← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 113

Sashe 26

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan kuwa sai da ta sanar da mijin nata, ya ce ya shigo idan ya zo babu damuwa. Ta kalli Iyah ta ce, "Komai aka yi shi akan ka'idojin shari'a ba a nadama, ke ma ki yi koyi da hakan. Kar ki yarda ki yi wasarere da hakkin mijinki, ko da baya gidan ki kiyayi duk abin da kika san ba ya so."

Sa'adah ta amsa da "To!" Sannan ta sauya maganar da tambayar, "Inna na dauko juice din?"

Da sauri ta amsa mata da cewa "Dauko mana ki hado da ruwa, ai ba sai kin tambaya ba."

"To Inna ai shekaranjiya na ga kin hana ni dauka ne!"

Tana rufe baki ita ma ta ce "Ai ba don shi aka saya ba, saboda Muutar ya sayo ya ce a ajiye idan ya zo ki dinga ba shi. Kin ga kuwa idan har ba Muutar ba ne ai ni ba zan bayar ba."

Wucewa dakin Sa'adah ta yi tana dariya tare da cewa,"Oh Innah maganar Baffa tamkar hadisi take a gunki!"

"Aljannata nake nema kin san kuwa aljannar mace ta fi samuwa idan mijinta ya yarda da ita."

Cikin dariya sosai Sa'adah ta ce, "Sadaqati Inna! Kin yi gaskiya In Sha Allah har a aljanna ke ce uwargidan Baffah."

Dariyar ita ma ta shiga yi tana fadin, "Allah ya shirye ki Iyah"

Daidai lokacin kuma waya ta hau kuwwa tana dubawa ta ga MK ne, ta amsa, ya sanar mata ya iso.

Ta mikawa Inna wayar tana cewa, "Ya iso."

Daki ta koma ta sake gyara fuskarta sannan ta feso turare ta fito, ta dauki tabarma ta na fadin, "Ki tashi Inna ki kintsa, na ajiye miki Hijabin da za ki saka a kan gado."

Harara ta galla mata tare da cewa ba zan saka wanda kika ajiye din ba 'yar fariya! Kin yi shigarki ta burgewa, amma kin tashi kin fesa turare."

Ta yi kwafa tana ayyana dauke shi za ta yi ta boye.

Murmushi ta yi tare da cewa, "Take heart mom!" Sannan ta juya ta tafi.

Ta isa da sallama yana tsaye yana amsa waya, ya yi kwalliya da yadin kufta kalar ruwan kasa (brown), ya dora hular da ta dace da kayan. Sosai ya yi kyau, musamman yadda sumarsa da hula ba ta rufe ta gaba'daya ba tana ta sheki alamun ta sha gyara na musamman.

Ya katse kiran yana zuba mata ido sosai sai kuma ya hau murza dukkan idanuwansa, ya sake kallon ta soasai, ya bude baki alamun mamaki tsawon sakanni goma sannan ya nisa ya ce, "Sa'adah ce kuwa, ko idona ne ya ke mini gizo?"

Ta tura baki tana dan murmushi tare da shagwabe fuska.

Hakan da ta yi sai ta sake burge shi ya ce, "Kin canja fa! Ba ki ga yadda kika yi kyau ba, ganin ki na yi tamkar 'yanmatan Ethiopia."

Da'di ya kamata musamman yadda bakinsa ya yi daidai da na Innar ta, ya lura da yadda take murmushi, ya fahimci tana son a ce ita mai kyau ce, ko ta yi kyau.

Ya ce "Ki fa daina wannan shagwabar ita ma tana sani a wancan yanayin!"

Ta rufe fuskarta da gefen Hijabinta, ba tare da ta iya cewa komai ba.

Ya sake cewa, "Idan ba so kike na zama agwagwa ba, to ki daina yin ta a yanzu. Ki tara mini ita zuwa lokacin da za mu tsinci kanmu a dakinmu!"

Ta sake rufe ido sosai tana ayyana wai shi ba ya jin kunya ne?

Ganin yadda ta rufe ido ta makale a bango sai ta ba shi dariya sosai.

Ya dan juya dan ganin ba wanda zai ji shi, ya yi kasa da murya ya ce, "Ba ki ji yadda na ji ba, ina ma ni kika makale ba wannan bangon ba! Kunyar nan ma burge ni take yi, komai na ki is special!"

Shiru ta yi ta kasa juyowa, bare ta tanka masa, tana ji a jikinta yadda idanuwansa ke yawo a kanta.

Da kyar ta bar jikin bangon ta shimfida tabarma tana cewa, "Bismillah!" Ya yi kicin-kicin da fuska tamkar ba shi ne mai walwala yanzun nan ba.

Ya ce, "Ba zan zauna ba!"

Ta dago ta kalle shi a kunyace ta ga yadda ya hade fuska, gabanta ya fadi, tana tunanin me ya 'bata masa rai kuma?

A hankali ta ce," Tafiya za ka yi?"

Ya girgiza kai sannan ya ce, "Zaman ne ba zan yi ba, ki dinga shimfida wa Honorable."

Ta yi shiru tana jin fargaba na taso mata!

Ta nisa ta ce, "Amma dai ai na ba ka ha'kuri, magana sai ta wuce."

Da sauri ya ce, "In dai sai na zauna a inda yake zama to kuwa magana ba za ta wuce ba!"

Ya juyar da kansa gefe guda, ganin yana Shirin dawo mata da yanayinsa da ba ta so na nuna ko in kula ta kalle shi ta ce "Bari na dauko maka wani abin zaman to."

Bai ce komai ba, ta nade tabarmar ta shiga da ita, ta dawo da kiret din lemon kwalba mai kwari, ta ajiye ta dora sallaya a kai, kamar ba zai zauna ba sai kuma ya zauna din.

Ita kuma ta zauna a kan wani dutse da ya ke zauren. Ta kalle shi ta ga bai ware ba, ta daure ta ce, "Ba don fishinka na gigita zaman lafiya ta ba, da haka zan so ganin ka kullum. yadda ba yanmatan da za su ga fuskar tunkarar ka, saboda kwarjini da tsare gida."

Dariya ta kwace masa, ya nisa ya ce, "Kina da son kai Sa'adah! Ba kya son na kula yanmata amma ke ba ki kiyaye kula wasu mazan ba."

Ganin ta yi kasa da kai sai ya canja maganar da cewa, "Mahmoud ya na gaishe ki"

A hankali ta ce "Na gode!"

Sun jima suna hira bayan ya sha ruwa, suka shiga ya gaida Inna, ya ajiye mata kudi, sannan su ka koma zauren, ba su dade da zama ba Baffa ya dawo, ya tarar da su, a kunyace, MK ya sauko daga inda yake zaune ya tsugunna ya gaishe shi. Baffa ya amsa cike da farinciki, har ya wuce sai ya dan tsaya ya ce, "Da ma kuwa ina son ganin ka, idan ka samu lokaci ka same ni."

Da girmamawa MK ya amsa da Fadin, " Koyaushe ina da lokaci."

Baffa ya ce "To bayan La'asar gobe idan ranmu ya kai."

Sai da ya shige sannan ya koma gun zamansa, Sa'adah na masa dariyar yadda ya takure.

Ya kalle ta ya ce, "Idan akwai abin da ya fi haka na kunya zan ji tunda yarsa nake so ya ba ni, ya kuma san abin da zan yi da ita!" Shike nan ya rufe bakinta ruf.

Ya zuba mata ido ganin yadda ta turo baki gaba alamun fishi-fishi.

Ya waske kamar bai gani ba, ya nisa ya kira ta da alamun seriousness "Sa'adah!"

Ta yi shiru, sanin halinta na shariya da sanin ta ji shi ya zarce da fadin, "Magana za mu yi ta gaskiya, ki nutsu ki ban hankalin ki."

"A kan kunnenki Baffa ya ce za mu yi magana, ga zatona mafi karfi ina ganin zai yi maganar idan mun shirya kanmu na turo da magabatana."

Nan ma ba ta ce kala ba.

Ya nisa ya sake cewa, "Kina ji na kuwa?"

Kai ta daga masa alamun tana tare da shi.

Ya ce, "Tsakaninki da Allah ki fada mini gaskiya don na san yadda zan tunkare shi. Mun kai lokacin da ya kamata a ce mun fahimci juna, maganar aure idan manya suka shiga ta kare fa! Ba maganar canjawa idan dai ba mayar da iyaye abokan wasa za a yi ba.
So nake yi, ki fada mini da bakinki idan Baffa ya tambayi mun shirya kanmu, me zan ce masa?"

Ta yi kasa da kanta ta kasa cewa komai, tsawon minti guda sannan ya dora da cewa, "Kar ki ji nauyin fadar gaskiya na yi miki al'kawarin zan fahimce ki, zan kuma fahimtar da Baffah yadda ba zai ga laifinki ba."

Ta kasa bude baki ta yi magana ita kanta ba ta san me yasa harshenta ya yi mata nauyi ainun ba? Tsawon mintuna yana dakon ta magantu amma shiru.

"Ina ta magana kin yi mini shiru kuma kin san ba na son ina magana kina ji amma ki yi kunnen uwar shegu."

Ta sake yin kasa da kai, da kyar kuma a hankali ta ce, "Ni to me zan ce?"

Bai ji dadin yadda ta ce ba amma sai ya ce, "kinsan me za ki fada mini da zai nuna kin aminta da Ni ko akasin hakan".

Ta kasa fadar ko daya, ya gaji da sauraronta ya ce "Shirunki yana nufin na yi hakuri, na sha kaye a hanun abokan takara".

Yana gani ta bude wayar dake hannunta wacce ta Inna ce ta fito da ita.

Ba zato ya ji wayarsa ta yi kara kadan, alamun shigowar sako (message) bai duba ba ga zaton sa MTN ne.

Ganin ta share ta hau daddana waya sai ya sake jin rashin dadi sosai, a tunzure ya ce,
"Silent again?"

A kunyace ta ce, "Ka duba wayarka!"

Bai yi musu ba ya dauko wayar sa ya shiga ma'adanar sakwanni (inbox) ya ga text din da ya shigo ita ta turo shi. Da sauri ya bude, harrufa uku kawai ya gani.

"*YES*"

Kawai ta rubuta wani irin dadi ya mamaye zuciyarsa da sauri ya ce, "Kin amince mini na turo Sa'adah da gaske?"

Kai kawai ta daga masa don ta sake ba shi tabbaci.

"Alhamdulillah!" Yake ta fadi tare da cewa "Na gode!" Ya bude murya sosai ya kira ta, bai jira amsawarta ba ya zarce da cewa, "Idan fa kin zabe ni har na turo aka nema mini aurenki, hakan na nufin kin rabu da Honorable, da wannan tabbataccen yaron! Da ma kowa da kowa, sai ni kawai.

Kin ga saboda na san kina da damar ki zabi wanda ya miki shi yasa nake danne kishina, amma tsakani da Allah idan har maganar aure ta kullu tsakanin manya dole ki rabu da kowa kin amince?"

Ba wani dogon Turanci ta ce, "E!"
Chapter 26 · 0% Book details