Sashe 38
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ta yi, tamkar ba da ita yake ba, ya matsa ya riko hannunta, ta fizge tare da zura su cikin hijab, wata irin fargaba ta kama shi, bakinsa har rawa yake yi ya ce "Har abin ya kai mu ga haka, laifi na yi ke nan?"
Nan ma shiru ta sake yi.
"Don Allah Sa'adah me na yi miki? Ki fada mini, ba ni za ki duba ba, Allah na hada ki da shi".
Jikinta ya yi sanyi sosai, ta kasa cewa komai sai da ya sake rokon ta sannan ta bude baki ta ce, "Ni gaskiya zaman ne ba zan iya ci gaba da yi ba, na gaji".
Gabansa ya yanke ya fa'di.
Murya ba amo ya ce "Me na yi miki?"
Shiru ta yi, hankalinsa ya yi mugun tashi ya fara fa'din,
"Ban miki komai ba fa Sa'adah, don Allah idan wasa kike mini ki bari bana so".
Yana rufe baki ta ce "
"Wallahi ba wasa na ke yi ba, zaman ya isa haka nan".
Ya tsura mata ido tsawon lokaci ba kakkautawa yana nazarinta, ya lura da gaske take yi, bugun kirjinsa ya karu, gumi ya fara karyo masa, jikinsa na bari ya ri'ke kafadunta da karfi, ya ce
"Kar ki mini haka Sa'adah don Allah, ina sonki fiye da kaina, fada mini inda na gaza, me na ke yi wanda ba kya so?"
Ta yi shiru amma fuskar nan a daure tamkar hadari, hannunta ya ruko da karfi ya dora a kan kirjinsa ta ji yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.
"Kin ji yadda zuciyata ta ke bugawa, tun daga ranar da kika canja mini Sa'adah har yanzu ban huta daga wannan bugun ba, ya sake matsarta sosai ya ce "Ko aikina ne ba kya so? Idan shi ne sai na je na ajiye musu".
"Ni ban ce ba, idan ba ka yi aiki ba 'kasa za ka ci?"
"Me yasa kika cire kanki, da gaske za ki iya rabuwa da ni?"
"E mana indai zan tsira da mutunci na."
Kansa ya kulle ainun ya kasa gane me take nufi.
"Ban gane idan za ki tsira da mutunci ba?"
Ta zumbura baki ta ce "Kai ba Bahaushe ba ne?"
Ransa ya fara 'baci, ya kalle ta cike da bacin rai ya ce "Kar ki fara Sa'adatu, kar ki fara mini rashin kunya ba zan 'dauka ba".
Ya mike ya fice da ga falon ya nufi dakinsa.
Zuciyarta sai rawa take yi, ita kanta jarumta take yi, ta kuma riga ta kudire sai ya janye waccan kalmar da ya jefe ta da ita, amma ta lura ransa ya baci sosai don ta fahimci indai ya ce mata Sa'adatu to ransa ya baci da ita ne.
Da kyar ta tashi ta yi wanka, ta shirya cikin guntuwar rigar barci cotton marar nauyi, ta zauna shan black tea, amma zuciyarta na tunanin ko MK ya yi barci, ko me yake yi, ko shima fishin zai dauka yau ba zai zo 'dakinta ba?
Ta dade a falo kafin ta kashe fitila da fanka ta shige daki ta kwanta, adduar barci ta karanta ta shafe jikinta, tana ta tunani, sai ta ji shigowarsa, dadi ya ratsa ta har da sakin ajiyar zuciya.
Yana tsaye ya kunna fitila idonsu ya hadu, nan da nan ta dauke idonta, ya kashe fitilar ya nufi gadon yana kwanciya ya janyo ta jikinsa ya saki ajiyar zuciya tare da fadin
"Ni ba zan iya fushi mai yawa da ke ba, bacin ran da kika sa ni dazu na yafe miki kin ji My Sa'adah! Ke ma ki yafe mini abin da na miki, ki kuma fada mini din kar na sake maimatawa a gaba".
Uffan ba ta ce ba, amma farinciki ke ratsa ta yadda yake ta rawar jiki da neman sulhu.
"Kin ji"
Bai jira amsarta ba
ya sake cewa " Don Allah me na yi haka har zuciyarki ta gaji da zaman mu tare, ban yi zaton akwai abin da zan yi ki daina sona ba".
Haka kawai ta ji zuciyarta ta karye, hawaye ya cika mata ido, cikin rawar murya ta ce "Ban daina sonka ba ai, kawai ha'kura zan yi don shi ne ya fi alheri tun ba ka juya mini baya ka fara wulakantani ba".
Jikinsa ya yi sanyi kalau, a sanyaye ya ce "Mafarki kika yi akan zan juya miki baya, yanzu a zaman da muka yi ba ki fahimci irin son da nake miki ba? Kin fi karfin ki wulakanta a hannuna."
Ta kasa cewa komai saboda tana bude baki kuka za ta yi.
Ya sake cewa "Na ji dadi da ba daina sona kika yi ba, ina hada ki da girman Allah ki fitar da ni daga duhu, me na yi miki?"
Kukan da ta ke matsewa ya subuce mata, hawaye har a kan kirjinsa, ya rasa abin da ya ke masa dadi, hankalinsa, in sun kai dubu to a tashe suke.
Haka ya dinga jijjigata yana shafa gadon bayanta tare da fadin sorry, tamkar mai mata bita.
Da kyar ya shawo kanta ta bude baki ta ce "Tun farko na so na hakura da aurenka saboda yadda kake nuna mini am nothing to you, sai dai na san Baffa ba zai fahimce ni ba, tunda sai da ya tambaye ni na ce ina sonka, iyayenka sun zo gunsa to ba ni da sauran dama, ban isa na ce na fasa ya saurare ni ba".
Ta sarara, ta ja hanci sannan ta dora da fadin, "Muna cikin wannan yanayin, sai na yi kuskuren shiga motar saurayi, kuskuren da ni kaina na yarda ban kyauta ba, ba irin ha'kurin da ban baka ba amma ka 'ki, karshe na sake yin wani kuskuren na dauki jiki na bi ka har inda kake, don ka gane yadda fushin ka ya hana ni zaman lafiya.
Sai ka bi ni da wulakanci kala-kala har ka iya ce mini Ballagaza akan idona!"
Kukanta ya dawo sabo, ta shiga yin sa har da rerawa tamkar a cikin nisha'di take, don kawai ta sake tayar masa da hankali, ai kuwa gogan ya kasa cewa komai tsabar yadda komai ya tsaya masa, yana tuno Baba Idi da ya ce lamarin mata yana da gigitarwa, tabbas ya yarda ga shi 'yar yarinya karama tana neman zautar da shi.
Cikin kukan ta ce "Tun lokacin na tabbatar barin ka shi ya fi alheri, tunda za ka iya jifa na da wannan mummunar kalmar a ranka, sai kuma na ga gara na nuna maka ni ba ballagaza ba ce, hakan kuma ba zai yiwu ba sai mun yi aure dole, zuwa yanzu na san ka gane in ma ni Ballagazan ce ko a kasin hakan".
Tsawon lokaci MK ya kasa bude baki ya yi magana. Ya yi shiru yana jin kukanta har cikin kwakwalwarsa.
Da kyar ya bude baki murya ba sauti ya ce, "Ba har zuciyata nake nufi wannan kalmar ba, subul da baka na yi".
Da sauri ta ce"Ai sai da na tambaye ka, ni ce ballagaza, ka ce e, idan akwai kalmomin da suka fita muni na hada da su domin na siffantu da hakan".
"Billahillazi Baby kishi ne ya rufe mini ido a lokacin, amma ba har zuciyata hakan nake nufi ba, na yarda na yi laifi ki yi ha'kuri na tabbatar ke din katangaggiya ce".
Zamewa ta yi a jikinsa ta koma karshen gado tana sake sabunta kukan da take yi tare da fadin, "Ni ba zan hakura ba, kai ne za ka yi ha'kuri kar ka wahalar da ni".
Mirginawa ya yi ya tarar da ita a karshen gadon, ya riko ta tana tirjewa, kukan gaske take yi, har da bubbuga kafa tamkar yar karamar yarinya.
Kwantar da murya ya yi sosai tare da cewa "Babyna tsaya ki ji, tsakaninki da Allah, tunda muka yi aure wacce kalar soyayya ce ba na yi miki?"
Cikin kukan ta ce "Ai don ka ga zargin da kake mini ba gaskiya ba ne, bayan haka kuma kana hutawa da ni".
Ya rasa ta inda zai bullo wa wannan yarinyar, ya nisa ya ce
"Zaman da muka yi na wata biyu har da doriya, ban yi wani abin da kika gamsu son ki nake yi da iyakacin gaskiyata ba? Ko a lokacin da kike ganin ba na tarairayarki, ai kona mini rai kike yi, na ce ba na son ganin ki da dan iskan yaron nan, amma ba ki ji ba, haka na yi ta ha'kuri ba don ina son ki ba za mu yi auren ne?"
Ya sake tausasa murya ya ci gaba da fadin, "Saboda Allah indai dama ba wani abu ne a ranki ba, mene ne na dawo da abin da ya wuce, ba haka kawai na fada miki maganar da kika kullace ni a ranki ba, ke kika janyo, ko ba ni da alaka da ke zan yi kishi yanayin da na gan ki, a matsayinki na mace mai daraja".
Ya yi shiru yana jin shesshekar kukanta, tana ta ajiyar zuciya tamkar wadda ya yini yana dukanta.
"Na roke ki, ki daina kukan nan haka, na yarda ban kyauta ba ki yi hakuri".
Ta yi shiru, kamar yadda ya roka din har da gyara kwanciya, da lulluba alamun barci za ta yi, tana sakin ajiyar zuciya, a ranta kuma tana fadin sai kuma rikicin gobe.
Ya so su kasance tare, amma saboda tsoron kar ta ci gaba da masa kuka yasa ya kyale ta, ba a jima ba ya ji saukar numfashinta alamun barci ya yi awon gaba da ita.
Ya saki gauron numfashi, ya haska fuskarta, da hasken wayarsa ya ga hawaye duk ya bushe a fuskar, kuma wani abin dariya ita da kanta ta boye fuskarta a jikinsa. Tsintar kansa ya yi da gyara mata kwanciyar yadda za ta ji dadin barcin.
Ya dawo Masallaci, ya tarar ta dira sabon kuka ga akwati a kan gado sai zuba kaya take yi tamkar mai shirin yin balaguron wata guda.
Zama ya yi gefen gadon yana kallon ikon Allah, da Asubar fari za ta fara masifa tamkar jiya ba ta yi ba, duk irin ha'kurin da ya ba ta ashe bakam ta masa. Yana kallon yadda ta gama shirya akwatin ya kasa cewa komai saboda gaba'daya He is speechless.