← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 113

Sashe 79

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk kokarin Mk ya samu Sa'a a waya ya ci tura.
Tunda ko Baffah da ya mata maganar Jawad na ta cikiyarta ta daure ta kira shi su gaisa.

Kai tsaye ta ce "idan da rabon zamu gana zai dawo ya tarar da ni, Ni bazan kira shi ba, tunda ba shi da wayar kansa".

Daga Baffa har Inna ba wadda ya tilastata.

Mk da ya gaji da kiran lambar Baffah yana cewa tana Makaranta ko shi baya gida, sai ya kira layin Sumayya ya bawa Jawad suka yi magana yana ta mata kukan yana expecting Mami has gone.

Tausayinsa ya cika zuciyar Sumayya, ta dinga lallashinsa tare da al'kawarin daga yanzu zuwa kowanne lokaci zai ji muryar ta, tana nan cikin koshin lafiya.

Suna gama waya kuwa ta tura musu sabuwar lambar Sa'a.

Jikin Mk har bari yake wurin kiranta, amma sama da sau goma ta ki picking.

Tana kwance a dakinta tana kallon
Yadda Kiran ke ta shigowa.
A ranta tana fa'din har abada ban son jin ka, Jawad din ma na yafe maka shi".

Mintina goma sai ga kiran Sumaayya a layin Inna, ta dinga yi mata fa'da tamkar ta shigo ta wayar ta daketa, saboda itama ta kira layin nata bata dauka ba a tunaninta Mk ne.

"Iyah kalaman Jawad sun tayar mini da hankali tunaninsa mutuwa kika yi ake boye masa, idan kina haka har yanzu akwai kullin Mukhtar a ranki. Ki amsa masa waya Jawad ne zai yi magana da ke yafi sati yana cikin damuwar rashin ji daga gareki".

"Ni wlh Anty har Jawad din ma bana bu'katar jinsa ina masa addu'a, ina fatan ta zame masa garkuwa a ko ina yake".

Sumayya ta ce " To shi laifin me ya miki haba Iyah! Ki ji tausayi mana".

Da kyar ta shawo kanta ta yarda zata 'daga wayar.

Ba a jima sosai ba kuwa, 'Kiran ya sake fa'dowa wayarta.

Ta dauka ta yi shiru, sanin da Mk ya yi dabiarta ce ba zata fara yin magana idan ya 'kira a waya tun fil'azal sai bai wani damu ba, ya dinga yin sallamah, ya koma cewa hello nan ma shiru, ya mayar da wayar hand free, a tunaninsa jiyota ne ba ya yi. Yaayin da Sa'adah tsananin bacin rai ne ya kamata akan me zai mata magana, ya bawa Jawad din wayar mana.

Murya a sha'ke ta ce "Jawad!"

Ran Mk ya baci wato tana jinsa amsawa ne ba zata yi ba.

Amma a zuciyarsa ya samu nutsuwa kwarai da gaske da ya gane tana nan cikin koshin lafiya har ma tana da kwarin guiwar yin wulakanci, dan haka sai ya mi'kawa Jawad wayar a fusace.

Ya tsurawa Jawad ido yadda ya ke magana yana wani irin murmushi, ya sake kallonsa sosai yana ganin ba kammanin Sa'a tare da yaron illah wushirya da farcen hannayensa, inka dauke Wannan tamkar Mk aka raba biyu aka yi shi dan tsananin Kamar da suke yi.

Ya nisa ya tuno yadda Sa'adah ta tsaya a gabansa tana sheganta masa yaro, banda dai so baya shawara ai da bai kamata ya cigaba da son Sa'adah ba.

Ya muskuta yana kasa kunne yana sauraron hirar su inda ya ji Jawad na maganar da ta ja hankalinsa.

"Mami na tara ku'din da zai ishe ki zuwa, zan fa'dawa Malam zan zo na taho da ke".

Ya juyo murmushin Sa'a da yake kashe masa zuciya ta na cewa " A ina ka samu kudi?"

"Idan Malam ya bani bana kashewa, sannan munje gidan freinds dinsa na samo ku'di da yawa, kuma Anty ta je da ni gidan sister dinta nan ma anbani kudi duk na boye miki su".

Dariya ta kwacewa Sa'adah ta ce "Ka siyi abin da kake so ka ji Jawad! Kudin ba zai isa na zo ba".

Ya fara mata kuka yana cewa
"kudin fa da yawa Mami! a school ma da muka yi tseren gudu da quiz na zo na daya an bani kudi da yawa har da chain din gold, na boye miki shima".

Kukansa ya ta'ba ta sosai dan haka sai ta ce "To ka ai baka da kudin zuwa da na komawa, iya nawa ka tara ka bari sai ka sake tarawa sai ka zo ka dauke ni".

Cikin kuka ya ce "Zan fadawa Malam ya biya mini".

"To ka daina kuka, idan kana kuka, bazan yarda na zo ba, sannan ka bari sai anyi hutun school, dan kar a wuceka a karatu, kuma ko ba ka ji ni a waya ba, ka daina damuwa kasan Ni ma ina zuwa school, karatu ne yake boye ni, amma kullum ina yi maka addu'a".

Ya goge hawayen ya ce " Na daina kukan, idan zaki mini addu'ar, ki dinga addu'ar kudin nawa ya isa na siyi jirgin kawai. Kinga sai na yi ta yawo da ke har da su Inna da Hajiyar Bichi."

Suka dinga hira sosai, suna Shirin yin sallama ya ce na bawa Malam ku yi magana? shima ya damu da ba bamu same ki a waya ba".

Mk ya sake kasa kunne dan ya jiyo amsar da zata bayar.

"Ai mun gaisa kafin ya baka wayar, stay blessed my Boy".

Daga haka ta katse wayar.

Da wani irin kuzari Jawad ya mikawa Mk wayar yana fadin "thank you very much Malam".

Da zai karbi wayar sai ya hada da hannunsa ya janyo shi ya dora shi akan cinyoyinsa.

"Da sakakkiyar fuska ya ce " Me yasa ka damu sai Mami ta zo nan alhalin kasan bata son zuwan?"

Da sauri ya ce "Lah tana son zuwa fa, tana son ka mayar da mu gidanmu mu dinga kwana tare, da zamu taho na roketa ta biyo mu na san ba zaka yi fa'dan mai yasa ta zo ba".

Mk ya dinga jin wani iri, a karancin shekarun Jawad ya shaide shi ba zai wulakanta uwarsa ba, anya bai kamata ya sasanta da Sa'adah haka nan ba? Tunda ya lura a fili Jawad yafi son uwarsa akan komai.

A hankali Mk ya ce "To ya baku taho taren ba?"

Ta ce mini "Ba ita ka ce ta zo ba, Anty amarya ka ce ta zo, sannan bata da ku'din zuwa, na ce mata ai Baban Anti ne ya biya mana, shine ta ce ita Baffanta ba shi da kudin da zai biya mata!
Sai na ce to ni zan tara kudi na biya mata itama".

Jikin ya Mk ya yi wani irin sanyi, ya dinga jin kalaman yaron har cikin zuciyarsa.

A shekarunsa na goma sha'daya har yasan kishin uwarsa? ya tuna duk sadda ya samu kudi yake nacin shi zai ajiye abinsa ashe uwarsa yake yiwa tanadi? Ya nisa ya sake tuno lokacin da makarantarsu ta karrama shi da bashi chain din gold, da suka dawo gida ya shige dakinsa ya masa boyo na mussaman duk rarrashin da Mk ya yi masa akan ya kawo a ajiye masa, ya ce shi ya boye da kansa, ashe duk uwarsa yake yiwa? ba abin da ya tsayawa Mk a zuciya irin da Saadah ta ce wai ita Baffanta ba mai kudi bane.
Shiyasa 'danta ya kudiri aniyar ya tara mata kudi, dan ya huce mata takaici.

A ranar Mk ya ji ya yafe mata kaso sittin cikin kullacin da ya mata, ya samu saukin da zuciyarsa ta yi akan lamarinta, sai dai wannan tsoron nata da ya shige shi, bai ragu ba.
Ya lura idan bai bi a hankali ba, nan gaba ba karamin matsala Jawad zai bashi ba, mussaman da yana sane uwarsa tana son ya mayar da su gidansu, amma bai yi hakan ba.

***

Tunda suka yi shekara da aure ba labarin samun karuwa!

Farida ta fara jelen ganin gynecologist, duk wani gwaje gwaje anyi mata an tabbatar komanta lafiya kawai lokaci ne bai yi ba.

Zuwa wannan lokacin Mk ya samu budi sosai adalilin tallafin da gwamnatin tarayyar Nigeria take bashi, ga albashinsa, ga kuma wadda yake karba na gwamnatin kasar ingila. Bugu da kari ya na kasuwanci sosai, ya sake fadada shagunan askinsa, ya bude na shagon saida kayan maza masu daraja da kyau.

Dan haka ya kammala katafaren gidansa da yake ginawa akan hanyar zuwa sabuwar Jami'ar Bayero, fenti kawai ya rage da Yan kananun abubuwa da sai a shiga gidan za'a fi bu'katar su.

Gida ya yi kyau sosai, ya tuna Sa'a ce ta tsara yadda gidan zai kasance, a ransa ya gamsu Sa'adah tana da baiwar fashion and design hadi da creative.

Cikin abubuwan da Mk yake yawan tunawa ya Sha mamaki akan lamarin Jawad shine wani lokaci da yake daf da barin kasar ingila, ya fita da su shopping, shagon kayayyakin Mata da kananun Yara na alfarma suka je, Farida ta zabi dogayen riguna na alfarma da suka amsa sunansu, guda biyar ga turarenta designer na Amour amour, ta hada da wani dan kunne mai kawanya da alamunsa daham ne.

Kasancewarta bata amfani da kowanne irin mai sai veseline ta cakude shi da gilasirin, tafi bada karfi a shower gel.

Jawad na tsaye yana kallonsu. Mk ya juyo ya ganshi a tsaye bai dauki komai ba, ya kalleshi ya ganshi tsaye ya rungume hannunsa a kirjinsa.

"Jawad baka dauki komai ba".
Ko sai mun je wani mall din?"

Ya girgiza kai ya ce "I thought Anty ce kawai zata yi shopping yau".

"Kaima ka duba duk abin da kake so ka dauko"

Suna tsaye suka hango shi rungume da dogayen riguna irin na Farida sai banbancin kaloli guda hudu, sai takalma na mata masu tsananin tsada kafa biyu, dukkansu kirar kasar itali, ya ajiye gurin buga kudi, ya wuce ya dauko zobe guda daya da ya kusan ninka Dan kunnen Farida.

Mk ya kalle shi ya ce "Me zaka yi da wannan kayan? "

Ya shagwabe fuska ya ce "Malam so nake yi ba kai ka ce na dauko komai nake so ba?"

"Na fa'da amma ai naka na ce ko?"

"Malam ni wannan nake so a maimakon nawa, kaga rigunan Nan tsaraba zan yi da su, daya Antyn Lagos, daya Maman Gombe, daya kuma Anty Samira".

Mk da Farida suka zuba masa ido domin kuwa wadda duk ya ambato zai bawa Mk bai isa ya ce komai akan su ba.
Chapter 79 · 0% Book details