Sashe 71
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya nisa yana jin wani irin abu ya shake shi, ya ce "Sa'adatu ki barwa Allah ya mana zabi kin ji, ina son ki har yau, idan 'kaddarar zaman bata 'kare ba ubangiji zai sake hada mu, amma ni yanzu fatana ki cire damuwa a ranki, ki fuskanci karatun ki, shi zai taimake ki a ko ina zaki samu kanki, duk abin da ya taso miki ki fada mini kai tsaye ki ji tamkar Nima Sumayya ne a gurin ki".
Ta kasa yin magana sai goge fuskar ta take duk ta bata Hijabin nata, haka ya shiga mota suka tafi Jawad ya yi lakwas, ya zama marar kuzari adalilin Halin da ya ga uwarsa a ciki.
A hanya ya dinga fa'din"Malam sai yaushe Mami zata zo ta dauke ni, mu koma gidan mu, me yasa kullum sai ta yi kuka? ko abinci bata ci sai Inna ta zauna kusa da ita, me take yi anan din?"
Ya 'kasa bude Baki ya amsa masa, ganin da Jawad ya yi bai kula shi, yasa shima ya yi shiru dan yasan idan ya dame shi zai mammake shi ne.
A kofar gidan Hajiya ya ajiye shi, ya juya karban wani sakon, sukuku Hajiya ta ga Jawad ya shigo Mata, ta dinga tambayar me ya same shi a Ina kuma ya Da'de ?.
Ai kuwa ya marairaice ya ce "Mami ce take ta kuka".
"A ina ka ga Mamin?"
"Malam ne ya kai mu, tana wani waje babba har da masallaci, tana ta kuka, tana ce masa ya mayar da mu gidan mu".
Jikin Hajiya ya mutu ta ayyana idan Mukhtar bai yi taka tsan tsan ba zai jefa 'kinsa a zuciyar 'dansa.
Wacce irin zuciya ne da shi haka mai tauri bata sani ba, kana son mace kana bibiyar ta amma ka kasa yafe mata ko dan kaima hankalin ka ya kwanta?.
Haka da ya zo ta dinga masa fa'da akan lalle ya mayar da Sa'a, amma ya kafe akan ta cigaba da addu'a abarwa Allah, ta yi shiru ta fara wasiwasi ko jifansu aka yi, ko aljana ce ta shige shi, tunda matsalar kin auren a gunsa take.
Haka ya tafi kasar ingila ya bar Jawad a hannun Hajiya.
Kuka ba irin wadda Sa'a bata yi ba dan kuwa tafiyar sai ta sake dagula mata lissafi, sati guda bata zuwa ko makaranta, har ta kai tausayinta sosai Inna ke yi, saboda ta gane sosai Iyah ta yi nadama, amma Mukhtar ya rufe 'kofar sulhu, duk da har a lokacin bata kullace shi ba.
Zainab Ma'aji da ta kammala karatunta tana bautar 'kasa ita take ta jelan zuwa tana jinya ha'di da ban baki har ta fara samun sukin jiki da na zuciya.
A wannan lokacin Sa'adah ta gane Bata da 'kawa ta amana irin Zainab domin ta nuna mata kauna ta gaskiya, ta tsaya mata a sadda ta shiga taskun rayuwa, yayin da su Halima da Safina har yanzu da ta shafe watanni masu yawa a gida basu waiwaye ta ba.
Haka nan ko a group din su na old girls basu ta'ba jajenta ba, dan tana yawan tambayar Zainab ko ta ga sun neme ta, amsar dai itace basu yi ba.
Ganin Mk ya bar kasa yasa Baffa amincewa da shawarar Sumayya da ta bayar na asiyar da kayan furniture's din Sa'a, a waccan lokacin kin amincewa ya yi, yana tunanin ko Allah zaisa su daidaita kansu, sannan kuma ai ba su suka yi kayan ba.
Tv da freezer kawai suka bari sai set din gado daya da katifarsa, aka hada kan kudi akaje can kauyen Alu gaban unguuwa uku aka sai filaye a jere guda biyu, bayan ta siyar ta zobenta daya aka cika kudin, tunda ba kamar yanzu bane da komai ya yi tsada.
*Shekaru uku a gaba*
Zuwa wannan lokacin kome ya lafawa Sa'a, sai dai damuwar zuci wadda karfin imani ke sawa ayi harka sosai har aga kamar mutum ba shi da damuwa
Sau daya Mk ya zo yayi sati uku ya koma
Ta kammala karatunta na diploma, ta yi jarrabawar D.E. don 'dorawa da karatun digiri a Jami'ar Bayero, duk da Baffah bai sani ba jira suke a samu admission din sai asan yadda za'a bullo masa, har yanzu kuma Mk ke dawainiya da ita duk da ba kasafai ma suke waya ba, Dan har yanzu ta'ki rike waya sam, amma duk karshen wata zata ji alart na kudi a wayar Inna tunda da layin ta bude ko mantawa ba ya yi, hakanan duk karshen wata Hajiya ke kawo mata Jawad da kanta yayi kwana biyu, idan kuwa aka yi hutu gaba'daya a gun uwarsa yake yinsa.
Ba wata wahala ta sami admission a B u.k kasancewar ta dage ta fito da sakamako me kyau a diplomarta hakanan jamb dinta ta yi kyau.
Wannan karon Sam Baffa Bai tirje ba saboda ya yadda iya a nutse take, sannan idan ba makaranta ba ko kofar gida bata fita, haka nan idan antashi bata tsaya ko Ina gida take Yi, hanyar ta daya tamkar tururuwa.
Sai dai a ranar da zata fara zuwa Jami'ar Bayero, a tsakar gida a gaban Innah Baffah ya ce "Iyah kina karatun nan ba dan ina so ba, na so ace daga gidan mijin ki, kike wannan karatun amma na yarda ki yi, domin na gamsu alfaninisa yawa ne a rayuwar ki da dukkan wanda ya shafe ki, ina fatan yaddda na barki kike karatun ki ba dan ina so ba, sai dan rayuwar ki ta inganta, Nima wataran zaki mini abin da nake so ko da bakya so, sai dan kin san ba zan miki sanadin shiga wahalar rayuwa ba".
Kai tsaye ta ce "In Sha Allah Baffah, bana fatan na fifita son raina akan na ka, bana fatan ranar da zaka ce na yi wani abu na bijire maka".
Ya dinga mata addu'ar samun Nasara a dukkan al'amarin ta.
Ba abin da ke gabanta sai karatunta, bata saurarar kowa, haka nan bata da kawa saboda ta ga illar kawance, tsakanin ta da abokan karatunta, gaisuwa da tattauna inda ba'a fahimta ba, amma ba kawance ba, ta riga ta fita harkar 'kawance duk da dai tana da kawar arzikin wato Zainab, sai dai bata san wacece zata sake zame mata kamar Zainab din ba,wadda a da raina Zainab din take yi, tana mata kallon bagidajiya, ashe itace Bagidajiyar bata fahimta ba sai da komai ya kubuce mata.
Ta fara karatunta daga aji biyu a Jami'ar Bayero duk dai a fannin Sharia, dan haka a old side take lectures din ta.
Second semester a year three dinta Mk ya kammala karatunsa, sai dai Jami'ar Bhirmingham din ta ri'ke shi tsawon shekaru biyu inda zai koyarwa masu degree na farko.
Ya dawo gida, ya yi hutun wata guda tunda sau 'daya ya zo Nigeria. Zuwa wannan lokacin Mk ya murje, ya goge fatarsa ta goge farinsa ya sake fitowa, gaba'daya ya canja, ilimi da gayu sun sake kama shi, Yan mata sai kai masa caffa suke, tunda ga dalibai har abokan karatunsa, bakake da fararen ingila.
Haka anan gida Nigeria ma bai huta da Yan mata masu ui masa kutse cikin shafukan sa na yanar gizo ba.
Al'amarin mata ya tsorata shi, wadda ya so, son da baisan iyacinsa ba tasa tsoron mata yake yi, gaba'daya, wahalar da ya sha a soyayya tafi da'din ta yawa shiyasa ya juyawa soyayyar baya, tsawon shekaru hudu haka yake gudanar da rayuwar sa, sai soyayyar Sa'adah da ke makale a kasan ransa.
Da Farida kawai yake dan gaisawa sama sama saboda nauyinta da yake yi, wadda yanzu ta kammala karatunta tana aiki da asibitin Nasarawa.
Har gida ya zo ya gaida Baffa tare da tsarabar yadi da turare da liptons masu yawa na Ahamad tea.
Sosai suka yi hira, haka nan ya shiga ya gaida Inna itama da tata tsarabar.
Ta dawo makaranta sanye cikin Hijabinta kamar kullum, suka yi kicibus da shi ya fito a gidansu, Jawad ya kawo, tunda ya zo basu hadu ba adalilin kullum tana makaranta, yana son ganin ta amma ya rasa yadda zai yi tunda har ya zuwa wannan lokacin ta ki ri'ke waya.
A zaure suka gaisa ya lura da yadda ta samu cigaba a nutsuwar ta, haka nan da alamun ilimi ya fara bin komai nata, kawai yadda ta kankace ta sake zama Yar karama ne ya bashi mamaki, ba alamun kwalliya a tare da ita amma fes take ba ta da makusa.
Ta kalle shi ta ce "Malam ka canja, ka sake girma, idan ka shiga cikin turawan sajewa kuke yi da su ko?"
Ya yi dariya baice komai ba, ya sake kallon ta ya ce "ke kuma kin zama Yar karama tamkar ba ke ce uwar Jawad ba".
Ta yi kasa da kanta bata ce komai ba, amma a ranta tasan rashin sa shine dalilin tunda kullum zuciyar ta ba Da'di
**
"Ba fa za ka koma wannan kasar da sunan aiki ba, ka yi ta zama ba aure kenan, muma nan kasar ai ana bu'katar irin ku"
Hajiya keta wannan fa'dan yayin da Mk ya yi shiru, ita kuma so take ya mayar da matarsa ko sati guda suyi tare sai ya yi tafiyar sa tunda ba zai yiwu ta bar karatunta ba.
Amma tana fara maganar ya hade fuska iya fuska, jikinta yayi sanyi, daga karshe ma sai ga Alh Isa ya zo mata da maganar ai ya samu yarinyar da zai aura, za'a daura auren kafin ya tafi, daga baya zata bishi idan Jawad ya samu visa.
Girman Alh Isa ya hana Hajiya cewa komai saboda kawaicin kar ta nuna masa iyaka akan Dan amininsa, wadda tunda maigidan nasu ya kwanta dama , Alh Isa Bai taba juya musu baya ba, yana tsaye akan almarinsu dana 'yayansu.
Ba'kin ciki a zuciyar Hajiya tamkar ta fashe kan dole Alh Isa ya hakurkurtar da ita tare da nuna mata aure kaddara da rabo ne, shi kansa Mukhtar din har ya dira a kasar bai san zai yi aure ba.
Al'amarin ya faru ne, da ya samu labarin rashin lafiyar Farida a bakin aminyar ta Rukayya Mustapha.