← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 113

Sashe 22

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabarma kawai ta dauka ta nufi zauren, a tsaye ya jigina da bango ta same shi. Sanye yake da farar shadda kal (Bankole style) ya dora hula ba'ka, kafarsa dauke da bakaken cover shoe. Sallama ta yi tare da shimfida tabarma sai da ya zauna sannan ta zauna ta gaishe shi. Ya amsa ba yabo ba fallasa, kamshin turarensa na Versace da wanda ta yi amfani da shi Escada suka cakude suka cika zauren da wani irin lafiyayyen kamshi mai nutsar da zuciya.

Tsawon mintina suna zaune shiru, ita kanta a kasa yake tana ta wasa da yatsun hannunta da ta musu kwalliya da zobuna (fashion).

Shi kuma kawai kallon ta yake yi, yana nazarin yadda ta iya tsara simple kwalliya ta burgewa tamkar wacce take karantar fashion and design.

Gani ya yi ta mik'e tana cewa, Ina zuwa." Ba ta jima ba ta dawo dauke da faranti a hannunta ta ajiye a gabansa. Ta koma in da tashi ta zauna.

Can ya nisa ya ce, "Wai fishin ne har yanzu?"

Takaicin sa ya makure mata wuya, tunda ya zo ban da kallon ta bai ce komai ba, sai gaisuwar da ya amsa mata ba karsashi, shi ne yanzu zai ce wai fishi take yi, so yake ta saki baki ta masa hira bayan shi ya kame bakinsa ya tsuke, saboda yana jin isa?

Don haka sai kawai ta daure fuska sosai, sannan ta juyar da kanta gefe ba tare da ta ce ko mai ba.

Dariya ta kamashi ya murmusa, sannan ya ce, "Ke kullum a cikin fishi kike? Da kin san yadda murmushi yake sake kawata miki fuska da kullum kin kasance a cikinsa"

Ba ta ce komai ba, ya yi shiru yana nazarin mai zai ce da zai sa ta kula shi. Ya nisa ya ce, "Babana ya yaba da karbar da Baffa ya masa, ya yi murna sosai har cewa ya yi na iya zaben suruki, yana fatan a ce ke ma ki yo halin karamci irin na gidanku "

Ba ta ce komai ba amma ta sassauta daurewar fishin, yana kula da ita, don haka sai ya sake cewa, "Kin san kafin na zo raina a bace yake da ke amma kina fitowa na ga wannan kwallliyar da aka cancanda mini sai na ji na manta komai! Ke kawai nake gani kin cika ko ina fiye da duniyar gaba'daya!"

Dadi ya kamata ta murmusa kadan, amma ba ta ce uffan ba.

Ya dade yana rarrashi kafin ta ware su yi hirarsu, cikin dabara ya tabbatar mata ai ya gan ta da Khalil suna hira a class shi ne kuma dalilin da ya hana shi zuwa, don Allah ta kiyaye.

Ba ta musa ba, cike da dariya ta ce, "Shi ne dalilin da ya sa ka ninka dukan da ka mini?"

"E, saboda ki ji dan kadan cikin takaicin da nake kwana ina tashi a cikinsa."

Bai tafi ba sai da aka fara kiran sallar maghrib, ya mike yana cewa kawo mini buta na yi alwala.

Tana tsaye har ya yi alwalarsa ya mayar da agogon da ya cire ya zura hannu ya ciro sabbin yan dari-dari da suka sha turare guda ashirin ya mika mata da 'kyar ta karba wanda sai da ya rantse akan sai ta karba, sannan ta sa hannu biyu ta karba, ita kanta a ranta addu'a take Allah ya sa kar ya mayar da kudinsa! Ta ga samu ta ga rashi 😁 a wancan shekarun dubu biyu tana da daraja ba kamar yanzu ba.

Ta kalle shi a kunyace ta ce, "Ka tsaya sai ka rasa sahun gaba, Baffa yana ta cewa kullum a sahun gaba kake sallah."

Dadi ya kama shi tare da cewa, "Ashe har kamfen Baffa yake mini a gunki, lallai ki ce na kwantar da hankalina, na same ki na gama! Amma yanzu ba na iya zuwa wurin da yake yin sallah, kunyarsa nake ji."

"Ta yi dariya sosai ta ce, "To kuma a ina kake yi?"

Ya kalleta yana jin wani irin abu na tsirga masa da sauri ya fice yana cewa, Nan Masallacin bayan layi nake zuwa."
Ya tabbatar sai ya sake alwala saboda yadda ya tsinci kansa cikin yanayi na sha'awa sosai.

Bata lura da yanayinsa ba ta dauka kawai gaggawa yake yi tunda an tayar da sallah, shi yasa bai bari sun yi sallama ba.

Sai da ta yi sallah sannan ta je falo gun Inna ta mika mata kudin da ya ba ta, za ta fita ta ce "Zo ki zauna."

Kusa da ita ta zauna, a hankali ta ce, "Ina fatan dai ba shi da matsala ko Iyah!"
Dariya ta kama Sa'adah ta cije ba ta yi ba, amma sai ta yi nufin tsokanar Innar, don haka sai ta ce
"Ba shi da matsalar komai Inna amma gaskiya ni wanzancin da yake yi ne bai mini ba!" Ta fada a dake tamkar gaske.

Salati sosai Inna take yi tana karawa, amma sai ta taushi zuciyarta cikin lallashi ta ce, "Iyah mene ne laifin sana'arsa saboda Allah? Ai abin alfaharinmu ne duka ace matasanmu sun daina zaman banza, sun daina zaman jiran gwamnati ta basu abin yi, ke yanzu raina wanzancin kika yi? To bari ki ji tun a lokacin ma'aiki akwai wanzamai, sannan duk inda wanzamai suke mutane ne masu amana masu kuma tsananin zumunci, bare kawai don yana da shagon aski sai ki mayar da shi wanzami?"

Dariyar da take dannewa ta kubuce ganin yadda Inna ta kwantar da murya tana lallaba ta, tana cewa a ranta Inna ta koma lallashi.
A fili kuma ta ce
"To shikenan ki cigaba da addu'a Allah ya sa na ji ina son sa tunda na lura duk ya kwanta muku a rai"

"Ai ni tunda na ji Baffanku ya yabe shi na ji ya kwanta mini a rai, kinsan mijin yayarki ma shi ne ya zaba mata, halayensa da nagartarsa kawai ya auna, shi yasa kema nake so ki masa biyayya kar ki yarda ya kubuce miki".

Alkalamin
*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*KAR KU BARI A BARKU A BAYA WURIN KARANTA DADDAN LABARIN NAN*!

*⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️*
NA
*Jameey yar'mutan kankia*.

*Promo* *Promo* *Promo*

_Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake_.

*#300-sau biyu a rana*
*#500 -sau ukku a rana*
*#700 -sau hudu a rana*

_Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316_.

*MASU SON A TALLATAH MUSU HAJARSU KOFA A BUDE TAKE*
_TUNTUBI_
08032773332.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

36-37.

Sannu a hankali cikin nutsuwa MK ke tafiyar da Sa'adah, a sati sau daya yake zuwa zance. Duk da ya karbi lambar wayar Inna tun da yanzu koyaushe wayar na hannunta amma ba kasafai yake kiran ba, duk a kokarinsa na ganin bai raba mata hankali ba, musamman da kullum jarrabawarsu kara kusantowa take yi.

A bangarenta kuma sai ta ke ganin kawai rashin daukar ta da muhimmamanci ne yasa yake nuna mata rashin kulawa, musamman yadda Khalil ke kiranta safe da yamma sannan su raba dare ana musayar kalamai, shi yasa ya daina damuwa da rashin saurarar shi da ba ta yi a makaranta.

A haka har aka rubuta jarrabawar JAMB, duk kokarin da MK ya yi na ganin Sa'adah ta samu rubuta jarrabawar abin ya ci tura! Saboda yadda Baffa ya ce masa "Ni sakandiren nan ma a dole na bar ta ta kammala ,yar uwarta aji uku kawai ta yi na aurar da ita, don haka ni ba zan barta ta tafi wata babbar makaranta ba, ta zo tafi karfina".
Ya dan tsahirta sannan ya rufe maganar da cewa, "Idan Allah ya sa ta zo hannunka komai ma sai ta yi, amma ni a yanzu babban burina shi ne na sauke nauyinta da ya yi saura a kaina, na aurar da ita a hannun da ko ba na numfashi ba za ta koka ba".

Kan dole MK ya ha'kura da maganar amma ya kudire a ransa Sa'adah za ta yi karatu har sai ta ce ya ishe ta.

Gab da za su fara rubata WAEC wa'adin da MK zai yi a makarantar FGC ya cika, amma saboda yajin aikin da jami'o'i suke yi, yasa hukumar makarantar ta roke shi ya ci gaba da zuwa kafin lokacin da ASUU za ta janye yajin aikin. Kasancewar MK da sakamako mai daraja ta daya (First Class) ya fita, yana cikin wadanda Jami'ar Bayero za ta dauka don yin koyarwa.

A haka suka ci gaba da tafiya a baibai tsakanin MK da Sa'adah, shi yana ganin ya ba ta lokacin da za ta yi karatu sosai, ita kuma tana masa kallon wanda bai girmama lamarinta ba, hakan ya sa take saurarar duk wanda ya nuna yana son ta ba tare da tunanin ai tana da wanda take so ba! Musamman da a lokacin damina Baffa ya fi zaman Gogel saboda kula da noman da yake yi, ita kuma Inna zuciyarta daya ta dauka MK ne yake zuwa.

A haka har ta kammala makaranta gaba'daya, cikin wannan yanayin ta hadu da Alhaji Mamman! Asibitin (Arewa Surgery) suka je duba Mahaifiyar Safina ita da Halima, sun fito harabar asibitin suka hadu da shi, ya nemi su shigo mota ya kai su, Sa'adah ta'ki amincewa amma da yake tare suke da Halima sai da ta rinjaye ta suka shiga motar, a hanya ya nuna ra'ayinsa akan Sa'adah, wanda sam-sam bai kwanta mata ba, musamman da yake ta gan shi dattijo da alamun yana da iyalai masu yawa a karkashinsa.

A lokacin wayar hannun ba ta da yawa sosai kamar yanzu, sannan mai madannai ce komai tsadar wayar. Ya tambayi lambar wayarta, Sa'adah ba ta ce komai ba sai da ya sake tambayar a karo na biyu sannan ta ce "Ba ni da waya."
Chapter 22 · 0% Book details