← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 113

Sashe 113

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ta yiwa Innah ganeral sanitation duk kuwa da ta daukar mata Yar aikin da take zuwa ta yi mata shara da wanke wanke.
Amma duk da hakan duk karshen wata sai ta zo ta yi mata gyara na mussaman.

Baffah ya tsura mata ido yana godiya ga Ubangiji, da ya arzuta shi da samun 'Yaya mata, ya tarbiyaantar da su har ya aurar da su, yanzu gashi sun zame masa gata, sun janyo masa mazajensu suna ta hidima da shi, ya yi Imani ko yana da 'yaya maza ba lallai su yi masa abin da Mukhtar d Idris din Sumayya suke yi masa ba.

Gashi kuma ya'yan nasa sun haifa masa 'Ya'ya takwas maza, domin nassin al'kura'ani ya nuna jikanka danka ne.

Madallah da iyayen da basa zaben jinsin da suke son su Haifa, suke godiya ubangiji ta hanyar tarbiyaantar da ya'yansu mata cikin adalci da tausayi.

Sa'a ta koma gidanta, iyayenta suna saka mata albarka da nemawa zuri'arta tsari daga rudin *HALIN YAU*

Mk ya cigaba da kula da iyalinsa cikin adalci da tausayi.

'Ya'yansa biyar Sa'a na da uku
Jawad, Jadid da Junior.

Yayin da Farida take da biyu
Amir da Amira.

Wani week end ya zo Kano, suna zaune a falo ya kalleta ya ce "sai nake tuna shekarun baya da kike ce mini kin yi mafarki, kin zama big Madam, na zama Alaji, na 'kera mana mansion".

Itama ta ce "Na tuna amsar da ka ke bani cewar banga ka 'kara Aure ba?"

Ya fashe da dariya tare da janyota Yana cewa 'dukkan mafarkin ki Allah ya tabbatar miki su, kin zama big Madam, abin alfaharin kowanne miji, tashi muje mu yi nafila mu sake godewa Ubangiji da ya cika mana ni'imominsa.
Wani watan Ina son dukkan ku mini rakiya na gano 'Dan-iyah a Canada har da kannesa zamu tafi".

Ta ce "Jawad bai zama 'dan Malam ba Sai D'an Iyah?"

Da murmushi ya ce "shi ya ce mini sunan da zai sanyawa jirginsa kenan 'Dan-iyah Airlines.
Yana kuma fatan ya samu sarautar 'Dan-iyan Bichi.
Zan fadawa Baban Khairat zamu tafi da ita, ta gano mutumin nata, wata'kila dai zumuncin Jawad da Khairat nan gaba ya bada mamaki".

A zuciyar Sa'a sai fata take Allah ya tabbatar da wannan hadin.

ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH.

*NA GODEWA ALLAH DA YA NUNA MINI WANNAN RANAR TA 27-7. DA NA KAMMALA RUBUTA WANNAN 'DAN LITTAFIN NAWA MAI SUNA A SAMA*.

*INA MIKA GODIYATA GA DUKKAN WANDA YA KARANTA LABARIN*.
*INA SAKE GODEWA MASU KIRANA, DA MASU YIN MAGANA TA WHATSAPP DAN SU YABA MINI, NA GODE MUKU SAOSAI, UBANGIJI YA FINI YABAWA*

*INA ADDU'AR ALLAH YA KAWO MANA ZAMAN LAFIYA A KASARMU TA NIGERIA, YA KUMA BAMU DAMINA MAI ALBARKA*.

*AUNTY RABI SANI GODIYA MAI YAWA, TABBAS KARFAFA GUIWAR DA KIKE YI MINI YA TAKA MUHIMMIYAR RAWA WURIN INGANTUWAR LABARIN NA GODE UBANGIJI YA FINI YABAWA*.

*INA ADDU'AR ALLAH YA JIQAN MAHAIFANA DA DUKKAN WADDA SUKA RIGAYE MU*.

*UBANGIJI YA SAKE HADA MU CIKIN WANI LABARIN, DA NAKE FATAN KU KAR'BE SHI TAMKAR HALIN YAU.*

*INA RO'KONKU KAR A HA'DA MINI DOCUMENT, BANA SO, DAN ALLAH A KIYAYE.*

*ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU*🤝

*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
✍️✍️
Chapter 113 · 0% Book details