← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 113

Sashe 88

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu zame ko ina ba sai gaban Hajiyar Bichi suka fa'da mata abin da Alh Isa ya ce.

Ta yi jugum ta ce "Ashe kuwa Allah ne ya so ni domin wlh ni kaina kunya ce ta sa nake ta jan kafar zuwa gidansu Sa'a, yanzu kuwa na fasa ba zan iya ba, maganganun Babanku akan turba suke, yanzu ne kake so mu shige maka gaba alhalin a farko ka nuna musu baka da iyaye".

Hankalin Mk ya yi tashin gauron zabi.

A hankali ya ce " Amma Hajiya da bakin ki kika ce zaki rarrasar mana ita".

Ta ce " eh na fa'da amma yanzu na gane bai kamata na shiga ba, domin a lokacin da yarinyar nan take cikin tasku ai baka yarda na yi iko irin na uwa da kai ba, ka ga kuwa bai kamata ace yanzu ita na yi mata karfa-karfa ba, tunda na san da dukkan zuciyarta tana sona tana girmama ni, ku je Mahmoud ya taya ka, zan biku da addu'ar dacewa ubangiji ya huci zuciyarta, amma ni kaina ban jin zan iya yafe irin abin da ka yi mata idan aka yi mini irinsa".

Idonsa ya ka'da ya ce "wai har me na yi ne haka Hajiya? Saboda na zabi na bar abin da ta mini a zuciyata shine kuma sai aga ni na zalunceta, na san dai laifin bai wuce kawai dan na yi aure ba".

Daga 'Karfi har Hajiya suka hada baki wurin cewa " Ai kuwa ya fi karfin ace kawai, kai yanzu ka barta ta auri wani mana indai kawai ne".

"Bana son haka 'Karfi bana son wannan kwatancen"

"A a ba da Mahmoud kake ba, da ni kake, ni kuwa ba yadda zaka yi da ni, domin ko yanzu Sa'a za ta yi wani auren da kaina zan jagorancin kaita dakin mijinta".

"Dan ka ji irin ciwon da ta ji alokacin da ka tura ubanta ya nemo maka aure".

Da rawar murya ya ce "Haba Hajiya! Haba mana! ni ban tura Baffa ba, kawai na fa'da masa zan yi aure, shikuma saboda yana mini kallon Ni 'da ne a gunsa ya shiga cikin harkar tsundum, amma menene laifi na anan?"

Hajiya ta ce "Baka da laifi ko kadan, yanzu na gane kawai sanin ya kamatansa ne ya yi yawa. Bai kamata kuma ka ji haushi dan nima zan nuna irin nawa ya kamatan ba".

Tashin hankalin da Dr 'Karfi ya lura ya fara bayyana a jikin Mk yasa shi cewa "Ha'kuri dai zaki yi Hajiya, dole a samu Babban da zai taya mu nema da rarrashi"

Hajiya ta ce "To sai kuje ku laluba a wani gurin ko za'a dace, sai ku tafi Bichi ko 'Karfi ku samo ai hidimar dan dangi bata lami".

Daga haka ta ce "Na sallame ku sallar walaha zan yi".

Kwanaki biyar Mk ya na fama da matsanancin kishi da damuwa domin ya kasa ganin Iyah sannan idan zai kwana yana kira ba zata dauka ba, ya lura idan bata ganinsa ta fi jarumta sabanin idan idanuwansu suka sarke da na juna zuciyarta take kasa boye sonsa da yake cikinta.

Har gidan Sumayya ya je amma bai Samu ganinta ba adalilin ta cewa mai gadin ya ce bata nan, tunda ta san ba su yi da Alh Mamman ko Anwar wani zai zo ba.

Ranar juma'ah bayan masallaci ya samu Baffa a shagonsa a kuma ranar ya dawo daga Gogel.

Da sakakkiyar fuska Baffah ya ce "Ina fatan zuwa yanzu ka shawo kan mutumiyar taka ta daina fishin kun shirya kanku?"

A raunane Mk ya ce "Ai sam ta'ki saurarona Baffah, jiya har Bichi na je wurin su Baba umaru akan su zo, su bawa Baba Isa hakuri, sai kuma su zo wajenka, amma kowa ya ce shi ba zai zo mini ba, kunyar abin da na yi maka suke ji".

A filin gurin Mk ya durkushe kan guiwowinsa ya ce "Ina sake bada ha'kuri Baffa! Ba zan ta'ba gajiya wajen neman afuwa da alfarmar kar ka kullace ni ba, kaddarar mu ce a hakan amma ba da gangan na yi hakan ba".

Baffa ya dago ya ce" Tashi ka zauna kada ka 'bata rigar ka"

Sai da ya nisa ya ce "kullum ka yi mini irin wannan rokon Mutari ina jaddada maka ba auren Iyah bane ya hadamu, ba kuma zai zama silar rabuwarmu ba! Yanzu kana tunanin har sai ka sake turo mini iyayen ka da na baka aure? Kawai wadda zai karbar maka ne zaisa na jira sai anzo tunda dai dole iyayenka da jini ya hada ku, sune a hakku akan ka, indai ba ina son na shiga al'amarin zumunci ba ne, ka kwantar da hankalinka ni sai na je na same su da kaina, a ko ina ni mai Nemo maka aure ne, ni so nake ka shawo kanta ko yaya ne, kasan tana yarinyarta ma cewa na yi ka nemi yardarta, to yanzu ma nemi yardarta ko ya ya ne idan ya so sai naga ta yadda zan bullo mata".

Mk ya dinga godiaya yana cewa "Baffa gaskiya idan ba taya ni ka yi ba, ba saurarona zata yi ba".

Farin-cikin Baffa ya kasa 'boyuwa saboda yanzu ya gamsu idan Iyah ta koma hannun Mutari zata yi daraja sabanin shekarun baya da ta koma din sai dai ta yi zaman hakuri da taka tsantsan.

"Ya labarin Jawad kuwa?"
Baffah ya tambaya.
"Rana ita yau ne hutun su in Sha Allah".
Murmushi sosai ya bayyana a fuskar Baffah har ransa yake jin kaunar Jawad fiye da ta su Khalifan Sumayya, wata'kila soyayyar uwarsa ce ta shafe shi. Ko da yake ai Mk ma na daban ne a wurinsa.

Kamar da rada Baffa ya ce"tana cikin gidan dazun nan ta zo mini barka da zuwa, je ka ku gaisa mana".

A kunyace Mk ya ce "Bata daukan 'kirana, har gidan Aunty Sumayya na je amma bata fito ba"

Jeka dai yanzun! Ina hango ka shiga zaure zan mata waya ta fito kamar zata karbi sako".

Mk ya rasa mai zai ce a duniya idan aka cire iyayensa biyu ba wadda yake sonsa yake karrama shi irin Baffan Sa'adah.

A matu'kar kunyace ya ce "Baffah na gode sosai Ubangiji ya fini yabawa, in sha Allah komai Iyah zata mini zan yi ha'kuri da ita muddin rai, ina maka al'kawarin zan ri'ke ta fiye da ri'kon farko, ka bimu da addu'a".

Da sakakkiyar murya Baffa ya ce " Bana jinka Mutari! Amma yau zan fa'da maka wani abu da ba wadda ya sani sai ni da ubangijin zuciyata.
Iyah itace abu mafi soyuwa a gare ni, ban taba mallakar wani abu da ya fita a gurina ba, ko mutuwa na yi idan kana ayyana ina ma ina nan da ka mini kaza. Na ro'ke ka duk abin da ka raya a zuciyar ka zaka mini na kyautatawa to ka yiwa Iyah shi. Basu da 'dan'uwa namiji ka taimake ni ka zame mata miji kuma 'danuwa, ta wahala akan ka, ta yi kukan rashin ka, na ro'ke ka kar ka bari ta yi kukan ita ubanta talaka ne, amanarta nake baka".

Hawayen tausayin Baffah ya kwacewa Mk ba tare da ya shirya ba, amma yasa dukkan karfin zuciya ya ce "Na karbi amana, na karba da dukkan zuciyata, zan taya ka sonta, zan jiyar da ita da'di, sai dai yau da gobe dole za'a samu sabani, mussaman da yake ita din Yar daru ce sosai. Wata'kila sai kana mata rubutun rage daru Baffah".

Murmushi sosai ya yi "ya ce zungurar ta kake yi Mutari, amma yanzu ai ta girma ta yi hankali wani abin ba zata yi su ba! Jeka kar lokacin maghrib ya karaso baku gaisa saosai ba".

Yana isa bai fi da minti biyu ba, ya fara jiwo takun dogayen takalmanta mai tsinin gaske, kamshin ta ya riga ta isowa. Kwalliyarta na cikin abubuwan da ba zata iya dainawa ba.

Ta karaso cikin taku 'dai'dai tamkar wata hamshakiya sanye cikin Riga da skirt na atamfa kalar ruwan hoda da fari.

Dinkin ya zauna tamkar a jikinta aka yi su.

Farin mayafi ta sanya dan haka takalmin kafarta ma fari ne mai tsananin tsada, da Mk ya lura zai gane wanda Jawad ya sa shi siya dole ne, wadda fa'dan kudinsa a lissafin naira sai aga tamkar fariya ce zata sanya a zuba wannan ma'kudan kudin a siyi takalmi kafa daya.

Sosai ta yi kyau domin ta zubawa fuskarta kwalliya, hakanan sabon kitsonta na shuku ya taimaka wurin kawata daurin dan kwalinta.
A ransa ya dinga yabon kyaun halittarta. Ya dinga tasbihi da hamdalar yadda aka jefa soyayyarsa a zuciyar wannan halittar da take tsananin daukan hankalinsa, duk tsawon shekarun da ya shafe a duniyarsa bai ga wadda ta zarta Sa'a iya tsara kwalliya ba.

Bai ga wadda take zuba ado iya ado ba tare da fita zata yi ba, ya fahimci tana samun farin ciki a cikin kwalliya, bata ta'ba bashi matsalar wai bai yabi kwalliyarta ba, yi take domin ta zame mata jinin jiki.

Ta wuce shi tamkar bata ganshi ba, ta fita kofar gidan, ta shafe minti biyu a tsaye, yayin da zuciyar Mk take wani irin bugu, mayafin jikinta iyaka cinsa kafadarta wadda tunda ga kanta ta na'de shi, gata a tsaye skirt dinta ya matu'kar fito da zahirin surarta, ba namijin da zai kalleta ya tsaya a iya kallon sharia guda daya, dole sai ya sake yin kallon bawa ido hakkinsa.

Mk ya dinga jin wani irin tashin hankalin yadda take tsaye a tiiti a hakan, anya akwai wadda ya saki matarsa a duniya amma yake dandana kudarsa kamarsa?

Can ya juyo ta tana cewa"
Baffa na dade da fitowa banga kowa ba"

Ta juyo da nufin shigewa ta bar shi fuskar nan daure tamkar hadarin da ya gama tunbatsa.

"Zo mana Dawisu sarkin ado, ni ne mai baki sakon ai".

Ta yi kamar ba ta ji ba, ta doshi hanyar shigewa da azama ya sha gabanta, ya ce "kwanakin baya fa a gabana Baffa ya ce miki ko rago ya kawo ya kamata ya shiga rigarsa".
Chapter 88 · 0% Book details