← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 113

Sashe 54

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na gama miki komai illah wurin da yake bu'katar signed dinki!amma a yanzu na fasa, matu'kar da aurena akan ki! wallahi ba za kije makarantar nan ba".

Cikin rudu tace "Ban gane ba fa?"
Ya tashi ya kunna fitila, sannan ya zauna! ya zuba mata ido yace
"Ina nufin idan har sai da yardata zaki yi karatu, to baza kiyi ba, idan kuma ya zama dole sai kin yi, sai dai kije a matsayin single amma ba matata ba".

Hawaye ya balle mata, ta ru'ko hannuwansa cikin rawar murya tace
"Na roke ka kar min haka! dan Allah kar bari na gasgata masu fadin ba zaka taba barina na yi ilimi ba".

Ido cikin ido yace "gara ki gasgata su Sa'adatu, ada kam na kudiri aniyar ilimi sai kince ya isheki! amma Billahillazi yanzu na fasa, ba ki fara karatun ba, kina iya zagina, bare kuma na baki damar da kullum sai kin fita, kin yi cudanya da mutane daban daban, tunda na gane kawaye zasu iya rinjayar ki, zasu iya canja miki dabi'a, zasu iya ruguza mana kyakkawan zaman mu, daga lokacin na gane barinki karatu mai zurfi ha'dari ne, ilimin sakandiren da kika samu, yasa kina jin kina da yanci, Ina kuma ga kin shiga babbar makaranta, ki zauna ki yi rainon Jawad kawai, tunda nace ki cire loop din nan, amma sun zuga ki, kar ki bari ki tara yara mu tsufar da ke, to ki zauna ki tabbata da kuruciya".

Kuka take yi, tana bashi ha'kuri, yace "na gama maganata, zabi na gareki, dan kuwa wallahi ba za kije ki koyo mini karatun raini da rashin da'a ba, a haka kina iya zagina,nan gaba kuma sai dai na ji mari."

Kuka take yi tun daga kasan zuciyar ta, a duk tsayin rayuwarta a duniya a ranar ta fara sanin Ashe kuka ma kala kala ne, duk wadda tayi a baya na nisha'di da shagwaba ne, na yau ne take yin na zunzuruntun bacin rai.

Ya kalleta yace "Ba abin damuwa bane Wannan fa, domin na riga da na baki damar ki, dan hakama nake ta dan jah baya, dan mu dan saba da rashin tarayyarmu, Ina tabbatar miki idan kin zabi makaranta akan aure! Wallahi zan dauki nauyin karatunki, kuma zan wanke ki a gun su Baffa, zan dauki laifin rabuwarmu Ni ka'dai."

Murya na rawa tsabar kuka tace, "Dan girman Allah yaushe na zage ka?"

"Kina nufin na miki sharri ba ki zage ni ba?"

Ta sake ru'ko hannuwansa da kyau tana harhado kalmomi tace " Ni bance haka ba Malam! amma dan Allah ka yi hakuri, na canja Wallahi, ba zan sake ba"

"A ranar da kika zage ni dama na tabbatar miki u will pay for it! zaki yi karatu da yardata ka'dai, idan na gamsu kin canja din da gaske, idan na tabbatar ba mahalukin da zai canja ni a zuciyar ki".

Ya zare hannuwansa daga nata ya mike, itama ta mike ta tsugunna ta ru'ko kafafuwansa, tana fadin "Malam bazan iya barinka ba, dan Allah, ba dan halina ba, ka janye wannan kudirin ina son karatun amma da yardar ka nake so".

Yace "idan kuwa kina son karatu da izinina, wallahi ba bana ba, to be frank Sa'adatu! ban san time din ba, har sai na gamsu ba third party a tsakanin mu, sai na gamsu na wuce zagi da diban albarka ta kowacce fuska daga gareki".

Ta sake shi! sanin halinsa idan ya rantse shikenan ya gama magana, ta ha'kura tana jin bakin ciki tamkar ta mutu! ta huta. Kuka ba irin wadda ba tayi ba, Mk da kansa mamakin kansa ya ringa ji, bai taba zaton zai iya mata haka ba, sai dai wata'kila yadda take gasa masa duk maganar da ta zo bakinta yasa ya iya jarumta haka.

Sa'adah tana ji, tana gani, ya hanata makaranta, duk ta zama wani iri, zaman nasu dai gashi nan, ta koma shiru, ba walwala sosai, kullum cikin kunci take amma bakinta dif, sai kuma yanayin data koma ya dame shi, fata yake su koma kamar da, rayuwar farin ciki, amma abin na neman cin tura, a zahiri dai suna zaune lafiya amma kuma babu nisha'di a cikin zaman.

Saboda su Halima da suke fadin "dama ai sun san pooling dinta yake yi, ba wata makarantar da zai barta, duk dan'iskan namiji zai yi iya yinsa ya kulle matarsa a gida saboda sun San Annabi baya tuntuben harshe, duk abin da ka yi da matar wani, sai anyi da taka.

Wattanni kusan biyu zamansu ba armashi, bata masa komai na laifi, amma kuma ta dadare ranta, suna cikin haka, aka fara babban zabe na kasa, kowa yasan Malaman jami'oi ne baturen zabe, Dan haka wata guda aka dauka ana yiwa su Mk horo na mussaman kan yadda zasu kare muradan yan kasa, kar su yarda ayi amfani da su, ayi wa dimokaradiya kafar ungulu, Malaman addini suka dinga musu wa'azi na suji tsoron Allah su yi gaskiya a cikin aikin da za su yi, karshe suka rufe bayanin da cewa duk wadda aka bashi kudi dan ya yi magudi, to ya karbe kudin ya adana, sannan ya yi adalci, ma'ana ya fadi sakamako na gaskiya.

A yanzu da suke shiga shekaru biyar da aure shi da kansa ya tabbatar tsoron ta yake yi, idan akwai abin da ya tsana to ta share shi, ko ta tsiri fushi, ko ya fita sai ya dawo, yasan yadda ya yi ya shawo kanta, yayin da ita kuma take jin kanta a sama komai take so sai ta same shi, SUMAYYA kanta mamakin yadda Sa'adah ta dawo take yi, kullum cikin tsadaddun sutura take , hatta salooon din da Sa'adah take zuwa one in town ne, kullum suka yi waya sai ta mata nasiha ta saukaka buri, ta rage dorawa mijinta hidimar da bai kai ya yi ba.
Itakuwa sai tace da ba zai iya ba, ai da bai yi ba, ya hanani karatu ai kuwa dole yamin yadda nake so, tunda idan ban ci ba ma, na waje ne zasu ci, har Sumayya ta gaji ta zuba mata ido tana mata addu'a.

Rannan da yamma Zainab Ma'aji ta ziyarce ta, kasancewar ana daukan lokaci kafin su hadu a dalilin Zainab din tana karatu ne a Jami'ar jahar kaduna(K.a s.u). ba kowanne hutun ma take zuwa Kano ba, sai take barin hoste ta tafi gidan kanwar mahaifiyarta ta yi hutunta indai ba mai tsayi bane.

Mamamki ta tsaya yi ganin yadda Sa'adah ta koma, ta goge sosai, fatarta ta yi fresh tabbacin tana samun tsadadden mai, tasan Sa'adah Yar gaye ce, amma ko kusa ba kamar yanzu ba, da ta ke samun dukkan wants dinta.

Sauyi sosai ta gani tunda ga jikinta, da abubawan more rayuwa na gidan, da cima ta mussaman, ga wata irin ginshira da ta gani a tare da ita.

A sanyaye Zainab tace "Kin zama wata Hajiya ko big madam zance? lallai Uncle a gaishe shi, ina Jawad? hatta maganar Sa'adah ta canja sai anfitar mata da wani salo na daban. lamarin da Zainab ta dinga dariya tana fadin ko za ki yiwa kowa wannan iyashegen ban da ni.

Suka yi dariya gaba daya sannan suka shiga hira, a gidan Mk ya tarar da ita, ta gaishe shi da girmamawa, shikuma ya dinga mata barka da zuwa cikin karamci, a dan dawowarsa da ya yi , Zainab ta fahimci abubuwa biyu, Uncle Mk ya gama lalacewa akan soyayyar kawarta, yayin da ita kuma Sa'adah take amfani da hakan take yin duk abin da take so.

Zainab ta tsinci kanta da adduar ALLAH yasa su Halima ba su jefa ta cikin HALIN YAU na bin malaman tsubbbu, domin ta tabbatar tun shekarun baya da Halima bata gama sanin kanta ba, take zuwa gidan malamai, ko aiken uwarta ko na kanta.

Har ta bar gidan tana jinjina wa Mk tana fatan Allah ya bata miji mai kwatankwacin halayyar sa.

Manyan kudade Mk ya samu a zaben da aka gudanar, saboda karamar hukumar da aka kai shi, itace mafi yawan jama'a, ganin gwamnati mai ci zata sha kaye, sai ta hargitsa zaben wannan yankin, tare da kiran Mk har gidan gwamnati a sirrince, aka tura makudan kudade a asusunsa akan ya canja alkulluman zaben, ya karbe kudin kamar yadda aka sanar da su.
bai canja alkulluman ba, amma sai sakamakon ya zama inconclusive, ma'ana bai kammala ba.

Kwana biyu yana jin farin ciki, yana ayyana indai kayan 'kawa sune muradin Sa'adah zai mata su, zai kashe mata ko nawa ne dan zamansu ya dawo tamkar shekaru biyun farko na aurensu.

Ba zato, ta ganshi da deep freezer, hankalinsa ya kwanta da ya ga Sa'adah ta yi murna, rabon da ya ga murmushinta sosai irin haka tun kafin su fara yar tsama.

Tare suka fita, suka yi siyayya mai uban yawa da tsada, hatta Sa'adah da kanta sai da ta girgiza da irin manyan laces da atamfofi super, da kuma shadda getzner da Mk ya dinga dibar mata. matu'kar tace abu ya mata kyau zaice ta dauka.
Barin takalma kirar itali da dogayen riguna rantsatsu, hatta turaren Escada da yasan tana so amma baya iya siyansa saboda tsadarsa, a wannan lokaci guda biyu ya siya mata, bayan kayan kwalliya na garari, suka zarce bakin asibitin Nasarawa, suka yiwa Jawad siyayyar hadaddun kaya masu yawa, hatta dan gidan Mahmoud da ya kasance jariri(Dady) sai da suka masa siyayya sosai.

A hanyar su ta komawa ya bata labarin inda ya samo kudi, ya kara da cewa
"Ina son na kewaye mana filinmu, a kuma fara ginin zuwa inda zai samu, a hankali kuma sai na dinga yi, har na kallama".

Ya kalleta ya ga farin cikin ta ya kasa boyewa yace "ki nutsu ki fada mini irin tsarin da kike so a miki a ginin, nasan dai kina son garden?"

Da azama tace "Da swimming pool, sannan upstairs nake so, irin wadda kafar benen zata kasance a tafken falo, a mini dining area, sannan kicin ya zama a cikin falon yake a fili, Ina fatan ka gane irin wadda nake nufi?"
Chapter 54 · 0% Book details