← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 113

Sashe 32

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juyo ya zuba mata ido tabbas ta rame, ta birkice amma hakan bai yi tasiri a zuciyarsa ba, musamman da ya tuno kallon rainin da Khalil ya yi masa, ya sake hango yadda ta fito a gaban motarsa, sai kawai ya juya ya ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya ce mata uffan ba.

A kidime ta ru'ko hannun jakarsa murya na rawa ta ce, "Na san na yi ba daidai ba, na ba ka ha'kuri, ka yi hakuri mana!"

Bacin rai sosai a fuskarsa ya dube ta sannan ya ce, "Ke ba na son ballagazanci, a titi za ki ri'ke ni?"

Ba'kin ciki ya kama ta ta fara kukan gaske ta ce, "Ni ka kira da ballagaza?"

Kishi ya rufe mai ido sosai, ba wani ja-in-ja ya ce, "E, idan akwai sunan da ya fi haka muni ma ki hada da ballagazar, don kuwa sunayenki ne, dabi'un da kike yi irin nasu ne. Yanzu kuma kin nuna mini kin saba cu'danya sosai da maza, har kike ganin za ki iya cakuma ta a titi."

Ba'kin ciki ya turnuke ta, ba a taba yi mata tozarci a rayuwarta irin na yau ba, kuka sosai take yi wanda ya matu'kar taba shi, kawai waskewa ya yi. ba tare da ta sake fadin komai ba, ta yi gaba da sauri ba ta ko sanin inda take jefa kafarta saboda tsananin 'bacin rai.

Al'kalamin
*Surayya Dee*
✍🏼✍🏼✍🏼

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

*TALLAH*.

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

47-48

A gigice ya ga ta nufi titi gadan-gadan tamkar zararriya, zuciyarsa ta buga, da azama ya bi ta ganin da gaske tsallakawa za ta yi ba tare da ta duba ba. A ki'dime ya fuzgo ta, ganin mota na shirin yin wasan-kura da ita, amsa-kuwwar motoci sun cika gun, har sai da mai motar ya tsaya ya fito ya dinga zazzaga mata sababi, yayin da ita ko kallo bai ishe ta ba illa fizgewa da ta yi daga ri'kon da MK ya yi mata, ta koma gefe tana hawayen ba'kin cikin maganganun da ya gasa mata.

Sai da ya ba wa mai motar hakuri ya tafi sannan ya tsayar mata da Adaidaita Sahu, juyin duniya ta ki hawa, har mai Adaidaitan ya ji haushi ya yi tafiyar sa.

Ya kalle ta ya ce, "Watau da ma zuwa kika yi ki sake tayar mini da hankali ko?"

Yana rufe baki ta ce "Kadai so hankalin naka ya tashi ne, ha'kuri na zo ba ka, ka ki ha'kura. Ka bi ni da kalaman muzanci, to ai sai ka yi tafiyarka tunda da ma ba kai ka kawo ni ba balle ka ce sai kasa na koma dole."

Ya kalle ta ya ga tana cikin fishi irin wanda bai taba ganin ta yi irinsa ba, sai ya sassauta ya ce,
"Na ji ba ni na kawo ki ba, amma kin ce gurina kika zo, idan kuwa haka ne to ba na son zuwan. Ki koma gida ni zan zo."

Kamar ta ce "Ba na son zuwan naka ni ma!" Sai ta daure ta kalle shi ta ce, "Nasan ba da gaske ka ke ba."

"Zan zo mana da gaske nake."

Ta yi shiru tana rantsuwa a ranta ba za ta yarda da maganganun da ya yi mata ba. Dolensa sai ya janye ko ya ga tashin hankalin da ya ke kirari.

Ya kalle ta ya ga ta turo bakin nan gaba, mamakin yadda ta ke son mayar da laifin da ta masa ya koma kansa ya ke yi.

"Kin yarda na tsayar miki da abin hawa?"

Shiru ta yi masa alamun ba ta yarda ba. Ya kalle ta ya ce, "Magana nake miki."

A gajarce ta ce "Ban yarda ba!Yawon ballagazan ci zan wuce."

Ji ya yi kamar ta wasta masa ruwan dalma a zuciyarsa, ya hassalo sosai ya nuna ta da yatsa ya ce, "Ni kike yi wa magana kamar kina yi da sa'anki? Saboda ba kya ganin girma da mutuncina?"

Ta yi mai shiru ta kasa cewa komai. Ya sake cewa "Ki dinga sanin abin da za ki na fada mini ba na son kau'din baki."

Duk yadda ya so ya tafi ya bar ta a gurin kasawa ya yi, ita kuma ta kafe akan ba za ta tafi ba, shi ya yi tafiyarsa ya 'kyale ta.

Da kyar da jubin goshi ta yarda ya tarar mata Adaidaita, bayan ya rantse zai zo gida ya same ta, sannan zai 'dauki kiran ta.

Yana tsaye yana kallon su har suka bar wajen. Wata ajiyar zuciya da bai san yana ri'ke da ita ba ta kwace, a fili ya ce "Wacce irin yar daru na kwaso wa kaina ne? Da motar nan ta taka ta, ina take son na sa raina? Me zan ce da iyayenmu idan aka gane muna tare ta sami wannan hadari?

Ya dade a tsaye yana mamakin irin son da yake wa Sa'adah. Ya dauka idan ya gan ta ba zai ji komai ba, ya dauka kaifin son ta ya dakushe, ashe ya nan daram. Musamman da ya ga mota na shirin take ta sai ya ji zai iya rasa ransa don ya tserar da ita, ko muzuran da ya mata na karfin hali ne kawai da son kwatar kansa a idonta.

Tana isa gida ana sallar La'asar, sai da suka yi sallah sannan ta ba wa Inna sakon da ta karbo, ta koma daki ta hau kiran MK.

Sai da ta kira har sau uku bai 'daga ba, shi kuma ya fito a Masallaci ke nan kiran ya shigo, bai daga ba sai da ya koma dakinsa ya kwanta sannan ya 'kira ta.

Har ta fara hasashen da ma zai iya rantsuwa akan 'karya? Sai kuma ta ga kiran sa ya shigo, da sauri ta dauka sai kuma ta yi shiru ta tura baki gaba tamkar yana ganin ta.

Shiru ya biyo baya tamkar ba kudi ke bin iska ba.

A shagwabe ta ce, "Na gode!"

Ya ce, "Godiyar me kike yi?"

"Ka cika al'kawari, don Allah ka yi ha'kuri wallahi na horu ba zan sake yi maka laifi ba."

Ta fa'da da rauni a muryarta.

Jikinsa ya mutu, wata irin kasala da ba ta da nasaba da gajiya ko barci ta lullube shi, murya a dakushe ya ce, "Kin bata mini rai, kin tayar mini da hankali, kin jefa ni cikin wasi-wasi mai yawa, kin janyo mini raini."

"Ka yi ha'kuri!" Ta fada da sauri.

Shiru ya yi ba tare da ya yi magana ba, saboda yadda ya ke fama da kansa, ji yake ina ma ya jita a jikinsa.

Murya ba amo sosai ya ce, "zan fada miki, ba na son yaron nan. Ina bakin cikin tarayyarki da shi, wannan ne karon karshe da zan miki afuwa a kansa, ba don girman son da nake miki da kunyar Baffa ba da na ha'kura da ke Sa'adatu. Saboda kina cutar da ni, da ni kika gani da Farida da ban san kalar tashin hankalin da za ki mini ba. Amma saboda yadda nake son ki, na ke gudun bacin ranki haka na rufe ido na rabu da ita da dukkan lamarinta. Ni kuma kin kasa tsayawa gare ni ni ka'dai."

Yanayin muryarsa da yadda ya ke maganar cike da rauni sai ita ma ya jefa ta cikin wani irin yanayin da duk mai lafiya ba zai iya kauce masa ba, tsikar jikinta har tashi take yi.

"Am sorry!" Ta fada a gajarce tana jin ina ma inama...

"Shike nan ya wuce amma kisa a ranki cewar yaune karon karshe da zan saurare ki na miki afuwa akan Khalil".

"Na gode my love!"

Mamaki ya kama shi, karon farko da ta kira shi da wani suna bayan Uncle.
Ya ce, "maimata abin da kika ce?"

Dariya ta yi "Thank you na ce!" Sai ya saki maganar ya ce, "Ba ni labari."

Haka suka sha hirarsu cike da Begen juna, dukkansu sun tabbatar sun yi missing din juna, sun kuma yarda farincikinsu na hannun junansu.

Washagari da yamma ya zo, ba Sa'adah kawai ba, hatta Inna sai da ta yi murnar zuwansa, hira suka yi cikin tattalin juna, har ya ba ta labarin irin gyaran da yake mata a gidan da za su zauna.

Tun daga wannan lokacin Sa'adah ta yanke hul'da da Khalil saboda ba karamin tashin hankali ya janyo mata ba.

Hankali ya kwanta sun shirya da MK amma ta 'kullaci kalmar ballagazancin da ya jefe ta da ita ba ka'dan ba, ta kuma ci alwashin maganar ba za ta bi iska ba, lokaci ta ke jira.

Haka kwanaki suka yi ta zuwa suna wucewa, har watan azumi ya kama al'ummar Musulmai kowa ya koma ga Allah ana fatan dacewa da Rahamar Ubangiji.

Zuwa wannan lokacin shirye-shirye ya yi nisa a bangaren MK, an kammala gyaran gida, gyaran da ya dawo da gidan tamkar sabo.
Chapter 32 · 0% Book details