← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 113

Sashe 110

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayin da ita kuma tana sallah tana kuka, tana ro'kon ubangiji ya sassauta mata kishi, ya bata jarumta da ha'kurin danne shi.

Kwananta hudu wata babbar motar daukan kaya ta zo shake da kayyaki, yini guda aka yi a bagaren Farida har washagari suna fama.

Ranar da juma'a kuwa wadda yayi dai-dai da satin Sa'a daya a gidan Mk ya dauko Farida da kansa.

Kai tsaye bangaren Sa'adah suka yada zango, cikin 'karfin hali ta karbe su, ta gabatar musu da ruwa da lemo har da abinci.
Cikin son K'ulla alaka a tsakanin su, Mk ya ce " kin zuba mana abinci tare, ke kuma kin koma gefe, dauko cokali kawai muci tare".

Ta daure ta ce "Na riga da na ci tun
'dazu".
Kallonta kawaya yi ya gane bata ci ba, sannan kokawa kawai take yi da zuciyarta.
Dan haka sai ya mike ya dauko mata spoon din da kansa.
Ta karba suka ci dukkansu uku a plate 'daya.

Ba magana sai karo a tsakanin cokula da plate.
Sai da suka kammala ya yi musu addu'a! Sannan ya roke su arzikin su zauna lafiya da juna, bayan ya tabbatar musu zai yi iyayinsa ya yi adalci a tsakaninsu, ya tabbatar musu dukkansu yana sonsu dan haka ba wadda zai musgunawa da gangan, ranar da aka samu akasi ya 'batawa wata, to ta yi masa uzziri yau da gobe ne, sannan dole idan ana tare dole a fuskanci matsaloli, sai dai kar a bari matsalar ta yi girman da ba zata gyaru ba.

Ya nisa ya kalli Sa'adah da kanta yake 'kasa ya sassauta murya ya ce" Sa'adah ta dago ta kalle shi sannan ta ce "Na'am"!

"Ku fa'da mini tsarin da ya muku wurin rabon kwana"

A sanyaye ta ce "Farida fa'di yadda zai yi".

Cikin nutsuwa Farida ta ce "Majority anfi yin kwana biyu, mu barshi a hakan mu ma".

Ya sake kallon Sa'a ya ce "Hakan ya yi miki?"

Ta amsa da "eh" a hankali.

Ya sake yi musu nasiha tare da shawartarsu su sanyawa ransu zaman ibada zasu yi, yin ibada tsabtatacciya kuwa sai mai hakuri mai kuma Imani na gaske.

Ya mi'ke yana cewa Sa'aadah "muje ki yi mata rakiya".

Ta bisu ba dan tana so ba, sai dan kar ya ga gardarmarta.
Da gaske ta dauki aniyar canji.

Suka isa bangaren Farida da ya 'kawatu da kaya na garari.

Duk yadda Sa'adah ta yaba haduwar bangarenta, da ta ga yadda aka narka dukiya a wurin Farida sai da ta girgiza matu'ka da gaske.

Jikinta ya sake mutuwa, bata fi mintina biyar ba ta mike tare da cewa"Allah ya sanya alkhairi".

Itama Faridan ta mike tana cewa "zo mu shiga mu ga gidan sosai mana".

Akan dole Sa'a ta bita, ta ga 'dakunan da suke falon wanda 'daya tsarinsa ya tabbatar mata Jawad aka shiryawa dakin.

Akwatuna da ta gani guda uku set, masu tsadar gaske, ya tabbatar mata kayan fa'dar kishiya Mk ya yi mata, Amma ita ko akwati 'daya bata samu ba.
Sai dai take ta tuno milyoyin da ya kashe mata, sai ta yarda ta kuma gane ba laifi ya yi ba.
Ta riga ta gamsu Mk bai kai 'karfin da zai zuba irin wannan kayan ba, ta kuma yarda idan har yana da ku'din yin hakan to ita zai fara siyawa.

Suka gama da dakunan suka yi kicin da yake shake da na'urorin zamanin da ba zasu lissafu ba.

Sa'a taki yarda da shiga dakunan su na cikin corridor wadda ta tabbatar sai ya ninka na falon 'kawatuwa.
Tunda dakunan Farida da Mk ne.

Har bakin kofar Farida ta rakota sannan ta juya ganin Mk na waje, ta sani rakiya zai yi mata, tunda wurinta yake ma'ana Faridan ce mai girki.

Sa'adah tana ganin Mk ta wuce shi fuu tamkar bata ganshi ba, ganin haka ya bita yana 'kiranta amma bata tsaya ba.

Har suka isa bangarenta, ta zauna a falo ta fashe da kuka, jikinsa na rawa ya ru'kota, ai kuwa ta dinga dukansa ta ko ina, ganin dukan ba mai illah bane, sai ya sunkuya mata sosai ta yadda zata ji da'din dukan nasa.

Sai data gaji dan kanta sannan ta barshi, shikuma ya janyota ya rungume.

Ya dinga karfafa mata guiwa, tare da zugata, har ya samu ya zagwanyar da rikicin da ya taso mata.

Sai da ya kaita har 'dakin barcinta, ya jira ta yi wanka, ta kwanta ya lulluba mata bargo.

Sai a lokacin ta ce "Malam" !

Ya amsa Mata da cewa "Na'am my dear Iyah"!

Cikin rauni ta ce "Amana dai itace amana! Haka cika alakawari sai mai Amana, kar ka bari a kwace mini kai, kar kuma ka saba al'kawarin ni zan jagoranci zuciyarka".

Ya kamu da tausayinta! Ya sani irin kayan alatun data gani an zubawa Farida shi ya sanya ta karaya.

Ya matsa jikin gadon ya ru'ko hannuta ya ce "shekaru uku na yi da aure amma ba a kwace miki ni ba, sai yanzu da muke tare?"
Ki daina shakku Malam 'din kine har yanzu, har kuma gobe".

Hawaye ya zubo mata ta ce "Na gode sosai! Sai da safe".

Ya ce ai ba zan iya tafiya ban ga murmushinki ba".

Ta kuwa murmusa sosai, ya sunkuya ya yi pecking dinta yasa hannu ya shafa cikinta.
Ya ce Good night and stay blessed".
Ya kashe mata fitila ya fita.

Ta dinga shafa daidai inda ya shafa cikin, tana Jin kaunarsa na ratsata.
Ta nisa tana hakaito kayan da Mk ya siya ya zuba mata ta tabbatar duk yadda Ma'aikatar shari'a take da albashi mai tsoka, sai ta shafe shekaru uku zuwa hudu kafin iya tara kudin siyan irinsu, ta tabbatar Farida kuwa iyayenta suka yi mata.

Ta share hawayenta tana Jin tabbacin ko a birnin Abuja ba za'a raina mata nata kayan ba.

Satin da ya zagayo aka yiwa su Jawad hutu.
A hanyar su ta dawowa ya ce "Malam".

Mk ya amsa da cewa"Jawad".

"Dama wannan hutun ma ka ce mini ina nake son yin hutuna?"

Dariya ta kama Mk ya ce "Dama ka bari muje gida tukun".

Suka wuce Gadon 'kaya Jawad ya ce "Malam zamu biya wani waje ne? Na ga mun wuce hanyar gida".

Ya ce "Na manta wani file a office ne, shine zamu je na dauko".

"Ok" Jawad ya fa'da a gajarce.

Suka iso mai-gadi ya bude musu.
Jawad ya kasa hakuri, ya ce Malam ko kun yi parking zuwa wannan gidan ne?"

"Mun dawo last two weeks"
Mk ya amsa masa.

Farida tana wurin aiki.

Kai tsaye bangaren Sa'adah ya nufa da shi, bata falo, Jawad ya fa'da kan kujera ko sandal dinsa bai cire ba.

Ya ce "Wow falon nan so mashallah! Ya 'dago a zabure ya ce Malam amma ka san me nake ji?"

Kafin Mk ya yi magana ya zarce da cewa!

"Ina jin irin 'kamshin gidan Maman Gombe (Sumayya) sannan ina jiyo 'kamshin Mamina! Aunty ta canja turare ne ko kuwa kewar Mami da nake yi ne?".

Mk ya zuba masa ido yana gasgata kaifin kwakwalwar yaron.
Kafin ya bashi amsa Sa'a ta fito cikin tattausar yadin material doguwar riga bubu, ta yi kyau sosai.

Jawad ya daskare a zaune, ya murtsuka idanuwansa yana son ya tabbatar ba Farida ce take yi masa gizo ba.

Ya budesu sosai ya tabbatar itace mussaman da kamshinta ya sake cika gurin.

Ya kuwa fasa ihu ya kwasa a guje zai wawurota.

Mk ya yi hanzarin ru'ko shi ya ce "Wallahi ba zaka ka kayar da ita ba, tana fama da kanta.

Da Jawad ya rasa yadda zai yi, sai kawai ya yi tsalle ya 'dane Babansa.
Yana fa'din thank you world best Father!
Ka cika promise, na dawo na tarar da Mami a gidanmu, thank u very much Malam".

Ya sauko ya nufi uwarsa cikin nutsuwa ya rungumeta, haka kawai sai ya tsinci kansa da fashewa da kuka.

Itama ta dinga hawaye. Mk ya kallesu da tarin 'kauna ya ce "To kukan kuma na menene, ban da dai kin 'bata shi da kukan shagwaba, maimakon ki hana shi sai ki taya shi kuma?"

Bata kula shi ba, ta ja hannun Jawad ta zauna akan kujera shi kuma ta dora shi a cinyarta tamkar 'dan shekaru biyar.

Da azama Mk ya mayar da shi kan kujera ya ce "Ban son haka! sai ya buge ki? Ai kinsan ba lafiya ne da ke ba, da zaki sun'kuma wannan 'katon yaron a cinya, garama a samo masa 'kanne da yawa, ko ke da shi kwa yarda ya girma".

Tissue ta dauko tana goge fuskarsa tana fa'din "is ok, ya Isa haka".
Sun dade kafin su samu kansa ya daina kuka.
Sai da ya yi wanka a dakinsa da aka shirya masa da kayan katako irin na 'kasar Turkey

Ya fito falon yana cewa "Dakin nan nawa ya birge ni, ya mini kyau".

Mk ya tuna kayan da Farida ta siya ta zuba masa a dakinsa na gidan gadon Kaya, masu tsananin tsada, amma bai ta'ba nuna sha'awarsa ba, bare ya yaba.

Ya sake hakaito a yanzu haka dakinsa na bangaren Farida ya ninka wannan 'kawatuwa, amma ya san halin Jawad sai ya fi son wannan saboda shine na side din uwarsa.

Yamma liss Farida ta dawo, a ranar Sa'adah ta karbi girki.
Da ke Jawad a Farin ciki yake da sauri ya je ya yi mata barka da zuwa.

Sai da dare ya yi Mk ya rufe ido ya ce Jawad ya tafi dakinsa na bangaren Farida ya kwana a can.
Akan dole ya tafi, Sa'a ta bishi da Ido.

Washagari tun sanyin safiya ya dawo side din uwarsa haka kullum yake yi.

Rannan Mk ya balbale Sa'a da fa'dan itace bata nuna masa ya dinga zama a wurin Farida.
Murya na rawa ta ce "Kullum ina yi masa fa'da, ji ne ba ya yi".

Yana fita ta kalli Jawad da yake rakube a gefe ta ce "Ka ji da'di, da ka janyo mini bacin rai".

"Ni wallahi Mami na gaji! A U.k. ba ayin haka, kowanne yaro ana barinsa ya rayu a inda yake so, bare ni da nake so na zauna tare da uwata".
Ya fa'da da bacin rai.

Mk da ba nisa ya yi ba, ya juyo daukan wayarsa.
Chapter 110 · 0% Book details