Sashe 105
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi shiru!
Ya nisa ya ce "fa'da mini menene tunda na san haka kawai ba zaki nemi ni ba tunda kin ringa kin jefa ni sahun Marasa adalci da daraja a duniyar ki".
"Ni ni bani da lafiya ne".
Ta fa'da a rarrabe kuma a shagwabe.
"Me ya same ki?"
Ta yi shiru, ta kasa cewa komai.
"Na san dai ba kewata kike yi ba, tunda tuni kin cire ni a masoyinki".
"Dama zan fa'da maka ne, Anty Sumayya da Umman Fanshekara suna son zuwa su ga gidan da zan zauna".
Ya murmusa ya ce "Na san ki tamkar tafin hannuna, fa'da mini dai gaskiyar magana. Kawai ki ce kin fasa yin rabin shekarar kina son tarewa dan kar abin da kike boyewa ya bayyana a gaban su Baffah".
Zuciyarta ta tsinke, da sauri ta ce "me nake boyewa?"
Ya waske da cewa "Tarin Sona mana na zuciyar ki, bayan bakinki yana ta jifana da kiyayya".
Ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. Ni ai dama ban ta'ba cewa bana sonka ba, sai dai na ce da aure ne bana yi, saboda kaima ai ba ni kake so ba".
"Fahimtar ki ce hakan, kuma Wallahi ina taya ki jin kunyar ace kin rayu da ni shekaru bakwai, amma baki ki san wannene Mukhtar ba".
Ta katse shi ta hanyar cewa
"Ni yanzu me zance wa masu son zuwa ganin gidan?"
Kai-tsaye ya ce "ki ce ban kammala gyran gidan ba, sai nan da wattanni shida lokacin ya yi dai dai da kammaluwar na ki Shirin".
A mugun shagwabe ta ce "Bana son haka, bana so, ka daina daukar hakkina haka Nan".
Wani irin farin-ciki ya mamaye Mk ya ce "fa'da mini me na yi miki na daukar hakki?"
"Ni kawai ka fa'da mini gaskiyar abin da zan fa'da musu".
"Ki fa'da musu saboda kin ce sai kin gama shiryawa, ya sanya nima na shiririce. Da gaske ban tanadi inda zaki zauna ba".
Hakan da ya fa'da ya sa ta fashe masa da kuka sosai.
Ya matse dariyar da ta so subuce masa ya ce "Share hawayen ki kin ji my dear, ki bari idan na dawo sai mu yi maganar a nutse, ki fa'da musu bana gari, Amma da zarar na dawo, zamu tattauna".
Da yake son tariyar take yi a kwanakin nan yasa ta biye masa, suka rabu kalau.
Yana ajiye wayar ya dinga dariya yana fa'din Ubangiji ka kaddara addu'ar da nake yi ne ka karba, ubangiji ka kaddara hasashena ya zama gaskiya.
Ya yi shiru yana murmushi a zuciyarsa sai fa'dawa Ubangijinsa yake yi idan har ya tabbata ciki ne da ita azumi uku zai yi na godiya ga Allah, abin da ya da'de yana son ayi masa kenan haihuwa! yana son ya ga Jawad ya na da mahadi, yana son 'kananun yara.
Ya tuna lokacin da ya matsu Sa'a ta sake haihuwa amma kawayenta suka zugata wai zata tsufa da wuri.
Ya fesar da zazzafar iskar bacin rai, a fili Kuma sai ya ce "Na yafe komai, na manta komai".
Sati biyu Mk ya dawo, zuwa wannan lokacin cikin yana shiga sati na bakwai, ta fara wani irin fari, sai kuma ya canja salon ba komai zata ci ba, asalima bata isa ta sha tsurar ruwa ba.
Sai dai ta sirka ya dai canja launi.
Ga miyau bai tafi ba.
Kullum cikin Hijabi take da safa, saboda yadda kafafuwanta suka yi fari, suka yi fresh, da zarar Baffah ya tafi Gogel zata tafi gidan Sumayya, saboda kada Innnah ta ganota.
Washagarin dawowar Mk ya iso wajen Sa'a da tarin tsarabar manja da kuma kwakar manja.
Da rawar jiki ta kai ta zubo a bowl ta dawo ta hau ci tamkar nama.
Ya zuba mata ido yana ganin sauyuka a tare da ita karara.
Zuciyarsa ya gama gasgata zatonsa. Ya dinga Hamdala a ransa.
Lafiya Lau suka gaisa, ba bacin rai.
Ganin Bai sako maganar da ya ce sai ya zo ba, ya sa ta kawar da fuskarta gede ta ce " Ya maganar da na yi maka?"
"Wacce?".
Ta tura baki gaba ta ce "su Anty sun matsa mini akan zasu je su ga yanayin windows da kofofi saboda maganar labule".
Ya cije ya ce "idan dan wannan ne ba matsala na riga na tanade su".
"Kar ku damu".
Ta juyo ta ce "Na damu ni na gama shiryawa ranar juma'ah zan tare".
Dariya ta kwace masa sosai, yayin da itakuma ta hau kuka marar sauti.
Ya kalleta sosai sai fahimci kuka take tunda ga zuciyarta ba wai na shagwaba bane.
Ya hadiye dariyarsa ya ce "menene kuma amma dai kinsan ban son irin wannan kukan ko?"
Ta kasa magana. Sai da ya dinga rarrashinta ya samu ta daina kukan.
A hankali ta ce "Akan me zaka mini dariya bayan abin da ka janyo mini?"
Da sauri ya ce "me na yi miki?
"Abin da ka yi mini a Sokoto mana".
"Oh sorry Sa'adah! na dauka abin ya wuce ai".
"Ina ya wuce tunda kullum yini nake da yawu a bakina, ga idan Innah na girki sai dai na rufe daki, na yi ta amai ban son ta gane mai nake ciki."
"Ya waske, da cewa to ana boye ciwo ne? Tashi muje ki ga likita".
Ya kalleta gaba'daya ta yi laushi, ya san laushin da ta yi dan ta samu yadda take so ne.
"Ni ba inda zani".
Ya kuwa mike da sauri ya ce "shikenan na fita hakkin ki, mu yini lafiya".
Tana daga zaune tasa hannu ta ru'ko rigar farar shaddar jikinsa.
Ya juyo suka ha'da ido suka dinga kallon juna, suna jin wani irin tsumin soyayya yana tsuma su.
Sa'adah ce ta yi saurin dauke kai.
A hankali ta ce "da gaske na gama".
Ya juyo ga'ba daya ya ce " Sa'a ba zai yiwu na tare da ke a hakan ba, kina musguna mini, ban isa ki mini yadda nake so ba, ban isa na ce ga yaddda zaki yi, ki ce to ba, haka kawai fa kika ce ba zaki tare ba, sanin kanki maganar ba a hannuna take ba, tunda Baba Kika fadawa, shine kuma ya bani umarnin na lamince miki ki kammala shirin ki, yanzu kuma cewa zai yi na nuna bai isa da ni a karo na biyu ba".
Ta tura baki gaba ta ce "Amma ai da ka ro'ke ni akan ka kira shi , na fa'da masa zan tare da bakina".
"Eh na fa'da amma sai na ga bai kamata na matsa miki ba, shekaru bakwai na yi ina kuakan rashin ki, Kinga kuwa duk dadewar da zaki yi kina shirin ba zaki kai irin wannan lokacin ba. Ki Bari ko wata uku ne, nan gaba sai mu san yadda za'a tunkare shi.
Kuka ta fara tana cewa" ba wannan maganar, wallahi ba zan yarda Innah ta fahimci Ina da ciki ba, tunda ba za su gane da bada son raina hakan ya faru ba".
Ya zauana ya fuskanceta sosai, sai kuma ya tafi ya yi sujjud shukur, ya dago yana cewa "Alhamdulillah, ubangiji ya raba ku lafiya, na dade ban ji farin-ciki irin na yau ba".
"Tashi muje ki siyi abin da kike so a matsayin tukuici".
"Ni ba inda zani".
Ido kawai ya zuba mata, jikinta ya yi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa.
Ta mi'ke tsaye, tana tura baki gaba, irin wadda take yi masa a shekarun baya, mai ha'de da wani irin ta'bara da shi kawai take yiwa irinsa.
Nan da nan jikinsa ya hau tsuma da sauri, ya matsa kusa da ita, ya rungumeta sosai, dukkansu sun shiga wani irin yanayi mai tsuma jiki da gangar jiki gaba'daya.
A kidime Mk ya saketa ya shiga waiwayen inda zai ga hijabinta, can ya hango wani a ninke akan akwati.
Da kansa ya ware ya fara kicinyar saka Mata. Tmda taimkonta hijabin ya daidaita.
Ya kalleta sosai ya ce "Bari na fita, sai ki fito muje asibitin a duba ki, daga Nan sai ki raka ni unguwa".
Ta kasa yi masa musu, tana tsaye tana jin yana yiwa Inna sallama, ya fice ya barta tana faman tauna maganar da zata fa'dawa Innah.
Haka ta fito rataye da yar 'karamar Jakarta, ta kalli Inna da take kofar kicin a tsaye, ta ce "Inna zanje asibiti, daga nan kuma zan wuce gidan Maman Khalifa".
Ido Innah ta bita da shi tabbas tana ganin kasala a tare da ita, kuma ba kasafai take cin abinci ba.
Ta ce "wanne asibitin zaki je?"
"Ban san wadda zai kai ni ba, Ni ba dan ya dage bama, da ba wani asibitin da zani, na san zazzabin cizon sauro ne".
"To sai kin dawo, amma kar ki kwana gidan su Khalifa, Baffan ku baya gari, gara ki dawo mu kwana tare".
Sa'adah ta amsa da cewa "To Innah".
Innah ta sake cewa "ki kula da kanki, ki lalla'ba shi, kar ki yi abin da zai ja hankalinsa akan ki, har sai anyi tariya. Ni ba gaskiya ba zaki mini wata uku a gidan nan da auren ki ba, wanan watan da wani watan ya isa, koma kudin bai isa ba, kina dakinki sai ki dinga siyan abin da kike so, tunda dai ai ansan mu masu karamin karfi ne".
A sanyaye Sa'a ta ce "Hakane Innah! Ni idan kin ce ma a wannan watan na tare zan yi biyayya ba dan Ina so ba, sai dan na nuna miki na fi girmama ra'ayin ki akan nawa".
Sosai Innah ta zuba mata ido tana son ta gasgata maganar Iyah, amma bata san meyasa take ganin tamkar akwai wani abu da yasa ta sauko haka da wuri akan tariyar ba.
Ta tafi, Inna ta bita da addu'ar dawowa lafiya.
Suna tafe yana ta yawo da su akan titi, shi kansa tunanin inda zai kaita yake yi.
Can ya kalleta ya ce "wanne asibitin kike zuwa yanzu?"
A hankali ta ce "Ni fa na je asibitin an duba ni, ta butde jakarta ta fito da magungunan da aka bata tana nuna masa.
Ya ce "To sannu My Sa'adah".
"Yanzu bari ki raka ni unguwa"
Basu zame ko ina ba sai gidansa na rijiyar zaki.