← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 113

Sashe 73

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mukallin mota ya 'dauka da sauri akan center table din da ke tsakiyar falon.

Ya kalli Mk da ke kishingide bai da niyyar tashi, ya ce "ko na je na dawo?"

Kai kawai Mk ya iya 'dagawa a dalilin mutuwar jiki, saboda yadda al'amarin Sa'adah ke damunsa.

A hanzarce Mahmoud ya fita ya na fadin "saboda gidan ba kowa yasa ka yarda ka zauna".
Da yake matar Mahmoud din sunje Kaduna bikin cousin sister dinta sai jibi zasu dawo.

Mahmoud na fita 'kofar gidan inda ya ajiye motarsa, bai shiga da ita cikin gidan ba, saboda yasan ba wani jimawa zasu yi ba, kawai sai ganin Sa'adatu ya yi tana bawa mai adaidaitanm sahun da ya kawota, ku'dinsa.

Da sauri ya karasa kusa da ita yana mata barka da zuwa, yana jin wani irin yanayin da ya ganta a ciki, alamun rashin lafiya da rasnin kwanciyar hankali baro baro a jikinta.

Ba dan 'karfin dangantakar sa da Mk ba, da ya aure yarinyar nan ko ya huta da motsawar da zuciyarsa ke yi a duk sadda zai ganta, kai so masifa ne, Madallah da mutanan da suke sadaukar da soyayyar su dan halacci, aminci, ko
masalaha.

Suka gaisa, ta tambayi iyalinsa, Har zaice matarsa bata gidan, sai kuma ya yi shiru, ya ce "ki shiga, zan je na dawo". Ya dinga addua da fatan sulhu a tsakaninta da Mk.

Tana shiga, kai-tsaye bangaren matar gidan ta dosa, ta dinga knocking, jim ka'dan Mk ya leko daga bangaren maigidan yana cewa "iso nan, bata nan matar gidan".

Ta shiga falon da sallama, ta gaishe shi, sai kuma ta kasa magana, sun Jima a zaune suna ta sake-sake a zuci.

Mk ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "ina jin ki, kin ce zamu yi magana".

"Malam da gaske ne wai aure zaka yi?"

Zuciyarsa ta buga, mamaki ya kama shi na yadda ya ji fargaba ta kama shi, saboda yadda ta yi tambayar muryarta na rawa. Ya kasa koda motsi, hakan ya tabbatar mata da gaske auren zai yi".

Hawaye ya balle mata, ta ce " Na shirya fa'da maka gaskiya".

Ya ce "Ina sauraron ki, waya baki kayayyaki nan?"

Cikin kuka mai yawa ta ce Khalil ne! ya bani agogo da rigunan Jawad tsarabar Egypt, shine ita kuma Halima ta ce da ya bar agogon ya siya mini waya! sai kuma ya hado har da wayar".

Ransa ya matu'kar baci tamkar yanzu abin ya faru, ya fesar da iskar bacin rai, ya ce "Ta hannun wa sa'kon ya same ki?"

Da kukan ta ce "wallahi Safina da Halima ne suka kawo mini! wannan itace gaskiyar magana ban munafunce ka ba".

Idonsa ya ka'da ya yi jawur dan tsananin kishi, ya ce "Munafunci kuma na nawa Sa'a! Ni dai kafin ki yi hakan wallahi ban ta'ba tunanin zaki mini wannan Munafuncin da aurena akan ki ba".

Kukan Sa'adah ya 'karu ta ce "Tsautsayi ne, ban ta'ba yin haka ba, wallahi a lokacin da kayan suka zo sai da na ce tsoron kar gani nake yi ba zan karba ba".

Ransa ya sake ri'banya baci a tunzure ya ce "Amma da suka fa'da miki Ni 'din banza! sai kika karba, mussaman da suka nuna miki idan ma na rabu da ke ga wadda ya fini 'kuriciya da kudi yana son ki ko?"

Ganin yanayinsa ya sake tada hankalin Iyah, saboda rikici ne zallah cikin idanuwan sa irin wadda bata ta'ba gani a tare da shi ba.

Da sauri ta ce "Wallahi Malam.."
Ta yi shiru sakamakon harar da ya watsa mata ya ce "Idan kika 'karyata ni wallahi zan miki duka, ki kiyaye ni".

Ta yi shiru sai kuka kawai ta ke yi wadda Mk har cikin zuciyar sa yake jin kukan, ya yi shiru yana sauraron kukan, sai ya dinga jin ashe har da kukanta cikin abubuwan da yake kewar su a tare da ita.

Tana rerewa yana tuna sadda take tisa shi a gaba tana masa kukan iyashege ko na shagwaba.

Tsawon mintina biyar kafin ya yi karfin halin cewa "Kinga idan iyakacin maganar kenan tashi ki tafi tunda kuka kika zo yi mini".

Ta shiga goge fuskar ta kafin ta yi 'karfin halin hadiye kukan ta ce "Kai ka ce duk sadda na shirya fa'da maka gaskiya, zaka saurare Ni fa".

Ya zakudo yace "eh na fa'di haka, amma ai ke yanzu bansan gaskiyar ki ba, sau nawa kina canja mini baki, da me zan dogara har na gamsu?"

Ta zube a gabansa kan guiwowinyata ta ce "Billahillazi iyakar gaskiyar kenan ubangiji shine shaidata".

Ya yi shiru! Bai ce komai ba illah fama da yake da zafin zuciya.

Cikin rawar murya ta ce "Ina ha'da ka da girman Allah da Ma'aiki ka yafe mini, ka mayar da auren mu, gobe kafin ka 'daura da wata jibi, na yarda na amince, ka yi auren har ma ka tafi da ita, Ni ka barni anan zan jiraka, na cigaba da amsa sunan matarka shine kwanciyar hankali na! Wallahi tunda ga ranar da ka sake ni Malam har yau ban sake barci da Ido biyu ba, me yasa ba zaka gasgata ni ba?".

"Sa'a ta ya ya zan gaskata ki alhalin ke baki gaskata kan ki ba?
Ke ce kika janyo komai, ke kika cusa mini rashin aminci game da lamarin ki".

Murya na rawa ta ce baka aminta da Ni ba fa ka ce?"

Kai tsaye ya amsa "kwarai da gaske Sa'adatu, menene alakar ki da Khalil da zai baki Agogon gold? kin tattauna da kawayen ki na kasa siya miki wayar da kike so, ke kika san tsiyar da kuka yi , ya mallaka miki kayayyaki masu daraja tamkar ke din yantacciyar mace ce".

Ta rushe masa da kuka tare da ru'ko kafarsa ya kwace da sauri.

"Kar ka zarge ni da abin da baka da tabbaci, kar 'bacin rai yasa ka daukarwa kanka zunubin da ba zaka iya daukarsa ba".

Ya mike da sauri, a fusace ya nuna ta da dan yatsa ya ce "ke kika haskaa mini kofofin zargin ai, akan wanne dalili zai baki Agogon gold?"
Da waya mai tsadar gaske?"

Murya a dakushe saboda da kuka ta ce "English gold ne Malam! Bai kai darajar Dubai gold ko Saudi ba"

"Amma dai me daraja ne? tunda a lokacin ai ba zan iya siya miki ba. Bayan haka me ya hana ki bu'de mini wayar? Me kuke yi da ba kya so na gani, ha'inta ta kawai kike yi Sa'adatu, dama ance yanzu mata ta waya ma suna tura tsaraicin su ga shedanun mazan da basu san darajar mace da kuma aure ba, bare wannan 'Dan iskan yaron da bani da tabbacin aure ne ya kawo shi duniya".

Ya yi shiru saboda yadda kirjinsa ke masa ciwo.

Ido Sa'a ta zuba masa, ta jima tana kallon shi, tana jin wata irin jarumta na shigarta, ido cikin ido tace "wannan dalilin ne yasa ka kasa mini afuwa, ka kasa kallon nadamata, ka kasa yi mini alfarmar cigaba da zama matarka da kuma rayuwa tare da Jawad?"

Ba ja in ja ya sake cewa "kwarai da gaske ai dama na ta'ba fa'da miki, ba zan sake miki uzziri akan dan'iskan yaron nan ba, ashe a lokacin ma abin na ku da tsabta".

Ya zarce da fa'din "dama yanzu ai anfi lalata da matan aure saboda kome aka kwaso kai-tsaye za'a likawa mijinta ya yi ta wahala da abin da ba nasa bane, ko ayi ta masa sharing matarsa hankali kwance, tunda darajar aure ya bata dukkan kariya daga jifan da zai ta'ba mutuncinta dana ahalinta".

Wani irin abu mai tsananin nauyi ya tokare a wuya da zuciyar Sa'a, hawaye mai zafi ya balle mata, ta mike tsaye, ta sake zuba masa ido ta ce "Na gode da dukkan dawainiyar da ka yi da ni har ya zuwa yau, ina maka fatan alheri a sabon aurenka, Ina fatan ko wacece ta kasance abokiyar arzikinka ce".

Kuka ya nemi subuce mata, amma ta sa dukkan dauriya ta danne shi, ta yi shiru, na dan sakwanni goma, sannan ta dora da cewa

"A yau na tabbatar komawa gareka ba alheri bane, domin cikin shekaru hudu ba yan waattani kullum a cikin sallar dare nake, ba abin da nake ro'kar ubangiji sai ya 'kaddara ka mayar da auren mu, duk satin duniya sai na yi azumi biyu, idan na zo buda baki ba abin da nake ro'ka irin na koma dakin ka".

Anan kuma sai kukan ya gwada mata fin karfi ya kwace ta sunkuyar da kanta 'kasa tana kukan sosai, a zuciya kuma sai ambaton*Hasbunallahu wa Ni'imal wakil* take yi! Ai kuwa ta sami sau'ki sosai .

Yana tsaye yana kallonta yana jin tamkar yasa ruwa da omo ya goge tsatsar da ta yiwa zuciyarsa, Amma ya kasa, ya tabbatar kishi ne ya rufe masa ido, fasa wayar nan da ta yi means a lot to Him.

Kanta na kasan ta bude murya ta ce "Na yarda da kalaman ka na cewa mu kan so abu alhalin sharri ne, haka nan muna kin abu alhalin alheri ne, na gamsu sosai tunda har Kai da ka tabbatar kaine mutum na farko da ya fara taka ta, amma ka kasa kubutar da ni daga sake saken zuciya da na shaidan.

Idonta a soye ta ce "shin ka gamsu Jawad 'danka ne ko kuwa kana tantamar li'ka maka na yi kake ta wahala da shi alhalin ba jinin ka bane?"

Da rawar jiki ya dunfare ta ba zato ta ji ya faskawa bakinta mari mai zafin gaske har sai da jini ya fara fitowa tabbacin ya fasa mata shi.

Cikin gajiyawa da neman sulhu ta ce "wannan shine kawaicin da zan maka na karshe akan 'daga mini hannu da kake yi, kuma dole na tambaye ka, idan shima a Ballagazancin da ha'incin na samo shi, sai ka dawo mini da 'dana ni zan cike masa gurbin uba, tunda dama ai mutum baya rasa uwa sai dai uba, to ka bani shi kawai, domin ba 'danka bane! nawa ne".
Chapter 73 · 0% Book details