Ma'aiki. Ai kuwa shine mafi tsayawa a kare darajarsa."
"Da wata irin murya mai nuna mutun na wurin da zai yi shagwaba son ransa.
Mk ya ce "Baffah sanar mini fa kawai ta yi, ba wai izini ta nema ba".
A wannan karon ko ka'dan Baffa bai karbi uzzirin Mk ba, kawai umarni ya bashi akan lallai ya barta taje ta wakilce su, wurin bawa Ma'aiki kariya.
"Shikenan Baffah zata je, amma ban yarda ta yi tafiyar nan cikin kungiya ba, ta jira zan zo na kaita, idan sun kammala na dawo da ita"
"Yauwa Ubangiji ya maka albarka, ya kore shaidanun da suke ta tunzuraku, Suka 'ki su barku ku gane kun girma".
Mk Yana dariya ya ce "itace ai yar burutsa".
Baffah ya taya shi dariya sosai ya ce "Kai kuma baka iya rarrashinta ba".
"Hmmm Baffah ai ba zaka gane ba".
***
A lokacin da Baffah yake bayanin Mk ne zai kaita, Inna hankalinta bai kwanta ba gaba'daya, amma ba yadda za'ayi ta hana ta zuwa wannan shari'ar domin ba karamin daraja bane ace ka samu damar bawa Annabi kariya. Sannan kuma mijinta ne da shari'a ta bashi damar ya tafi da ita duk inda ya so.
Yayin da Sa'a ta ji takaicin wulakancin da Mk yake mata, zata bishi suje, Amma ko shine 'kuda wurin naci sai dai ya kalleta kawai, ba zai yiwu ya shareta na sati guda, sannan yanzu ya ce "tare zasu tafi ba".
Haka ce ta kasance lafiya Lau suka isa Sokoto. A hotel ya kama musu daki, ya dinga tuno moment dinsu a tafiyar da suka yi Abuja, a wanccan lokacin ba karamin hutawa da soyayya Suka sha ba, amma wannan karon ta yi kicin kicin da fuska, ko kallonsa bata yi.
Haka suka kwana! da wuri suka nufi kotun, ta shige cikin tawagar lauyoyi, shi Kuma ya zauna a sahun masu kallo, duk kuwa da an tsaurara matakan tsaro kwarai da gaske.
Da azahar suka bar kotun, saboda yadda aka 'daga Shari'ar zuwa wattanni biyu masu zuwa.
A hanyar su ta komawa ya ce "ba wadda zaki kaiwa ziyara ne a Sokoto?".
Fuska a daure ta ce idan ina da su kaini zaka yi ne?"
Da sauri ya ce "Eh Mana ranki ya Da'de, to menene aikina idana ba direbanki ba?"
Ta tura baki ta ce "Humaira Suraj da muka yi F.G.C anan take aure sai dai bani da contact dinta".
"Amma bari na kira uwar dakina idan tana nan ta mini kwatance muje mu gaisheta".
Da kulawa ya ce "Wacece uwar dakin ki ?"
Da murmushi ta ce "uwar marubuta, da makaranta da kuma marubuta masu tasowa, Umman mu Hajiya Saliha A.A Zaria."
Dariya sosai Mk ya saka tare da cewa dadina da ke ri'ke alakawari! Na tuno sadda kike karanta mini littafin Yarda da kaddara kina fa'din yadda Abba lawal yake yiwa Asama'u zan dinga yi Miki. Dole kam muje nima zan gaisheta, domin littafanta no yasa na samu tagomashi a wurin Sa'ade nah".
Ta yi masa shiru.
Ta fido da waya bugun farko Umma ta dauka, tare da cewa "maraba da diyata Sa'adatu".
Soasai Sa'a take jin da'din karamci da mutuntata Dan adam da Umman Sokoto take yiwa masoyan litttafanta, komin 'karancin shekarun mutum kuwa.
Cikin farin-ciki Sa'a ta ce "Gani a Sokoto, kuma ina kan hanyar zuwa gidanki dan gaisuwar girma.
Dadi ya kama Hazi'kar marubuciyar mu ta ce "na gode miki Sa'adah, ubangiji ya kawo ku lafiya.
Haka kuwa Mk ya tsaya ya tambayi adireshin da ta turo musu, ba wahala suka isa.
Murnar da Haj Saliha ta yi, ba yar kadan bace, a lokacin Sa'a da Mk suka gane ashe alherinta da suke ji a waya ba komai bane, sai ka ga zahirinta zaka san ita din Ummul khairi ce.
Ta dinga yi musu nasiha da jan kunne kan hakuri, da kuma gwaggaban ladan da mai yinsa ke rabauta da shi.
Da zasu ta fi ta bawa Sa'a abu a leda da ba tasan ko menene ba, ita kanta Sa'a da aka bata, bata kula da sadda ta ru'ko hannuta ta saka mata ba, saboda tsananin yadda Umma ta iya karrama dan Adam.
Suka tafi cikin Jin da'di kusan saboda nasihar da Umma ta yiwa Sa'a yasa, ta biyewa Mk a hanya suka yi ta hirar arziki, suna ta yiwa Haj Saliha addu'ar samun lafiya da nisan kwana mai albarka. Hadi da yiwa iyalanta addu'ar shiriya da tsari daga dukkan abin ki.
Ya ce sai "Ina kuma".
"Sai gidan kawar Anty Sumayya!
Anty Zalihatu Umar,
da k'awata Hauwa'u Umar matar Nasir,
Shinenan".
Ya ce "angama Hajiyata".