← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 113

Sashe 36

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ta kai ga zama ba, ya shigo falon, kai tsaye ya isa kusa da ita yasa hannuwa ya janyo ta zuwa jikinsa sosai, bugun zuciyarsu ya karu, har kowa yana jin yadda zuciyar dan'uwansa ke bugawa.

A hakan ya zauna a kujera, ya zaunar da ita kan cinyoyinsa, ya zame dan'kwalinta yana shinshinar ta tamkar maye, hannuwansa na ta kai komo a jikinta. Jikinta sai tsuma yake tare da wani irin shauki na ban mamaki.

Ya dinga kici-kicin ya zura hannunsa kasan rigarta amma ya kasa kasancewar doguwa ce kuma fitet. Karamin tsaki ya yi, yana rada mata "Ki daina samin doguwar riga irin wannan a yanzu".
Ba ta iya cewa komai ba, sosai yake ya mutsata. Ya yi nisa wurin tsotsar harshenta, ya ji wayarsa da ke aljihunsa tana ta kuwwa, da kyar ya hakura ya raba bakinsu ya fito da da wayar, ganin sunan Mahmoud ya sa shi sakin tsaki a fili sannan ya amsa tare da cewa
"Saboda Allah mene ne hakan?"

Mamaki ya kama Karfi ya ce "Yi ha'kuri leko ina kofar gidan ka karba wa Amarya sako" Daga haka ya katse wayar.

Kan dole ya fita yana bude gate din ya ga Mahmoud a cikin adaidaita sahu, ga kuma kaya ya sauke masa a bakin kofar gidan.

Ganin ya fito yasa Mahmoud ba wa mai adaidaita sahu umarnin ya ja su tafi ba tare da ya yi wa MK magana ba.

Da sauri MK ya bi su yana fadin "Karfi tsaya mana!" Amma fur ya hana direban tsayawa kan dole ya juyo yana mamakin yawan kayan da Mahmoud ya jibge masa.

Akwatina masu kyau guda biyu babba da karami, kwalin indomie guda biyu, kiret din kwai biyu, da leda mai dauke da kayan shayi. Gefe madaidaicin botiki ne dauke da soyayyar miyar kaji da katan din ruwa na SWAN da katan din coke da fanta. Daga jikin akwatin ya hango yar takarda da alamun soke ta aka yi, hannu yasa ya ciro ya fara dubaw *Abawa Amarya, miyar kuma In ji Umma*.

Murmushi ya yi ya san fushi ya yi, a ransa kuma jinjina yawan alherin Karfi yake yi.

Haka ya yi ta kinkima yana shiga da su cikin gidan, sai da ya kammala shigowa da su, sannan ya zauna yana cewa "Duka wannan sakon ki ne in ji Karfi".

Da walwala a fuskarta ta ce "waye hakan?"

"Mahmoud fa."

"Oh shi ne Karfin?"

Kai ya daga mata yana kokarin bude akwatin da ya fi girma, kaya ne tamkar na lefe, sai dai dogayen riguna da English wears sun fi yawa. Dayan akwatin kuma shake yake da kayan kwalliya da na gyaran gashi.

Sosai ta nuna farincikinta kan kayan tare da yi wa Mahmoud fatan alheri.

MK ya yi kasa da muryar sa soasai ya ce, "Mu je daki ki ji wata magana".

Nokewa ta yi tare da fadin, "Fada mini a nan".

"Maganar ba ta nan ba ce Sa'adah na!"
Ya tashi yana jan ta zuwa dakin, ganin da gaske yake yi, ya sa ta cewa "Amma dazun nan ka ce ni bakuwa ce, ba zan yi komai ba sai na zama yar gari?"

"E na fadi hakan, amma kuma ban ce har da wannan al'amarin ba".

Tabe fuska ta yi hadi da tura baki gaba ta ce "Ban warke ba, zafi zan ji."

"I promise you, ba za ki ji ba, I will be soft and gentle".

"Ni dai a'a uncle".

"Bangane a'a ba?"
Ya fada yana mata wani irin kallo. Kan dole ta mi'ka masa kai ya yi yadda ya ke so.
Bata fahimci komai a sai zafi da wata irin takura.

Bai samu kansa ba sai bayan La'asar, don haka a gurguje suka yi wanka, suka yi jam'i.

Kwalliya sosai Sa'adah ta sake yi duk da yadda take jin radadi a kasanta.

Kwanciya ta yi a dakin, tana ayyana gaskiya ba wani dadi a wannan lamarin, sai dai a barka da radadi da ciwon jiki. Romance dai, idan za a yini ana yi ba za ta kosa ba.

A karo na biyu ya sake shigowa dakin.
"Kin san dai barcin bayan La'asar ba kyau ko?"

Idonta a rufe ta ce "Ni ba barci zan yi ba".

"To fito falo, fita zan yi na dora ruwa akan risho idan ya tafasa ki wanke shinkafa ki zuba".

Shiru ta yi tamkar ba ta ji abin da ya ce ba, ya san ba ta gamsu da fitar da zai yi ba ne.

"Kin ji".

"Ni gaskiya ka kashe rishon".

"Ba za ki yi abin da na
saki ba ke nan?"

Cikin tura baki ta ce
"Ni tsoro nake ji kar barci ya dauke ni abincin ya kone".

"Ba fa dadewa zan yi ba, salad zan sayo kawai".

Da sauri ta ce "shike nan adawo lafiya, amma dai kana sayowa ka dawo gida."

"Mai za ki ba ni idan ina gidan?"

Kai tsaye ta ce, "Abin dadi mana."

Murmushi ya yi tare da fadin, "Kamar gaske, a haka kamar jaruma ana taba ki kadan sai raki".

Shiru ta yi tamkar ba ta ji shi ba. Ya juya yana fadin, "Bari ma na zuba shinkafar na san yanzu ruwan ya tafasa".

Biyo shi ta yi tana cewa, "Ka je kawai zan zuba, a dawo lafiya"

Bai wani jima ba ya dawo, da hanzari ta karbi ledar tana masa barka da dawowa, ya amsa cike da jin dadi.

Cikin kankanin lokaci ta yanka salad din ta wanke da gishiri, ta bar shi a kolanda, ta hau yanka cocomber da su tumatur.

Ba ta koma falon ba, sai da ta tace shinkafar, ta yi kasa da rishon ta mayar kan wutar don ta silala a hankali.

Tana shiga daki ta nufa, ganin hakan yasa MK da ke zaune a kujerar kusa da kofar daki ya fizgo ta ta fado masa.
"Kin ce na dawo da wuri na dawo din kuma sai ki shige ki bar ni, ko dai kari kike so?"

Zabura ta yi, ta zame tana cewa "Indai ba so kake ka mayar da ni chopping the rice 🍚 ba, ya kamata ka daina wannan maganar haka nan".

Dariya sosai ta ba shi, ya dinga kyakyatawa, ita kuma ta shige daki tana cewa, "Dole ka yi dariya mana ka same ni kana yin yadda ka ga dama da ni, ba tausayawa".

"Oh haka kika ce? Za ki ga rashin tausayin kuwa".

Yanzu ma shi ya shiryo musu abinci, tana zaune tana kallon karamin tray din da ya zubo salad, mamakin yadda ya zauna ya yi garnishing din salad din da waken gwangwani da su cocomber da tumatur take yi, tamkar a restaurant.

A plate daya ya zuba musu abincin, suna ci suna yaba dadin miyar Umman Mahmoud.

Suna kammalawa Sa'adah ta kwashe kayan ta share gurin. Ya kalle ta ya ce
"Sannu da kokari, amma na ce miki sai kin fita daga bakunci kafin ki fara hidima".

Ta gefe ta kalle shi, ta juyar da idonta gefe sannan ta ce "Ka bar ni kawai na yi ayyukana tunda hidimar ba duka ka dauke mini ba".

Murmushi ya yi tare da cewa "Ashe ban yi gwaninta ba?"

Cikin kunkuni irin na shagwaba ta ce "Ba ka yi ba".

Karar wayarta ya katse damkar da ya yi niyyar kai mata, daki ta shige don a can wayar take. Da sauri ta amsa kiran "Anty Sumayya kin ce fa za ki zo mu yi sallama kafin ki wuce, ga shi har Maghriba ta kawo kai ban ganki ba".

"Kai Iyah! Da gaggawa kike, to muna kofar gidan, zo ki bude mana".

Katse wayar ta yi, ta
isa gaban madubi ta kalli kanta, riga da siket din atamfa ne jikinta, powder da turare ta sake shafawa sannan ta fito.
"Uncle, su Anty Sumayya ne suka zo"

Kafin ya yi wata magana har ta fice da sauri.

Bin ta ya yi da ido, yana jin wani irin abu a zuciyarsa akan me za ta fita a haka?

A hankali ya mike ya fita daga falon ya shige dakinsa da yake tsakar gidan.

Ba su jima da shigowa ba, ya fito, suka gaisa da Anty Sumayya da yaranta, ganin Sa'adah ba ta ba su ruwa ba yasa ya shiga kicin ya shirya ruwa da lemo a tray, da tumblers, ya doro cake din da yasa a fridge, yana jin farincikin ruwa da lemon da Mahmoud ya kawo musu na ratsa shi.

Da kansa ya dauka ya kai musu, Sumayya sai sannu take masa tare da fadin "Ga yara kuma sai ka dauko da kanka, sannu na gode".

Murmushi ya yi tare da cewa, "Ba komai Aunty".

Alwala ya yi, ya fito daga waje ya tsaya ya kira Abba ya danka masa sabbin kudi na dubu biyu,"Ku sayi sweet kai da kannenka".

Fir Abba kin karba ya yi, tare da cewa "An hana mu karbar kudi Uncle"

Dole sai Sa'adah ya kira ya ba ta, ya ce ta ba su. Ta kalle shi bayan Abba ya koma falon ta ce "Fita za ka yi ne?
"Masallaci zan je daga nan kuma zan je gida".

Bata rai ta yi sosai
"Ba dadewa za su yi ba Uncle, so kake na yi ta zama ni kadai? tunda dare ya yi kawai ka bari gobe ka je da wuri".

"To" Kawai ya ce ya daga labulen falo ya ce, "Anty Allah ya mayar da ku lafiya, mun gode sosai."
Ita ma ta amsa cike da mutuntawa.

Daki suka shige, suka bar yaran a falo suna kallo suna fama da cin cake. Jan kunne da nasiha iri-iri Sumayya ta sake yi wa Sa'adah.

Ta dauko wata leda a jakarta mai dauke da tambarin Welcare,ta mi'ka mata ta ce ki adana su sosai, likitan ya ce za ki iya shan wannan ba komai. Ganin da Sumayya ta yi Sa'adah ba ta bude ledar ba yasa ta ce "To ki bude mana na nuna miki yadda za ki sha".
Chapter 36 · 0% Book details