Sashe 57
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata cikin su, tana bude Baki ta ce "Amma kuma matan aure sun muku zarra da mutunci da kuma 'kima, macen aure tana tsufa tana sake daraja, adalilin gatan da musulunci ya mata".
Dukkan su suka sa mata dariya, suna ganin wautarta, Lubna ta ce "kai ku rabu da Hajara kunsan tunda ta gama wannan makarantar ba ta sake shiga aji da nufin zurfafa ilimin ta ba, kenan kanta a duhu yake bata san komai ba, tana cikin jerin matan da maza suka rufe a gidaje suke gallaza musu, suka kuma hana su fahimtar cigaban da duniya ta samu"
Su Halima da suke jin tattaunawar suka kwashe da dariya suna fadin "ai yanzu duk wadda ta zauna namiji na mata mulkin kama karya mata ta rako duniya, a wannan karnin da ilimi shine komai yaushe zaka yarda a barka da jahilci, barin ma idan mijin naka mai ilimi ne? Da zarar muguntar namiji ta motsa sai dai ki ji ya amarce da mai ilimi, ko kiga yana jin kunyar ya saka ka a al'amuransa".
Jikin Sa'adah ya yi sanyi ganin itama cikin rukuninsu ita kadai ce mai sakandiren, haka akayi ta kutsiri tsoma, ba a gama da wannan maganar ba, a saketa a kamo wata, da za su tafi, a motar Safina suka dunguma har kofar gidansu suka kaita, a hanya suka yi hirar Humaira Suraj da a yanzu take aure a sokoto, dama can ne garinsu aiki ne kawai ya kawo mahaifin ta Kano.
Tun wannan lokacin Sa'adah ta fara canjawa, ita da kanta tasan ba abin da ta nema ta rasa illah motar kanta ba wai ta Mijin ta ba, amma zuciyar ta sai tsalle take mata tana ganin kamar ita ta wuce komai sai ta jira iznin miji kafin ta zartar, tana bu'katar ta zama yantacciyar mace mai yin komai babu 'dar balle fargaba.
Kullum a WhatsApp su Halima na sake kuranta kyakkawar siffarta, har suna cewa ba wadda zai ganta yace ita ta haifi Jawad, ko su da suke 'Yan mata basu fita komai ba.
Suna cikin wannan zaman na ba yabo, ba fallasa, Su Halima suka zo mata da kaya cike da katuwar leda, kana ganin ledar kasan tafiyayyace, sai da aka bude kaya, suka ga kayan Jawad ya kai set biyar, sai agogo na English gold, da kuma waya blackberry bold 4, da tarin alawowi da biscuit duk tsaraba ne inji Khalil abawa Jawad waya da agogo kuma nata ne.
A kidime Sa'adah ta ce "Na shiga uku Safina idan Malam ya gani fa, da me zan kare kaina? Gaskiya bazan karba ba tsoro nake ji.
Harara Suka galla mata, Halima tace "to kuma barinsa zaki yi ya gane daga inda suka fito, sai an kwana biyu kice Anty Sumayya ce ta aiko muku, waya kuma ki boye abarki sai ba ya gida, ko idan zaki je taron fitar kunya, na gaji da ganin ki da karamar android shiyasa na fa'da masa baki da wayar shiga taro".
Safina ta dora da cewa "Da yake ya damu da farin cikin ki kasa da awa ashirin da hudu da fa'da masa ya siyo, ya bayar akawo miki, gaskiya Gogel kin tafka asarar masoya, na tabbatar ko yanzu da kika zama uwa, Khalil zai aure ki a matsayinsa
na saurayi".
Suka hada baki wurin cewa "duk da ke 'din ma kinfi 'yanmata da yawa nagarta".
Tun lokacin hankalin Sa'adah yafi karkata kan wayar nan, kullum Mk ya fita za ta fito da wayar ta, ta yi komai, mussaman take da layi na daban a ciki, amma da layinta ta bude komai.
Tun Mk na tambayar ba'asin canjinta har ya gaji, yana ganin ya kyaleta ya huta shima, dan taga yana damuwa ne shiyasa take masa wulakanci, dan haka ya rungumi sabuwar rayuwar da ta bude musu, hatta a shimfida ta canja, ba wai gudunsa take yi ba, kawai zama take yi tamkar gunki, sai dai ya yi kidansa ya yi rawarsa shi ka'dai.
Haka nan abu kadan Jawad zai yi ta rufe shi da duka tamkar wadda take dukan babba.
Wadannan dabi'u suna matu'kar ciwa Mk tuwo a 'kwarya mussaman dukan yaron da ta tsira, ko abu ne ya hadasu sai ta huce akan 'dansa.
Rannan suna kwance sun gama mu'amalar da ba gishiri a cikinta balle Maggie, ran Mk a bace yake sosai, ya rasa mai zai mata kuma, ya riga ya kai gejin rarrashinta, ya gane gaba'daya kwakwalwar kifi ne da ita.
Ya yi gyaran murya ya ce "tsakanin ki da Allah ki fada min me kike nufi da ni, rokon ki nake yi, yanzu na tabbatar ba kya sona Sa'adatu".
Yana rufe baki ta ce "Kaine dai baka sona, komai zan yi a laifi na ke, 'dazu ba ka ga irin 'barnar da Jawad ya mini ba, dan na dake shi, ka hayayya'ko mini, salon kasa ya raina Ni".
"Amma tun ba yau ba ki ke wannan fizgewar, yaushe rabon da ki saurare ni cikin da'din rai, kullum da bacin rai kike yarda da ni, ko kin yarda kai tsaye to sai dai ki zame mini tamkar gawa, anya kuwa dama kina sona? anya kina jin tsoron hakki na akan ki, amma na yafe miki, na kuma dauki laifin ko menene ki yi hakuri ki yafe mini".
Ta tura baki ta ce"Tun yaushe nake ce maka zan dubo mahaifiyar Halima da ta yi hatsarin mota, duk yan ajin mu sun je banda ni".
Murya ba amo ya ce " Hana ki dubo uwar Halima yasa ki ka na'de kafar wandon yin min wula'kanci haka?"
Ta yi shiru ta kasa cewa komai saboda ta ga ya hassalo sosai, ya furzar da iskar bacin rai ya ce "Shikenan ko da wani laifin bayan wannan?"
Kamar shasha ta ce "yauwa ni fa yanzu nake son motar nan, na ga kai kuma kana nufin kamar sai anja lokaci, kawai ka dakatar da ginin ka siya mini".
Ya kalleta ido cikin ido ya ce "yin hakan shine sharadin samun zaman lafiya a tsakanin mu?"
Ta kasa amsawa tsawon lokaci, dan haka ya ce "Ba wadda zan miki ko 'daya, idan ya so zaman namu yafi haka muni".
Ta tashi ta fita tana 'kun'kuni, akan sai ta je, ta gaji da 'yadda ya maidata bagidajiya marar yanci, kansa ya sara yana jin ba'kin cikin ta na neman kassara shi.
Haka har kwanaki uku suna zaman doya da manja, Rannan cikin dare ta ji hannunsa na lalubarta, ta zabura kuwa ta bige hannun, tare da fadin "Bana so".
Bai saurare ta ba ya damko ta, ya fara kokarin gwada mata 'karfi saboda ya gaji da rarrashinta.
Ganin da gaske zai cimmata alhalin ta riga ta kudiri aniyar ba za ta saurare shi ba.
Dan haka ta fashe da kuka ta ce " raping dina za ka yi? na fahimci bani da mutunci a gurinka indai ba bu'katarka ce ta ciyoka ba, na daina ganin aibun 'yantattatun mata wadda suka juyawa aure baya, saboda sun san ba komai a cikinsa sai ba'kin ciki da takura da kuma 'bacin rai".
Jikin Mk ya mutu yana rike da ita, da ta lura, tashin hankalin da ke zane baro baro a fuskarsa ba zai bari ya ci gaba da rarrashinta a YAU kamar yadda ya Saba ba.
"Matan da suke zaman kansu, duk abin da suke so, aguje suke samu, amma matan aure sune agaba wurin samun hawan jini saboda tsabar bakin cikin da mazajensu suke 'kulla musu".
'Kololuwar tashin hankali Mk ya shiga, ji yayi jiri ya kwashe shi dan ma a zaune yake, ya tafi luu ya buge 'keyarsa da fuskar gado.
Da kyar ya dauki hannunsa ya ri'ke kansa da yake tsananin sarawa, da karfi ya dinga ambaton" innalillahi wa Inna ilaihir raji'un".
Ya dade yana nanata kalmar, har ya dan sami nutsuwa kadan, ya mike ya saka rigarsa da wando, ya ware murya sosai ya ce "Ni ki ka fadawa wannan maganar? Ashe kuwa har yau baki gane ni ba, zan nuna miki ba a bariki muke ba, ba kuma auren bariki na ke yi ba, ki ri'ke dukkan abin da ki ke tun'kaho da shi bana so, ki ji'ka ki shanye abin ki, amma ki sani yau da Gobe zasu biyar da ke indai kina sha'kar numfashi".
A daren ya dauke dukkan abin da yake nasa ne a cikin dakin Sa'adah, sai Agogon hannunsa da yake cikin wadirof dinta ya manta bai dauka ba. har ya kwanta ya tuna bai dauko tawul dinsa ba, ya koma ya dauko, kafin ya fita ya tsaya ya kalleta tana zaune duk jikinta ya saki da alamun ba tasan girman munin maganar data furta ba, sai bayan ta fada.
A kausashe ya ce "Na tsane ki, na tsani na bude ido na ganki, ba dai kin fi sha'awar rayuwar 'kazanta akan ta sunnar Ma'aiki ba? kin raina duk kokari na, kin raina ni'imar da kike ciki, Na rantse miki! ba dan kunyar Baffa ba, da a yau na mayar da ke 'yantacciyar macen da kike fata, ni kaina NADAMAR auren ki na ke yi, amma na gode Allah da nake ganin sakamakon son zuciyata a duniyar nan, ba sai naje lahiraa ba,'kiri 'kiri na nunawa mai sona da gaskiya HALIN YAU, na butulci".
Ya juya ya fita ya barta cikin rashin sukuni mai yawa.
Tun daga ranar ya bala'in dauke mata wuta, idan ya fita tun safe, sai dare ya fara turawa zai dawo, sannan matu'kar yana gida to kuwa kofar dakinsa a gar'kame ta ke hatta Jawad ba kasafai yake ganinsa ba, kullum cikin tambayar Sa'adah Ina Malam ya tafi?".
Wannan ne karon farko da ya yi fishi ba waiwaye, hatta fuskarta baya son gani a yanzu, sabanin da da ganinta shine cikon farin cikinsa, har yau fama yake da ciwon da bakaken maganganun suka sababa masa a zuciya yake yi.
Ana haka mijin Sumayyah ya yo waya akan bata da lafiya sosai, haihuwa ne ta zo mata da tangar'da anmata C's an fito da yaro amma kuma bata da lafiya.
A ranar Baffa ya sanar da Mk, akan gobe za su yi asubanci zuwa Gombe shi da Inna, idan ba damuwa ko zasu tafi da Iyah ta gano jikin yar'uwarta.