← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 113

Sashe 83

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har suka iso layin gidan Sumayya kuka sosai take yi, yayin da Mk ya biris tamkar bai ji ta ba, wani wula'kanci da Mahmoud ya yi mata, maimakon ya isa gidan sai ya samu gefe ya yi perking ya kunna musu a.c ya fice ya barsu, a kokarinsa na su dan sami daidaito shima kuma ya fita ya shaki isakar da zai dan samu sukunin zuciyarsa, da gaske da son Iyah zai mutu a ransa, wannan na cikin kaddararsa rashin cikar buri.

Tsawon mintina Sa'a na kuka sosai, Mk da ya tabbatar ta yi shi ba ka'dan ba, ya santa da son a rarrasheta.

Dan haka ya matsa sosai daga jikinta, ya yi gyaran murya ya ce " kukan ya isa haka My first love".

Wani azabben kishi ya duro mata na ba zata, ta sake karfin kukanta tare da cewa "karka kuma cemin first love dinka, domin ni ba ita bace, kaima kasan ba ni bace. First love dinka tana can tana jiranka wacce ba zata tsufa ba tunda bata da kamar Jawad, Ni barni a makiyarka domin bansan komai da ka mini, kuma kake kan yi mini ba Sai kiyayyya da zalunci hadi da wulakanci".

Jikin Mk ya yi sanyi ya ce da bakinki kika ce ban miki komai ba sai kiyayya da zalunci?".

Da azama ta ce "kwarai kuwa! zan kuma rokeka ka koma ka fa'dawa Hajiya da Baffah su janye dolen da suka yi maka, domin ni ba sonka nake yi ba, ko ina sonka to na ha'kura, domin a yanzu sun nuna mini ka fini a gunsu tunda sai yanzu ne zasu maka dole,to ni kuwa ina tabbatar maka na wuce haka wallahi".

Ya ce "Zan so kwarai mu fahimci juna, domin ni ban zo gurinki bisa ra'ayin wani ba, tsokanar ki nake yi, na gane ke ce cikon farin ciki na, ki zo mu rayu tare na sauran shekarun da ubangiji zai ara mana a gaba. kin san ina son ki, kin san ke kika mini laifi, na dauka ko wani kika ji ya ce na zalunce ki, zaki kare ni, amma fa'da mini me nayi miki na zalunci?"

Ta yi shiru tana kuka kasa kasa, tana jin tamkar ta tashi ta yi ta rawa dan ta nunawa duniya irin farin cikin da kasan zuciyar ta yake ciki.

Ta kasa cewa komai, ya nisa ya ce "Yanzu mu ba yara bane Sa'adah, ya kamata mu bar komai mu manta komai, mu gina sabuwar rayuwar da babu gillin bacin rai a ciki, ubangiji shine shaidata ba komai a zuciyata na yafe miki, na kuma manta komai".

"Kema ki daure ki manta duk wani zaluncin da kike ganin na yi miki, ina tsananin son na rayu da ke my Sa'adah".

Da kuka sosai ta ce "Ba haka bane a zuciyarka, kaima kasan ba haka bane, akwai dalilin da ya saka ka yafe mini amma ba dan kana sona ko dan kana son ka rayu da ni ba, daga ranar da ka jefe ni da mafi munin al'amari, a ranar na gane baka sona, wata kake so, kake neman hanyar da zaka rayu da ita, tunda ni amfani na ya kare a gurinka, ka riga ka dandana ni, shiyasa ka 'karanta tunaninka, ka kasa shaidata, ka kasa gane abin da zan yi da wadda ba zan yi ba, dama Kuma ai tun bamu yi aure ba, kake jifana da wannan zargin, yanzu kuma idan na koma maka ai cewa zaka yi har dakinka nake iskancin".

Ta nisa ta sake cewa "na tabbatar ita baka ta'ba dukanta ba, amma ni saboda rashin gata da 'kin da kake mini kanka tsaye kake duka na"

Ta fa'da cikin kuka, maimakon hankalin Mk ya tashi sai ya ji wata irin nutsuwa ta zo masa domin kuwa ya gane da gaske 'Karfi ya ke da ya ce akwai soyayyarsa mai yawa a zuciyarta duk da bakinta na kirarin 'kinsa.

Kishin Farida ke ya galgalata wannan kuwa ba yadda zata yi sai hakuri. Domin ya riga ya kudire ba zai ta'ba barin matsanancin son da yake yiwa Sa'a ya sa ya zalunci Farida ba, ba kuma zai yi kuskuren rabuwa da ita dan zai dawo da tsohuwar matarsa ba.

Bashi da burin auren mata biyu, amma tunda kaddara ta zaba masa to kuwa zai yi iya kokarinsa bai bari soyayyar daya tasa ya danne daya ba.

Cikin lallashi ya ce "sonki ne yake rufe mini ido shiyasa nake dukan ki, Amma ai kinsan iya bakinki nake duka dan shine mai dafi, amma ta yaya zan doki jikin ki alhalin shine abin hutawata. Na rantse miki banda tsoron ubangiji da a motar nan sai na shige, dan ki gane ba karamin kewar ki nake yi ba, har yau din nan 'kwarar Farida nake yi domin idan ina tarawa da ita bana samun nutsuwa, sai na ayyano ke ce a 'kasana amma kina fa'din wai ban miki komai ba sai zalinci".

Kuka sosai Sa'adah ta fashe masa maimakon ta ji da'din kalamansa, ai sai ta ji tamkar cin fuskarta yake yi, yanzu ya murde mata baki Dan ta yi jam'u ta ce wasu samarin alhalin yasan shi ka'dai ta cirewa samartaka. Amma shi yana fa'da mata yana tarawa da wata kansa tsaye.

A cikin kukan ta ce " in Sha Allah Babu sauran zama a tsakanin mu, zan yi dukkan kokarina naga ban jefa kaina a uku ba, a satin nan zan fitar da wadda zan aura, ba zan iya auren ka ba Mukhtar. Ka yiwa Allah ka rabu da ni bana sonka yanzu".

Cikin rashin damuwa ya ce "Ban damu da ki so ni ba, domin son da nake miki ya isa ya ri'ke auren mu, idan kuma kin kafe ba zaki yarda mu yi auren ba, shikenan amma ki sani ban yi al'kawarin zan iya cigaba da jarumtar kawar da ido akan ki ba, kin sanni sarai! Billahillazi ki shirya yin jegon da babu sannu, domin kuwa ciki zan miki, ki haifarwa Innah, kafin a ankara zan sake dirka miki wani sai akaiwa Hajiyar Bichi".

Gaban Sa'a ya buga da karfin gaske, mafarkin Innah ya Fa'do mata, amma sai ta waske ta daure fuska ta ce "saboda kana jin isa, ko dan ka raina gidanmu?"

Ya make kafada ya ce " whatever".

"Dan Allah Mukhtar ka bude min kofa zan fita na gaji da jin Wannan maganganun marasa azanci da kan gado".

Ya yi dariya ya ce "inace dan kin san bana son kina gatsa sunana ne yasa kike ta fa'da, to idan kin so kina iya cewa Mukhtar Kabir Bichi. Zan amsa miki amma nan gaba ka'dan Billahillazi idan akace ki fa'da ba zaki iya ba, zan fa'da miki wallahi ba zan ta bin kanki akan ki dawo gareni ba. Kina so, Ina so to karmu wahalar da juna dan wallahi kika ce zaki ja ni a kasa, ba zan yarda ba, ki rabu da Alh Mamman ban son ganin ki da shi".

Da guntun hawaye ta ce "sannu ubana, to shi nake so, domin kuwa kullum zai ta ganin yarinta ta ne, dama kuma ai tsofaffin sun fi dadiin harka.

Sosai ransa ya baci, a fusace ya dinga kwankwasa gilashin har Mahmoud ya ankra ya iso ya ja motar har kofar gidan Suka kaita, Mahmoud Yana ta faman tsokanarta ya san ai anshirya sai maganar shan biki, duk yadda take jin nauyin 'Karfi yau haushin sa take ji dan haka har ta sauka kala bata ce masa ba.

Da shigarta Sumayya ta dinga bin ba'asin kukan da take yi, bata boye mata ba, ta bata laabrin wula'kancin da Baffa ya janyo mata a wurin Mk na sawa ya kawota.

Ran Sumayya ya baci sosai ta ce "ai sai dai ki dau dangana domin kuwa Baffah burinsa bai wuce ki komawa uban Jawad ba. Duk irin bacin ran da ya jefa mu, duk irin yadda ya jingine ki shekara da shekaru, yanzu kuma dan gata da rashin kishin naka, Dan ya dawo sai ka sake bashi aure?".

Kwalla ta cika idon Sumayya tana ji a ranta Mk bai cancanci auren Iya ba, har ga Allah ta fi sonta da Anwar, amma ko ita ai ba karamin ba'kin cikin Mk ta hadiya ba.

Amma sanin maganar mahaifin su gaba take da kowa, yasa ta hadiye maganganun a zuciyarta, sannan kuma tasan komin borin da Iyah zata yi ba wadda take so irin uban na Jawad.

****

Sai bayan magariba ya isa gidansa, ya iske Farida cikin cotton din doguwar riga kirar Pakistan, kanta dauke da hular da ta dace da rigar, sai kamshi take yi, ta yi kyau sosai, amma saboda ba ita yake son gani a yanzu ba , sai yaji ba haka yake bu'katar ganin kirjinta ba, so yake ya kamo wadda zasu cika masa hannu kamar yadda dazu ya lalubo na Sa'a da nufin zai kamo bakinta.

Ya zauna a kujera ta tashi ta kawo masa ruwa da lemon coke, da cake da ta yi a yammacin yau.

Yana zaune ya rike kansa alamun yana cikin rashin sukuni.

A hankali ta ce "halan baka jin da'di ne?"

Dai-dai lokacin sai ya dinga jin muryar Sa'a na masa kuwwa tana fadin Alh Mamman take so, ai tsofaffi sun fi dadin harka.

A fusace ya mike ya ce mata "A a asibiti ne a kaina ban son katsalandan wallahi". Sannan ya wuce ya haye sama.

Jikin Farida ya yi mugun sanyi, ta zauna tana ambaton Allah.

Ta jima tana nazarin me ya same shi, kaso mafi yawa tafi zaton Sa'adah ce ta zaunguro shi, kishi ya kamata sosai, domin ta lura duk sadda ta ganshi a burkice to ba shakka itace ta birkita mata miji.

Haka ta yi ha'kuri ta kwashi abincin ta bishi da shi, abin mamaki kuma sai ya rungumeta yana fa'din ta kara hakuri da shi, Yana cikin wani irin al'amari ne da yake neman fin karfinsa Dan Allah ta kara hakuri, ta kuma yi masa uzziri.

Matsananciyar sha'awar Sa'a da ya taho da ita tasa ya kasa fita sallar isha, domin akan Farida ya sauketa, sai da suka samu nutsuwa, suka yi wanka sannan suka yi jam'i tare.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU*.
Chapter 83 · 0% Book details